Jirgi Dauke da 'Yan Najeriya Ya Yi Hatsari a Hanyar zuwa Libya, Mutane sun mutu

Jirgi Dauke da 'Yan Najeriya Ya Yi Hatsari a Hanyar zuwa Libya, Mutane sun mutu

  • Mata biyu 'yan Najeriya ne kawai suka tsira bayan wani jirgin ruwa dauke da mutane fiye da 50 ya kife a cikin tekun kasar Libya
  • Hukumar IOM ta bayyana cewa akalla mutane 484 ne suka mutu ko suka bata a tekun Mediterranean tun farkon shekarar 2026
  • IOM ta yi kiran gaggawa ga kasashen duniya domin samar da hanyoyin shige da fice na halal don ceto rayukan 'yan gudun hijira

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Libya - Hukumar Shige da Fice ta Duniya (IOM) ta sanar da cewa akalla mutane 53 ne ake fargabar sun rasu ko kuma sun ɓata bayan wani jirgin ruwa ya kife a gaɓar tekun Libya.

Jirgin, wanda ke ɗauke da mutane 55 daga ƙasashe daban-daban na Afirka, ciki har da Najeriya ya kife ne a yankin Arewacin Zuwara dake ƙasar Libya a ranar Juma'a.

Kara karanta wannan

Ana wata sai ga wata: 'Yan bindiga sun sake kai hari coci, sun sace masu ibada

Jirgin ruwa ya kife da mutane fiye da 50 a tekun Libiya, ciki har da 'yan Najeriya.
'Yan gudun hijira na iyo suna neman dauki bayan jirgin da suke ciki ya yi hatsari a tekun Italy. Hoto: Chris McGrath/Getty Images
Source: Getty Images

Jirgi ya kife da 'yan Najeriya a Libya

A shafinta na intanet, IOM ta bayyana cewa ƴan Najeriya biyu, dukkansu mata ne kawai aka samu nasarar ceto su yayin aikin bincike da jami'an Libya suka gudanar.

Ɗaya daga cikin matan da suka tsira ta bayyana cewa ta rasa mijinta a hatsarin, yayin da ɗayar kuma ta ce ta rasa jariranta biyu lokacin da jirgin ya kife.

Rahotanni sun nuna cewa jirgin ya tashi ne daga Al-Zawiya da misalin ƙarfe 11:00 na dare a ranar 5 ga Fabrairu, inda bayan sa'o'i shida ya fara cin ruwa kafin ya kife.

IOM ta nuna alhini kan wannan rashi, tana mai cewa dakarunta sun samar da agajin gaggawa na lafiya ga waɗanda suka tsira bayan sun isa gaɓar teku.

Mutuwar mutane a tekun Mediterranean

Bayanan IOM sun nuna cewa akalla mutane 375 ne suka mutu ko suka ɓata a cikin watan Janairun wannan shekara kadai sakamakon kifewar jiragen ruwa da dama.

Kara karanta wannan

Rashin imani: Yadda 'yan ta'adda suka kira Sallah, suka kashe duk wanda ya zo Masallaci

Wannan sabon hatsarin ya kawo adadin mutanen da suka mutu ko suka ɓata a wannan hanyar ta Tsakiyar Tekun Mediterranean zuwa akalla mutane 484 a cikin shekarar 2026.

Hukumar ta yi gargaɗin cewa ƙungiyoyin masu fasa-ƙaurin mutane suna ci gaba da amfani da jiragen ruwan da ba su da ƙarfi wajen sanya rayukan mutane cikin haɗari.

Hukumar IOM ta nemi hadin kan kasashen duniya bayan jirgin ruwa ya kife da mutane fiye da 50
Wasu 'yan gudun hijira a kan jirgin ruwa da ke shirin nutsewa suna neman dauki a tekun da ke tsakanin Libiya da Italy. Hoto: Anadolu / Contributor via Getty Images
Source: Getty Images

IOM ta nemi hadin kan kasashen duniya

IOM ta bayyana cewa:

"Wadannan ƙungiyoyin suna samun riba mai yawa daga safarar mutane a jiragen da ba su da aminci yayin da suke jefa rayukan mutanen ga hadari da cin zarafi.

Hukumar ta kuma kara da cewa:

"Akwai bukatar a samar da hadin kai na kasa da kasa tare da ingantattun hanyoyin shige da fice domin ceto rayukan mutane da kuma murƙushe ayyukan masu fasa-ƙaurin."

Wannan dai na daga cikin manyan hadurran da masu zuwa ci-rani suke fuskanta a tekuna, musamman masu zuwa Libiya da sauran kasashen da sai an ketare ruwa.

Jirgin ruwa ya yi hatsari a Nguru

A wani labari, mun ruwaito cewa, aƙalla mutane 25 ne suka mutu yayin da wasu 14 suka ɓace bayan wani jirgin ruwa ya kife a ƙaramar hukumar Nguru da ke jihar Yobe.

Kara karanta wannan

Tashin hankali: Ƴan bindiga sun kai sabon hari Benue, sun kashe fiye da mutum 10

Haɗarin ya faru ne lokacin da jirgin wanda ke ɗauke da fasinjoji 52 yake kan hanyarsa ta dawowa daga garin Adiyani na jihar Jigawa zuwa garin Garbi da ke Yobe.

Hukumar SEMA ta tura jami'anta daga ƙananan hukumomin Bade da Nguru domin haɗa kai da jami'an tsaro da dakarun sa-kai na yankin wajen gudanar da aikin ceto.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza (Hausa Editor) Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i. Imel: sanihamzafuntua@gmail.com