Jerin Coci-coci 10 da aka mayar Masallatai a duniya
Daya daga cikin wasiyyar karshe da manzon Allah (SAW) ya yi shine haramta wariyar launin fata da asabiyyanci inda yace: Dukkanmu daga Annabi Adam muke, kuma Annabi Adam daga tabo aka halliceshi.
Shiyasa yawaitan Musulmai a kasashen Turai da Amurka bai zama abin mamaki ba inda bincike ya nuna cewa nan da shekarar 2040, yawan Musulmai zai zarcewa Kirista a duniya.
A yanzu haka, akwai cocina da dama daka sauya zuwa Masallatai a wasu sassan duniya musamman Amurka.
Ga jerin Masallatan:
1. Cocin Katolikan St Gerard dake New York, Amurka: An sauyan cocin zuwa Masallaci ne bayan kotu ta bada umurnin haka saboda yawaitan adadin Musulmai a birnin New York.
2. Cocin St. Nicholas: An mayar da cocin Masallaci ne a shekarar 1968 bayan gwamnatin kwaminisanci ta rusashi
3.Cocin Hagia Sopia: An sauya zuwa Masallaci ne bayan gwamnatin Ottoman ya kwace mulki a Anatoliya, Turkiyya
4.Cocin Katolikan St Philip: Asalinta Masallaci ce amma aka mayar Coci a shekarar 1845 kafin aka sake mayar da ita Masallaci a 1962
5.Masjid Isa Ibn Maryam dake Syracuse, New York asali cocin Katolika ne
DUBA NAN: An sace N16m na albashin mutane a ofishin sakataren gwamnatin jihar Katsina
6.Jami Masjid in Buffalo, New-York, asali cocin Katolika ne
7.Babban Masallacin Tangiers dake Morocco asalin Cocine
8. Cocin St Anthanasiuis: Asali cocin Katolika ne aka mayar Masallaci lokacin da addinin Musulunci ya shiga kasar Masar
9.Cocin Jamus da aka mayar Masallaci domin masallata 2000
10.Masallacin Nyalgosi Jamia: Asalin sunansa Cocin Nyalgosi ne a Kenya. An mayar da ita Masallaci ne bayan Faston ya karbi addinin Musulunci.
Asali: Legit.ng