Birnin Kudus: Majalisar Dinkin Duniya ta bukaci dukkan kasashen duniya da su juyawa Amuka baya
- Majalisar Dinkin Duniya ta bukaci dukkan kasashen dake duniya da su juwa Amurka baya
- Wannan biyo bayan kuri'ar raba gardamar da aka jefa a zauren
- Sakamakon kuri'ar ya nuna cewa kasashe 128 ne suka bukaci yin fatali da kudurin kasar
Majalisar Dinkin Duniya ta bukaci dukkan kasashen dake duniya da suyi fatali da bukatar kasar Amurka wajen maidawa 'yan share wuri zauna na yankin Isra'ila birnin kudus biyo bayan kuri'ar raba gardamar da aka jefa a zauren.
KU KARANTA: Donal Trump ya soki yan Najeriya dake kasar Amurka
Sakamakon kuri'ar raba gardamar da aka jefa dai ya nuna cewa kasashe dari da ashirin da takwas ne suka bukaci yin fatali da kudurin kasar ta Amurka yayin da kuma kasahe tara suka goyi baya kamar dai yadda kuma wasu kasashen talatin da biyar suka ki yin zaben.
Legit.ng dai ta samu cewa a ranar 6 ga wannan watan na Disemba ne shugaban kasar na Amurka Donald Trump ya umurci ofishin jakadancin Amurka dake kasar Isra'ila da ya koma birnin Kudus, lamarin da ya jawo cece-kuce a tsakanin kasashen duniya musamman ma na musulmi.
Idan ka na da wani shawara ko bukatan bamu labari, tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng Ku ci gaba da bin mu a Facebook: https://www.facebook.com/naijcomhausa da
Kuma Tuwita: http://twitter.com/naijcomhausa
KU LATSA: Sabuwar hanyar karanta labarain Legit.ng HAUSA
Asali: Legit.ng