Za a Mayar da Shirgegen Coci a Ingila zuwa Masallaci bayan Shekaru 11 a Rufe

Za a Mayar da Shirgegen Coci a Ingila zuwa Masallaci bayan Shekaru 11 a Rufe

  • Karamar hukuma a Watford ta amince da shirin sauya tsohon cocin St Thomas zuwa masallaci bayan kada kuri’a
  • Majalisar ta ce amfanin da al’umma za su samu ya fi matsalar ajiye motoci da wasu suka nuna wanda zai taimaka wa mutane
  • Sabon masallacin zai kunshi makarantar yara da wuraren taron al’umma, kuma ana sa ran bude shi a wannan bazarar

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.

Watford, England - Wani tsoho coci a Watford da ke Birtaniya, zai koma masallaci bayan da majalisar karamar hukumar yankin ta amince da shirin sauya amfani da ginin.

Kwamitin kula da harkokin gine-gine na majalisar Watford ya amince da bukatar sauya cocin St Thomas’ United Reformed da ke kan titin Langley.

Cocin Ingila zai koma masallaci a Watford
Cocin St. Thomas da ake son mayar da shi masallaci. Hoto: Google Street View.
Source: UGC

Yaushe aka bar amfani da cocin?

Rahoton Watford Observer ya ce za a mayar da cocin zuwa wurin ibadar Musulmi, bayan taro da aka gudanar a daren Talata, 3 ga Fabrairu, 2026.

Kara karanta wannan

Saudiyya ta yi rangwame ga attajirai game da dokar hana sayan barasa

Cocin, wanda aka rufe tun shekarar 2015, ya dade ba ya aiki, inda rahotanni suka nuna cewa ginin ya zama mara amfani sakamakon manyan matsalolin tsari da lalacewa.

A yayin taron, ‘yan majalisar sun kada kuri’a tare da amincewa da shirin, suna mai cewa amfanin da al’umma za ta samu daga sabon masallacin ya fi matsalolin da wasu ke tsoro, musamman batun ajin motoci.

Jagoran aikin gina Masjid Al-Ummah, Numan Majeed, ya yi jawabi yana mai jaddada cewa shi dan yankin ne, kuma shirin na da nufin dawo da al’adar gini na addini da ke yi wa al’umma baki daya hidima.

Baya ga masallaci, shirin ya kunshi fadada da gyara ginin gaba daya, inda za a samar da makarantar yara da kuma wuraren taron al’umma domin amfani da jama’a.

Musulmai na kara samun ci gaba a wasu kasashen Turai
Al'ummar Musulmi na gudanar da sallah a masallaci. Hoto: Getty Images (An yi amfani da hoton ne domin misali, ba shi da alaka da labarin).
Source: Getty Images

Mayar da coci masallaci ya samu goyon baya

Rahoton ya kara da cewa shirin ya yi daidai da tsare-tsaren ci gaban yankin gaba daya, kamar yadda Christian Premier News ta ruwaito.

A lokacin tuntubar jama’a, an samu ra’ayoyi 84 na goyon baya, yayin da 37 suka nuna adawa. Adawar ta ta’allaka ne kan batutuwan ajiye motoci, hayaniya, da kuma rashin amincewa da sauya cocin Kirista zuwa masallaci.

Kara karanta wannan

Gwamna ya kunyata matarsa a bainar jama'a bayan ta yi kokarin kin sumbatarsa

Kwamitin ya yi la’akari da damuwar ajiye motoci, amma ya ce ba su kai matakin hana amincewa da shirin ba, yayin da aka jaddada cewa rashin yarda ta fuskar addini ba batun tsare-tsaren gine-gine ba ne.

Masu shirin sun bayyana cewa binciken sufuri ya nuna cewa zirga-zirgar jama’a ba za ta wuce karfin hanyoyin yankin ba, domin an tsara lokutan ayyuka ta yadda ba za a samu cunkoso a lokaci guda ba.

Rahotanni sun nuna cewa wannan na daya daga cikin tsofafin coci biyu a Watford da ake shirin mayarwa masallatai. Sai dai shirin sauya Leavesden Road Baptist Church zuwa masallaci an ki amincewa da shi a makon da ya gabata, saboda dalilan kare ginin tarihi.

An mayar da coci masallaci a Turkiyya

A baya, an ji cewa Shugaba Recep Tayyip Erdogan ya saka hannu kan wata doka na mayar da wani tsohon coci na ƙarni na 6 da aka mayar gidan tarihi zuwa masallaci.

Ginin mai nisan kilomita shida ne daga fitaccen ginin Hagia Sophia an mayar da shi masallaci har musulmi sun fara sallah.

Dokar da shugaban ƙasar ya saka wa hannu kamar yadda aka wallafa ta umurci a mayar da gidan tarihin Chora zuwa masallaci.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 5 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.