Chora: An sake mayar da wani coci mai tarihi zuwa masallaci a Turkiyya

Chora: An sake mayar da wani coci mai tarihi zuwa masallaci a Turkiyya

Shugaba Kasar Turkiyya, Recep Tayyip Erdogan, a ranar Juma'a ya saka hannu kan wata doka na mayar da wani tsohon coci na ƙarni na 6 da aka mayar gidan tarihi zuwa masallaci a Istanbul.

Ginin na da nisan kilomita shida ne daga fitaccen ginin Hagia Sophia da a watan July aka mayar da shi masallaci har musulmi sun fara sallah.

Dokar da shugaban ƙasar ya saka wa hannu kamar yadda aka wallafa ta umurci a mayar da gidan tarihin Chora zuwa masallaci.

A cewar dokar mai kama da wadda aka yi a game da Hagia Sophia, za a mika ginin ga hukumar kula da addini na kasar Turkiyya.

Chora: An sake mayar da wani coci mai tarihi zuwa masallaci a Turkiyya
Chora: An sake mayar da wani coci mai tarihi zuwa masallaci a Turkiyya. Hoto daga Daily Nigerian
Asali: Twitter

DUBA WANNAN: Hotuna: Jirgin saman da ya yi karo da katanga a Legas

Ginin wadda aka sani da sunan 'Church of Holy Saviour' ya yi fice saboda zane da wasu kayayyakin tarihi da ke cikin sa.

Daular Usmaniyya ce ta mayar da shi zuwa masallaci a karni da 16 sannan mahukunta ƙasar Turkiyya suka mayar da shi gidan tarihi a shekarar 1945.

A watan Nuwamban 2019, babban kotun kasar Turkiyya ta soke dokar da aka yi a 1945 inda hakan ya bayar da damar a mayar da shi masallaci.

Chora da Hagia Sophia dukkan su da farko coci ne na Kirista sannan aka mayar da su masallatai, sannan gidajen tarihi sai kuma daga baya suka zama masallatai.

A watan Yuli, Amurka, EU, Rasha da UNESCO da wasu shugabannin coci-coci da dama sun nuna damuwar su kan sauya Hagia Sophia zuwa masallaci duba da cewa abin tarihi ne da al'ada ga musulmi da kirista baki daya.

Shugaba Erdogan ya yi watsi da sukar da suka yi inda ya ce ba zai amince da katsalandan daga ƙasashen waje ba tunda Turkiyya ƙasa ce mai ƴancin kanta.

Amma a halin yanzu ba a sanar da ranar da za a fara sallar ba a Chora.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Aminu Ibrahim avatar

Aminu Ibrahim (Hausa HOD) Aminu Ibrahim leads the Hausa Desk at Legit.ng. He holds a Bachelor's degree in Microbiology from Ahmadu Bello University, Zaria, and pursued further with a Master's degree in Environmental Microbiology from Federal University Dutse, Jigawa. With over seven years of experience, Aminu has honed his craft in news reporting and content editing, weaving narratives that captivate and inspire audiences: aminu.ibrahim@corp.legit.ng or +2348030996164