Google ya bayyana abubuwan da mutanen Najeriya suka fi lalube a yanar gizo

Google ya bayyana abubuwan da mutanen Najeriya suka fi lalube a yanar gizo

  • A watan nan ne aka yi shekara 15 ana amfani da manhajar Google Trends
  • An bayyana abubuwan da mutanen Najeriya suka fi ziyarta a yanar gizo
  • BVN, Mercy Johnson na cikin abin da mutane suka fi neman bayanai a kai

Google Trends wata na’ura da ke nuna abubuwan da ake bibiya a yanar gizo ta cika shekara 15 da kafu wa a ranar 11 ga watan Agustan shekarar 2021.

Domin ayi bikin cikar wannan manhaja 15 ana amfani da ita a Duniya, an fitar da jerin abubuwan da mafi yawan ‘yan Najeriya suka fi bibiya a yanar gizo.

Premium Times ta ce rahoton ya kunshi abubuwan da mutanen Najeriya suka fi nema idan sun hau yanar gizo tun daga shekarar 2006 zuwa shekarar bana.

A Najeriya abubuwan da suka fi farin jini sun hada kungiyoyin kwallon kafa irinsu Man U”, “Real Madrid”, “Chelsea FC”, "FC Barcelona'' da kuma "Liverpool".

Kara karanta wannan

Harin yan bindiga kan makarantar sojoji abun kunya ne – Kungiyar ACF

Haka zalika mutane na yawan neman bayanai a kan mawaka da ‘yan kwasan kwaikwayo kamar Mercy Johnson”, Odunlade Adekola da kuma “Burna Boy.

Bayanai fiye da biliyan daya ake nema a kowace rana daga wajen Google. Sama da sau tiriliyan 1.2 ake naman bayanai daga shafin na Google a duk shekara.

Me aka fi laluba a Najeriya?

Menene soyayya?

Ya ake samun kudi ta yanar gizo?

Menene komfuta?

Nawa ne farashin Dala?

Ya ake rubuta takardar neman aiki?

Ya ake duba BVN?

Google
Google Trends Hoto: techeconomy.ng
Asali: UGC

Wakokin da aka fi bincika?

Xxxtentacion Bad Vibes Forever

In Christ Alone

Brown Skin Girl

All Of Me

Onise Iyanu

Reckless Love

Despacito

Silent Night

Great Is Thy Faithfulness

Ancient Words

Kara karanta wannan

Abubuwa 5 da zai sa a dade ba'a daina magana kan auren Yusuf da Zahra ba

Taurarin Nollywood da suka fi suna a Google

Mercy Johnson

Funke Akindele

Ini Edo

Odunlade Adekola

Adam A Zango

Iyabo Ojo

Rita Dominic

Angela Okorie

Juliet Ibrahim

Adunni Ade

Mawakan da aka fi bibiya

Burna Boy

Omah Lay

Adekunle Gold

Tope Alabi

Small Doctor

Reekado Banks

Banky W

Frank Edward

2Face Idibia

Yinka Ayefele

Wasu mawakan Turai ake bibiya?

Nicki Minaj

Chris Brown

Cardi B

Ariana Grande

Kanye West

Celine Dion

Meek Mill

Bob Marley

Whitney Houston

August Alsina

Fina-finai

The BFG movie

Titanic movie

Black panther full movie

Moana

Frozen 2

Kesari Yoruba movie

Half of a Yellow Sun movie

War room movie

Fifty Shades of Grey movie

Kungiyoyin kwallon kafa

Man U

Real Madrid

Chelsea FC

Arsenal FC

Man City

FC Barcelona

Liverpool FC

AC Milan

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng

Online view pixel