'Ta Fi Corona Hadari,' Bayani game da Nipah, Sabuwar Cuta da Ta Bulla a Duniya
- Hukumar lafiya ta duniya (WHO) ta tabbatar da bullar cutar Nipah a wasu sassan duniya, wadda ake kyautata zaton ta fi Coronavirus hadari
- Ana daukar cutar Nipah daga jemage ko aladu zuwa ga mutum ko kuma ta hanyar mu'amala ta kurkusa tsakanin mutane dake dauke da ita
- Har yanzu babu wani takamaiman riga-kafi ko magani na cutar Nipah wanda hakan ya sa ta kasance daya daga cikin cututtuka mafi hadari
Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida
India - Hukumar Lafiya ta Duniya (WHO) ta ba da rahoton mutane biyu da suka kamu da wata sabuwar cuta mai suna "Nipah" a gabashin kasar Indiya a ranar Alhamis.
Wannan cutar ta Nipah ta da matukar hadari, inda take shanye jikin mutanen da ta kama. An samo sunan cutar ne daga wani kauye a kasar Malaysia inda aka fara gano ta.

Kara karanta wannan
Wasu kwamishinoni sun rikita gwamnatin Kano bayan komawar Abba APC? Gaskiya ta fito

Source: Getty Images
Yadda ake daukar cutar Nipah
Rahoton CNN ya nuna cewa cutar tana daya daga cikin dangin cututtukan da ke janyo kyanda, sai dai ita Nipah ta fi ta hadari nesa ba kusa ba.
Cutar Nipah tana daya daga cikin cututtukan da ake dauka daga dabba zuwa mutum. Kamar yadda kafar watsa labaran ta ruwaito, hanyoyin da ake bi a kamu da ita sun hada da:
- Mu'amala da dabbobi: Kai-tsaye ta hanyar taba alade ko jemage da ke dauke da cutar.
- Abinci: Cin ’ya’yan itatuwa ko shan ruwan dabino wanda fitsari ko miyau na jemage ya bata.
- Daga mutum zuwa mutum: Ana dauka ta hanyar mu'amala ta kurkusa da wanda ya riga ya kamu da cutar.
Alamomin kamuwa da cutar Nipah
Yana daukar kwanaki 4 zuwa 14 kafin alamomi su bayyana bayan mutum ya kamu da cutar. Alamomin farko sun hada da zazzabi, ciwon kai, ciwon tsoka, amai, da kuma ciwon makogwaro.
A cikin kashi biyu cikin uku na marasa lafiya, cutar tana tsananta cikin sauri, inda mutum kan iya shiga mawuyacin hali na suma cikin kwanaki biyar zuwa bakwai. Wasu kuma suna samun matsalar numfashi da tari mai tsanani.
Me ya sa cutar take da hadari?
Cibiyar takaita cututtuka ta Amurka (CDC) ta sanya Nipah a matsayi na hudu, wanda shi ne matsayi mafi hadari da ake sanya kwayoyin cuta irin su Ebola.
Rahoton da aka wallafa a shafin WHO ya nuna cewa cutar tana da hadari sosai saboda:
- Rashin magani: Har yanzu babu wani takamaiman riga-kafi ko maganin da aka amince da shi.
- Illa ga kwakwalwa: Cutar tana kai hari ga sassan kwakwalwa da ke kula da bugun zuciya da hawan jini, wanda kan iya barin nakasa ta din-din-din a jikin mutum.

Source: Getty Images
Abin da ake yi wa wanda ya kamu
Yana da wuya a bambance Nipah da sauran cututtuka kamar ciwon sanyi ba tare da gwajin dakin bincike ba. Ana amfani da gwajin RT-PCR ko kuma gwajin jini na ELISA domin tabbatar da ita.
Tunda babu riga-kafi, babban abin da ake yi wa mara lafiya shi ne ba shi kulawa ta musamman kamar ba shi iskar oxygen, kula da abinci, da kuma tabbatar da cewa sassan jikinsa ba su daina aiki ba.
Hukumar WHO ta sanya cutar Nipah a matsayin daya daga cikin cututtukan da ake bukatar gaggauta bincike akansu domin samar da magani.
Wata sabuwar cuta ta bulla a Adamawa
A wani labari, mun ruwaito cewa, gwamnatin tarayya ta fara bincike domin gano musabbabin barkewar wata sabuwar cuta da ke cin naman mutum a Adamawa.
Rahoto ya nuna cewa daga ranar 10 ga Satumba, 2025, an tabbatar da cutar a jikin mutane 67, inda aka yi wa takwas daga cikinsu tiyata a Asibitin Koyarwa na Modibbo Adama, da ke Yola.
Gwamnati ta bayyana cewa har yanzu ba a tabbatar da musabbabin cutar ba, amma ana zargin Buruli Ulcer ce, wacce cutar Mycobacterium ulcerans ke haifarwa.
Asali: Legit.ng

