Cibiyar NCDC ta saki lambobin jiha-jiha da mutum zai iya kira
Cibiyar takaita yaduwar cututtuka a Najeriya NCDC ta saki jerin lambobin jiha-jiha da mutum zai iya kira idan ya bukaci magana ko gwaji.
Cibiyar ta jaddada cewa cutar COVID-19 ba ta yawo a iska. Innama kasa take fadi idan mai dauke da cutar yayi atishawa ko tari.
Saboda haka, ta shawarci mutane su rika nisanta da juna na akalla tsawon mita biyu.

Asali: Facebook
KU KARANTA: Bayan rufe iyakokin jiha, Yan sanda na karban cin hancin N500 hannun matafiya - Gwamnatin Ayade
A bangare guda, yaduwar cututtuka ta Najeriya (NCDC), ya nuna cewa an sake samun karin sabbin mutane 23 da suka kamu da cutar coronavirus a kasar.
A wani rubutu da ta wallafa a shafinta na Twitter, hukumar ta ce tara daga cikin mutanen sun kasance a jahar Lagas ne, bakwai daga Abuja inda biyar suka fito daga jihar Akwa Ibom sai kuma mutum daya daga jahar Bauchi.
Yanzu haka jumullar mutane da ke dauke da cutar a kasar sun zama 174, an salami mutane tara yayinda biyu suka mutu.
Lagos- 91
FCT- 35
Osun- 14
Oyo- 8
Ogun- 4
Edo- 4
Kaduna- 4
Bauchi- 3
Enugu- 2
Ekiti- 2
Rivers-1
Benue- 1
Akwa Ibom- 5
Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.
Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:
https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng