Ilhan Omar: Bidiyon yadda Aka Farmaki 'Yar Majalisar Wakilai a Wani Taron Jama'a

Ilhan Omar: Bidiyon yadda Aka Farmaki 'Yar Majalisar Wakilai a Wani Taron Jama'a

  • Wani mutum ya kai wa yar majalisar Amurka Ilhan Omar hari da allura dauke da wani sinadari yayin wani taron jama'a
  • Yar majalisar ta bayyana cewa ba za ta taba barin tsoro ya hana ta gudanar da ayyukanta ba bayan jami'an tsaro sun kama maharin
  • 'Yan sanda sun tsare mutumin yayin da aka fara gudanar da bincike kan sinadarin ruwan da ya fesa wa yar majalisar a jikinta

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Amurka - 'Yar majalisar wakilan Amurka, Ilhan Omar, ta gamu da hari a ranar Talata yayin da take gudanar da taron tattaunawa da mutanen mazabarta a birnin Minneapolis.

Wannan danyen aiki ya sanya jami'an tsaro da 'yan sanda daukar matakin gaggawa, a daidai lokacin da ake takun-saka kan dokokin shige-da-fice na tarayya a birnin.

Kara karanta wannan

'Yan ta'adda sun take yarjejeniyar sulhu, sun afkawa Katsinawa

An farmaki 'yar majalisar Amurka a wurin wani yaro.
'Yar majalisar Amurka, Ilhan Omar na martani bayan wani mutumi ya farmake ta a wurin taro. Hoto: OCTAVIO JONES / Contributor
Source: Getty Images

An farmaki 'yar majalisar Amurka

Kafar watsa labarai ta BBC ta ruwaito cewa wani mutum dauke da allura ya fesa wa yar majalisar wani sinadarin ruwa da har yanzu ba a tantance ba.

Wani bidiyo da ya karade shafukan sada zumunta, ya nuna wanda ake zargin sanye da bakar rigar sanyi, ya mike daga inda yake zaune, ya farmaki 'yar majalisar rike da sirinji.

Bidiyon ya nuna mutumin yana zaune a sahun gaba kafin ya tunkari Ilhan Omar ya fesa mata sinadarin ruwan da ke cikin sirinjn a lokacin da ba ta yi tsammani ba.

Jami'an tsaro ne suka samu nasarar tadiye mutumin zuwa kasa, suka damke shi tsaro jim kadan bayan kai harin, yayin da mutanen dake cikin dakin taron suka rika tafi.

Kalaman Ilhan Omar kafin kai mata hari

Wannan hargitsi ya faru ne jim kadan bayan Ilhan Omar ta soki hukumar kula da shige-da-fice (ICE) tare da neman murabus din sakatariyar tsaron cikin gida.

Kara karanta wannan

Shiri ya baci: Amarya ta hallaka mijinta har lahira a Jigawa

A yayin taron, 'yar majalisar ta bayyana cewa, "Hukumar ICE ba za ta taba canzawa ba," tana mai nuni da buƙatar yin garambawul ga yadda hukumar take gudanar da ayyukanta.

'Yan sandan Minneapolis sun tabbatar da cewa jami'ai sun ga mutumin yana fesa wa yar majalisar sinadarin ruwan, inda nan take aka kama shi aka kai shi gidan yari.

'Yar majalisar Amurka, Ilhan Omar ta fuskanci hari a lokacin da take jawabi a taron jama'a
'Yar majalisar Amurka, Ilhan Omar ta na jawabi a taron da aka farmake ta. Hoto: Brandon Bell / Staff
Source: Getty Images

Yanayin sinadarin da aka fesa wa yar majalisa

Manema labarai dake wurin taron sun bayyana cewa sun ji wani wari mai karfi kamar na "Vinegar" a lokacin da mutumin ya matsa kan allurar.

Duk da wannan firgici, Ilhan Omar ta ci gaba da taron bayan an fitar da maharin, inda ta bayyana cewa ba za ta taba barin tsoro ya hana ta aiki ba.

Daga baya, ta wallafa a shafinta na X cewa:

"Ina cikin koshin lafiya. Ni jaruma ce don haka wannan 'yar barazanar ba za ta tsoratar da ni daga yin aikina ba."

Kalli bidiyon yadda aka farmaki 'yar majalisar a kasa, wanda aka wallafa a shafin CSPAN na X:

Ilhan Omar ta lashe zabe a Amurka

Kara karanta wannan

Daga fitowa gida, 'yan Boko Haram sun harbe malamin addini da jami'an tsaro har lahira

A wani labari, mun ruwaito cewa, Ilhan Omar, ta sake lashe zabenta a matsayin mai wakiltan mazabar Minnesota ta 5, Minneapolis, a jihar Minnesota.

A zaben farko, Ilhan Omar ta kafa tarihi a siyasar kasar Amurka, inda ta zama mace Musulma da ta lashe zabe a kujerun majalisar wakilan kasar.

Ilhan Omar, ta samu nasara a mazabar Minneapolis, inda ta doke Keith Ellison a wa'adinta na farko wanda shima shine Musulmi na farko da aka zaba zuwa majalisar wakilan Amurka.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza (Hausa Editor) Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i. Imel: sanihamzafuntua@gmail.com