An samu mamba mace musulma da zata fara zuwa zaman majalisa da hijabi a kasar Amurka

An samu mamba mace musulma da zata fara zuwa zaman majalisa da hijabi a kasar Amurka

- A karo na farko, majalisar jihar Amurka zata bawa musulma mace daman saka hijabi ta kada kuri'a da yin jawabi a zauren majalisar

- Ilhan Omar wacce ta dade tana fafutikan neman 'yancin hakan zata kasance mace na farko da zata saka hijabi a yayin da za a rantsar da ita a ranar Alhamis 3 ga watan Janairu

- Har yanzu, majalisar ta haramta saka hula mai malfa (cowboy hat) da hular baseball a cikin zauren ta

Majalisar wakilai na Amurka ta amince da bukatar daya daga cikin mambobinta mace musulma, Ilhan Omar na neman izinin saka hijabi yayin da zata kada kuri'a ko gabatar da jawabi a zauren majalisar.

Daily Mail ta ruwaito cewa kakakin majalisar mai jiran gado, Nancy Pelosi da Ciyaman din kwamitin kafa dokoki, Jim McGovern sun goyi bayan bukatar na Omar kuma sun saka shi a cikin dokokin majalisar a ranar Talata 1 ga watan Janairu.

An samu mamba mace musulma da zata fara zuwa zaman majalisa da hijabi a kasar Amurka
An samu mamba mace musulma da zata fara zuwa zaman majalisa da hijabi a kasar Amurka
Asali: UGC

DUBA WANNAN: Kungiyar musulmi ta takawa Bishop Kukah birki kan shirinsa na taimakon almajirai

Legit.ng ta gano cewa Omar wadda za a rantsar a ranar Alhamis, 3 ga watan Janairu ta dade tana neman a bata ikon sanya hijabi a zauren majalisar.

A cewar rahoton, an hana sanya sauran huluna na al'ada kamar hular cowboy da hular baseball. Abin rufe kai na addini ne kawai aka amince da sanyawa a majalisar ta 116.

Bayan ta lashe zabe, Omar wadda tayi takarar a karkashin jam'iyyar Democrat ta rubuta a shafinta na twitter cikin watan Nuwamba cewa: "Ni ne zan sanya hijabi in rufe kai na. Ra'ayi na ne - wadda dokar kasa ta bani. Wannan ba shine kadai dokar da zan canja ba."

Jam'iyyar republicans za ta mika mulki da Democrats bayan kwashe shekaru takwas suna rike da majalisar.

Omar itace 'yar majalisa musulma na farko da zata fara sanya hijabi a zauren majalisar da zarar an rantsar da ita a ranar Alhamis 3 ga watan Janairu.

Baya ga Omar, 'yar majalisa Rashida Talib na jihar Michigan itama musulma ce da tayi nasarar lashe zaben zama 'yar majalisar.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: : https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel