Kisan Kiristoci: Yan Majalisa 31 Sun Goyi Bayan Matakin da Amurka Ta Dauka kan Najeriya

Kisan Kiristoci: Yan Majalisa 31 Sun Goyi Bayan Matakin da Amurka Ta Dauka kan Najeriya

  • Shugaban Amurka, Donald Trump ya samu goyon baya kan matakin da ya dauka na sanya Najeriya cikin kasashe masu matsala
  • Yan Majalisar Dokoki 31 sun yaba wa Trump, suna mai cewa hakan ya farfado da muradun kiristoci da ake kashewa a Najeriya
  • A cewar yan Majalisar, kungiyoyi 'yan ta'adda masu tsattsauran ra'ayin addini na kashe dubban kiristoci a kowace shekara, ya kamata a dakile hakan

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Amurka - Ƴan Majalisar Dokokin Amurka 31 sun yabawa shugaban ƙasa, Donald Trump bisa sake sanya Najeriya cikin jerin ƙasashen da ke da babban matsala kan yancin addini (CPC).

Kara karanta wannan

Luguden wuta a Najeriya: APC ta rubutawa majalisar Amurka wasika kan Trump

Ƴan majalisar sun bayyana wannan mataki a matsayin “na jarumta da ɗabi’a”, su na mai cewa hakan ya nuna damuwar Trump kan abin da suka kira cin zarafi da kashe Kiristoci a Najeriya.

Shugaban Amurka, Donald Trump.
Hoton shugaban kasar Amurka, Donald Trump Hoto: @RealDonaldTrump
Source: Twitter

Wannan yabo ya fito ne daga wata sanarwan hadin guiwa da dan Majalisa, Robert Aderholt, shugaban House Values Action Team, ya fitar a ranar Talata, kamar yadda Vanguard ta ruwaito.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

'Yan Majalisa 31 sun yabi Shugaba Trump

Aderholt ya ce matakin da Trump ya ɗauka ya farfaɗo da muradun Kiristocin Najeriya da kuma tabbatar da Amurka a matsayin ƙasa mai kare ’yancin addini a duniya.

“Kudirin Shugaba Trump na kawo ƙarshen kisan Kiristoci a Najeriya da kuma sake sanya ƙasar cikin jerin kasashen CPC ya ba wa mutane fatan sabuwar rayuwa,” in ji shi.

Ya ce ƙungiyoyin masu tsattsauran ra’ayi a Najeriya suna kashe dubban Kiristoci a kowace shekara, don haka ya zama wajibi Amurka ta jagoranci yaki da wannan tashin hankali.

Abin da wasu 'yan Majalisa suka fada

Shugaban masu rinjaye na Majalisar dokokin Amurka, Tom Emmer, ya yaba da jarumtar Trump, inda ya ce:

Kara karanta wannan

Trump ya kara nuna yatsa ga Najeriya, ya ce ba za a ji da dadi ba

“Allah ya albarkaci Shugaba Trump saboda kare mutanen da ke yin addininsu cikin tsoron Allah. Mun sake samun shugaba wanda baya tsoron yin abin da ya dace.”

Shugabar Jam’iyyar Republican, Lisa McClain, ta kira kisan da ake yi a Najeriya da “laifi mai girma da abin ƙyama ga ɗan adam."

Trump da Tinubu.
Hoton shugaban Amurka, Donald Trump na da shugaban Najeriya, Bola Tinubu Hoto: @RealDinaldTrump, @OfficialABAT
Source: Getty Images

Haka kuma wasu daga cikin ƴan majalisa kamar Josh Brecheen, Mary Miller, da Mark Alford suka bukaci a ƙara tsaurara takunkumi da ɗaukar matakai masu ƙarfi kan Najeriya.

A nasa bangaren, Chris Smith, shugaban kwamitin harkokin waje na Majalisar', ya bayyana matakin a matsayin gyara kuskuren cire Najeriya daga jerin ƙasashen CPC da gwamnatin Biden ta yi a 2021, in ji rahoton ABC News.

Trump ya kara nanata barazana ga Najeriya

A wani labarin, kun ji cewa Shugaba Donald Trump ya kara yin maganganu masu tsauri a kan yiwuwar amfani da karfin soja a kan Najeriya saboda ikirarinsa kisan kiristoci.

Trump ya yi gargaɗin cewa zai ɗauki mataki nan da nan idan hukumomin Najeriya suka gaza takawa wadanda ke kashe-kashen nan burki a sassan kasar nan.

Kara karanta wannan

Najeriya da sauran ƙasashen Afrika da Amurka ke yi wa kallon barazana

Ya umarci Ma’aikatar Yaki da ta fara shiri don yiwuwar daukar matakin soja, yana mai cewa duk wani hari da za a kawo zai zama mai tsanani kuma ba za a ji dadinsa ba.

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262