Yanar gizo: Hanyoyin da za ka gane jabun shafin sada zumunta na Facebook

Yanar gizo: Hanyoyin da za ka gane jabun shafin sada zumunta na Facebook

- Dandalin sada zumunta na Facebook na tara mutane masu kirki da bata gari

- Sai dai, akwai bukatar ka gane sakon bukatar zama aboki daga wani wanda baka yarda da shi ba, don gane shafi na gaskiya ko na bogi

- Akwai hanyoyi 6 da za a iya gane jabun shafin sada zumunta a Facebook

Dandalin sada zumunta da musayar ra'ayi na Facebook, na daya daga cikin manyan kafafen sada zumunta na yanar gizo da ke tashe, kafar da mutane daban daban ke amfani da ita daga fadin duniya. Wadannan mutane sun hada da masu kirki da kuma bata gari, wanda a kowane lokaci za su iya tura maka sakon bukatar zama aboki, (Friend Request).

Sai dai, akwai bukatar ka gane sakon bukatar zama aboki daga wani wanda baka yarda da shi ba, wala-Allah kana tsoron ya kasance shafi ne na damfara ko kuma masu sankame shafukan mutane.

KARANTA WANNAN: Cutar kwalara ta bulla jihar Yobe, ta kashe mutane 61 - Kwamishinan lafiya

Yanar gizo: Hanyoyin da za ka gane jabun shafin sada zumunta na Facebook
Yanar gizo: Hanyoyin da za ka gane jabun shafin sada zumunta na Facebook
Asali: UGC

Ga hanyoyi 6 da za ka gane jabun shafin sada zumunta a Facebook.

*Hoton mamallakin shafi

Abu na farko da ya kamata ka fara ankara dashi, ko ka fara bincika a duk lokacin da kaci karo da wani shafi wanda baka yarda da shi ba, shine hoton mamallakin shafi, idan har baka yarda da wannan hoto ba, to ka ajiye hoton don yin bincike akai.

Yadda zaka yi hakan shine, ka sauke koton akan komfuta ko wayarka, sai ka shiga shafin image.google.com, sai ka shiga bangaren kamarar daukar hoto, zai nuna maka damar zabar hoto daga waya ko komfutarka, sai ka bude tare da daukar hoton, a nan take Google zai gudanar da bincike akan hoton, idan har ka ci karo da hoton a shafin batsa, to daga nan zaka san shafin mutumin na facebook na bogi ne.

*Bayanan kan shafi

Babban abun da zaka fi mayar da hankali shine nazartar bayanan kan shafin wanda kake zargi. Zaka fahimci wani kuskure da duk mai shafin bogi ya ke yi, yawanci suna amfana da sunan mata, sai dai fa ba kowane shafin mace bane na bogi. Zaka fahimci hotunan mamallakin shafin ba sa wuce 2 ko 3, kuma kusan duk na sanannun mutane ne.

Don haka, idan har mamallakin shafin bai yi wani canja rubutaccen ra'ayin sa ba, ko kuma babu musayar ra'ayi daga abokansa ko nata akan wannan ra'ayi da ta/ya dora, to ta iya yiyuwa shafin ba na bogi bane.

KARANTA WANNAN: Kiwon lafiya: Rundunar sojin sama ta kai daukin gaggawa ga al'umar Zangeru, jihar Niger

Haka zalika, idan har bayan da ke kan shafin ba su gamsar da kai ba, to ka dauka shafin na bogi ne, sau tari sukan sanya wasu bayanai ne da zasu kaika ga wani shafi.

*Shafuka masu dauke da hotunan mata

Mafi akasari, akan bude shafukan Facebook na bogi ne da hotunan mata a jikin hoton mamallakin shafin, wanda hakan ke jawo mutane wajen turawa mai shafin sakon bukatar zama aboki ko tura masu sakwanni don zantawa da su. Ka kasance mai taka tsan-tsan da ire-iren wadannan shafukan, dole ne ka yi bincike kan hoton kamar yadda muka fara yin bayani da shi a baya.

* Ranar haihuwa a 1 ga watan Janairu

Akwai rahotanni da ke nuna cewa mafi akasarin masu amfani da shafukan bogi na sanya ranar haihuwarsu a 1 ga watan Janairu, wanda ya ke zama mai sauki a yayin bude irin wannan shafi. Don haka dole ka yi taka tsan tsan da irin wannan shafi, tare da daukar mataki da zaran kaci karo da shafin a jerin abokanka.

*Binciken ayyukan mamallakin shafin

Ka tsaya ka yi nazari tare da bincike akan ayyukan mamallakin shafin a kafar, idan har ya kasance mamallakin shafin na tura sakon bukatar zama aboki, ba ya nuna sha'awar wasu shafuka ko shiga shafukan kungiyoyi, to ta iya yiyuwa shafinsa na bogi ne. Domin mai shafin na son tara abokai don cimma wata manufa ta sa.

*Lambar waya a shafin mace

Mafi akasarin shafukan da aka bude su da suna mace, zaka samu lambar wayar mamallakin shafin a jikin bayanan shafin, wanda kowa ya san cewa abu ne mai matukar wahala mace ta bayar da lambar wayarta haka kawai.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukan mu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

INEC na iya haramta amfani da wayar salula a rumfunar zabe | Legit.ng TV

Asali: Legit.ng

Online view pixel