An Zane Mace da Namiji Bulali har 140 bayan Yin Zina Kafin Aure da Shan Barasa

An Zane Mace da Namiji Bulali har 140 bayan Yin Zina Kafin Aure da Shan Barasa

  • Wata kotun shari’ar Musulunci ta yi wa namiji da mace bulala 140 kowanne bisa laifin zina da shan barasa wanda ya saba addini
  • Hukumar ‘yan sandan shari’a ta ce wannan hukunci na daga cikin mafi tsanani tun bayan bai wa jihar Aceh a Indonesia ikon aiwatar da dokar
  • Hukuncin bulala a bainar jama’a na da karbuwa sosai a Aceh, inda ake amfani da shi wajen ladabtar da laifuffuka kamar zina, caca da shan barasa

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.

Aceh, Indonesia - Jami’an ‘yan sandan shari’ar Musulunci a jihar Aceh da ke kasar Indonesia sun yi wa wani namiji da wata mace bulala har 140.

Kotun ta dauki wannan mataki na zane macen da namijin sakamakon aikata zina da kuma shan barasa wanda ya saba ka'ida.

An hukunta namiji da mace kan aikata da shan barasa
Ana zana mace da ake zargin ta aikata zina a Indonesia. Hoto: CHAIDEER MAHYUDDIN/AFP. (An yi amfani da hoton ne kawai domin misali).
Source: Getty Images

An zane wasu saboda zina da shan barasa

Kara karanta wannan

'Dan bindiga da ya hana Turji, yaransa sakewa ya mutu, an kashe shi wurin sulhu

Rahotanni sun nuna cewa wannan hukunci na daga cikin mafi tsanani da aka taba yankewa tun bayan da Aceh ta samu ikon aiwatar da dokar Shari’a, kasancewar ita ce kadai jiha a Indonesia da ke da wannan damar, cewar The Sun Indonesia.

An aiwatar da hukuncin ne a fili, cikin wani fili a birnin Banda Aceh, inda aka rika dukan su a bayansu da sandar itace yayin da jama’a da dama ke kallo.

An ruwaito cewa matar ta suma yayin da ake yi mata bulala, lamarin da ya tilasta daukarta cikin motar daukar marasa lafiya zuwa asibiti.

Shugaban ‘yan sandan shari’a na Banda Aceh, Muhammad Rizal, ya shaida cewa an yi wa mutanen bulala 100 ne kan laifin yin zina ba tare da aure ba, sannan aka kara musu bulala 40 saboda shan barasa, wanda ya kai adadin bulala 140 ga kowanne.

Ya ce hukuncin na daga cikin mafi girman bulala da aka taba yankewa tun bayan bai wa Aceh ikon cin gashin kai na musamman a 2001, wanda ya ba ta damar aiwatar da dokar Musulunci.

An zane mace da namiji da suka yi zina a Indonesia
Shugaban kasar Indonesia a taron tattalin arziki na duniya. Hoto: Prabowo Subianto.
Source: Facebook

Yawan mutane da aka hukunta a lokaci guda

Mutanen biyu na daga cikin mutane shida da aka hukunta a wannan rana saboda keta dokokin Musulunci.

Kara karanta wannan

Sojoji sun bankado masana'antar kera bindigogi, an cafke makeri

Daga cikinsu har da wani jami’in ‘yan sandan shari’a da budurwarsa, inda aka same su tare a wuri na kashin kansu, aka yi musu bulala 23 kowanne.

Rizal ya jaddada cewa babu sassauci wajen aiwatar da hukunci, ko da kuwa jami’an gwamnati ne, yana mai cewa hakan ya bata sunan hukumarsu matuka.

A jihar Aceh, hukuncin bulala a bainar jama’a na da karbuwa sosai, kuma ana amfani da shi wajen hukunta laifuka kamar caca, shan barasa, alakar jinsi tsakanin jinsi daya, da kuma zina.

A bara ma, wasu maza biyu sun fuskanci bulala 76 kowannensu bayan kotun shari’a ta same su da laifin yin jima’i ba bisa ka’ida ba, cewar CBS News.

Mai hukunta mazinata ya aikata zina

A baya, mun ba ku labarin cewa an kama wani da ke hukuncta mazinata inda shi ma aka yi masa bulali saboda laifin da ya yi.

Mutumin dan asalin kasar Indonesiya da ke aiki a majalisar malamai ta garin Aceh ya shiga hannu bayan an kamashi da laifin zina.

Shi dai wannan mutumi mai suna Mukhlis bin Muhammad mai shekaru 28 ya kasance guda daga cikin jami’an majalisar malamai na yankin Aceh a kasar Indonesiya dake dabbaka tsarin shari’ar Musulunci.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 5 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.