Masu Umrah Sun Kone Kurmus da Motar Su Ta Yi Karo da Tankar Mai a Madina
- Wata motar bas dauke da masu Umrah daga Indiya ta yi karo da tankar mai a hanyar zuwa Madina, inda mutane 45 suka rasu
- Gwamnonin jihohin Indiya da suka hada da Revanth Reddy da M.K. Stalin sun jajanta tare da daukar matakan gaggawa
- Firayim Minista Narendra Modi ya bayyana alhini, yana cewa jami’an Indiya suna aiki kafada da kafada da hukumomin Saudi
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
Madinah, Saudiyya – Mummunan hatsarin bas ya yi ajalin ’yan Indiya 45 da ke kan hanyar zuwa Madina domin ibadar Umra.
Rahotanni sun bayyana cewa lamarin da ya tayar da hankalin iyalai, shugabanni da al’ummar Indiya baki ɗaya.

Source: Twitter
Hukumomin Saudiyya sun sanar a X cewa bas ɗin ta yi karo da wata tankar man dizal a kan hanyar Madina.

Kara karanta wannan
'Sai mun biya': Al'umma sun fadi makudan kudi da suke ba 'yan bindiga domin kariya
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Rahotanni sun ce mutum guda ne kawai ya tsira daga hatsarin, yayin da hukumomin Saudiyya da takwarorinsu na Indiya ke ci gaba da bada taimako ga iyalan mamatan.
Shugabannin Indiya sun yi alhini
Gwamnan Telangana, Revanth Reddy, ya bayyana hatsarin da cewa “mummunan lamari”, yana mai nuna alhini a madadin gwamnatin jiharsa.
Al-Jazeera ta ce ofishinsa ya sanar da cewa an kafa dakin kulawa a ma’aikatar jihar domin tattara bayanai da kuma taimaka wa iyalan mamatan.
Gwamnan ya ce:
“An kafa dakin kulawa a sakatariyar jihar domin bibiyar bayanai da matakan tallafi. Ga layukan dakin kulawa: +91 79979 59754, +91 99129 19545.”
Har ila yau, gwamnan ya umurci jami’an ma’aikatar harkokin wajen Indiya da ofishin jakadancin Saudiyya da su dauki matakan gaggawa domin tallafawa al’ummar da abin ya shafa.

Source: Twitter
A Tamil Nadu kuwa, gwamna M.K. Stalin ya bayyana ta’aziyarsa yana mai cewa:
“Ina mika ta’aziyata ga iyalan waɗanda suka rasu. Ina fatan wanda ya jikkata zai samu cikakkiyar kulawa ya warke da wuri.”

Kara karanta wannan
Abin takaici: Yan bindiga sun harbe tsohon dan takarar majalisar tarayya a Zamfara
Haka nan babban sakataren jam’iyyar AIADMK, Edappadi K. Palaniswami, ya nuna bakin cikinsa kan mutuwar ’yan Indiya da lamarin ya rutsa da su.
Maganar Firaministan Indiya, Modi
Firaminista Narendra Modi ya bayyana bakin cikinsa kan wannan babban ibtila’i da ya faru a kasa mai tsarki. A rubutunsa a dandalin X, ya ce:
“Na ji tsananin bakin ciki kan hatsarin da ya faru a Madina wanda ya yi ajalin ’yan Indiya. Ina mika ta’aziyata ga iyalan mamatan, kuma ina addu’ar samun sauki ga duk wanda ya jikkata.
"Ofishin Jakadancinmu a Riyadh da ofishinmu a Jeddah suna ba da duk taimakon da ake bukata, kuma jami’anmu suna ci gaba da tuntubar hukumomin Saudiyya.”
Shugabannin Andhra Pradesh da Telangana suma sun bayyana alhini, inda suka ce hatsarin ya girgiza su matuka.
Kasar Saudiyya ta nada sabon mufti
A wani labarin, kun ji cewa gwamnatin Saudiyya ta tabbatar da nada sabon mai fatawa na kasa baki daya.
Dattijon malami, Sheikh Salih Al-Fawzan Al-Fawzan ne aka zaba domin cigaba da amsa tambayoyi da ake yi a kasar.
An nada shi mufti ne bayan rasuwar Sheikh Al Sheikh da ya shafe shekaru da dama yana jagorantar majalisar malaman kasar.
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng
