Bayani: An Gano abin da Ya Jawo Wasu Shafukan Intanet Suka Dauke a Sassan Duniya
- An samu babbar tangardar fasaha a kamfanin Cloudflare, wanda ya jawo tsayawar shafukan intanet masu yawa a duniya
- Wannan tangarda ta Cloudflare ta janyo durkushewar shafuka irinsu X, ChatGPT da Letterboxd da na watsa labarai
- Rahoto ya bayyana cewa ana dogaro da fasahar kamfanin Cloudflare wajen kare shafuka daga hare-haren DDoS a intanet
Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida
Amurka - Masu ziyartar shafukan inatenet da yawa a yau sun gamu da matsalar “matsalar sadarwar cikin gida” bayan wata gagarumar tangarda da ta afkawa kamfanin Cloudflare.
Cloudflare kamfani ne da ke samar da muhimman fasahohi wajen kare shafukan intanet daga hare-hare da kuma tabbatar da cewa suna ci gaba da aiki yadda ya kamata.

Source: Getty Images
Shafuka irinsu X (Twitter), ChatGPT, Letterboxd da wasu daruruwan shafukan intanet sun dauke, suka daina budewa, kamar yadda BBC ta rahoto.
Cloudflare ta tabbatar da matsalar Intanet
Kamfanin Cloudflare ya fitar da sanarwa a shafinsa na intanet, inda ya bayyana cewa:
“Muna sane da matsalar da ka iya shafar abokan hulda da yawa kuma muna ci gaba da bincike.”
Amma, bayan sa’o’i sama da biyu da matsalar ta fara, kamfanin bai bayyana lokacin da za a kammala gyara ba.
A baya ma Cloudflare ta yi ikirarin cewa an shawo kan matsalar, sai kuma daga baya aka gano matsalar na nan daram.
A sabuwar sanarwar da ya fitar, kamfanin ya ce:
“Muna ci gaba da aiki don gyara matsalar.”
Wannan dai ya nuna cewa matsalar ba ta kau ba, kuma tuni ma'abota amfani da intanet suka tsinci kansu a mawuyacin hali.
Matsalar ta cigaba da yaduwa zuwa karin shafuka
Ganin cewa shafin DownDetector shima ya samu cikas ya sa rahotanni kan illar tangardar ba su fito fili ba, amma wasu shafuka kamar Vinted da Grindr sun fara bayyana cikin jerin wadanda suka durkushe.
Wasu masu amfani da shafukan intanet sun ruwaito cewa ba iya shafukan yanar gizo ke daukewa ba, har ma wasu manhajoji sun daina aiki gaba ɗaya.
A halin yanzu babu wani takamaiman lokaci da Cloudflare ya bayar, wanda ke nuna cewa lamarin na da girma sosai.
Kasancewar mafi yawan shafukan intanet suna jingina lamuran tsaronsu ga kamfanin Cloudflare, duk wata matsala da ta shafi kamfanin, na shafar kusan kowa.

Source: Getty Images
An kira lamarin “babbar tangardar intanet"
Alp Toker, daraktan kamfanin NetBlocks, ya ce:
“Wannan tangarda ce mai girma ga tsarin Cloudflare gaba ɗaya.”
Ya kara da cewa dogaro da Cloudflare wajen kare shafuka daga hare-haren DDoS ya mayar da kamfanin babbar hanyar da matsala daya ka iya durkusar da dimbin shafuka.
A cewarsa, yawancin yanar gizo a shekarun baya sun koma bayan Cloudflare domin tsaro — abin da ya maida shi “matattarar intanet."
'Yan Najeriya sun yi martani kan tangardar
Wasu 'yan Najeriya da muka zanta da su sun nuna damuwarsu kan daukewar wasu shafuka da aka samu.
Nura Haruna Mai karfe ya ce:

Kara karanta wannan
Bayan Kebbi da Neja, ƴan bindiga sun sace dalibai a Nasarawa? Ƴan sanda sun magantu
"Ni dai abin ya ba ni mamaki, ina ta kokarin in wallafa wani rubuta a shafin X amma sai ya rika nuna mun akwai matsala, in sake gwada, ga shi kuma dole ina bukatar dora rubutun a wannan lokaci.
"Zan iya ce maka duk wadanda suke aiki Web3 ransu ya baci yau din nan, saboda akwai wadanda aikinsu ba da amsa a tambayoyi ko abin da muke kira 'shilling' watau tallata abu a X don ya samu sanuwa sosai.
"Sannan sai ga Canva ta zo ta tsaya, wannan ma ya ci mun tuwo a kwarya don da shafin nake tsara hotuna, shi ma ya zo ba ya yi. Kai, yau dai mun ji jiki malam."
Wata mai aikin wallafa bidiyo a shafukan sada zumunta, Sadiya Khalid, ta ce ta ji takaicin daukewar ChatGPT, domin tana tsakiyar tattara bayanan bidiyon da za ta wallafa gobe ne shafin ya daina aiki.
Sadiya Khalid ta ce:
"Da ChatGPT nake amfani wajen tsara labari da fitar da yadda hotunana za su zama, to amma kwatsam na ga ya dauke, na dauka ma ko data ce ta kare, amma na ga su WhatsApp suna aiki, sai na rasa gane mecece matsalar, sai yanzu da kake fada mun.
"Gaskiya ya taba mun aikina na yau, don yanzu lokaci ya riga ya kure, ba zan iya shirya bidiyo har in dora ba. Shi ma Canva da nake hada hoto da shi ya zo ya dauke.
"Akwai bukatar ace babban kamfani kamar Cloudflare ya mallaki wani tsari da idan an samu tangarda to akwai wani tsarin da zai iya tafiyar da shafuka ba tare da ya taba su ba."
Abin da 'yan Najeriya suka fi lalube a intanet
A wani labarin, mun ruwaito cewa, rahoton Google Trends ya nuna abubuwan da mutanen Najeriya suka fi lalube idan suka hau yanar gizo tun daga shekarar 2006 zuwa 2021.
A Najeriya abubuwan da suka fi farin jini sun hada kungiyoyin kwallon kafa irinsu "Man U”, “Real Madrid”, “Chelsea FC”, "FC Barcelona'' da kuma "Liverpool".
Haka zalika mutane na yawan neman bayanai a kan mawaka da ‘yan kwasan kwaikwayo kamar Mercy Johnson”, Odunlade Adekola da kuma “Burna Boy.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng


