Trump: Cacar Baki Ta Balle tsakanin China da Amurka a kan Najeriya

Trump: Cacar Baki Ta Balle tsakanin China da Amurka a kan Najeriya

  • Riley Moore, 'dan majalisar Amurkan da ya gabatar da kudirin sanya Najeriya a matsayin kasar da ke kashe kiristoci ya soki China
  • Wannan ya biyo gargadin da China ta yi wa Amurka na fita daga harkokin cikin Najeriya, tare da bayyana cewa tana tare da gwamnatin kasar
  • A martaninsa, Riley Moore ya ce China ba ta da hurumin yi wa Amurka darasin yadda za ta gudanar da harkokin ƙasashen wajenta

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.

United States of America – 'Dan majalisar wakilan Amurka, Riley Moore, wanda ya gabatar da kudirin da ya sanya Najeriya a cikin jerin kasashen da ke kashe kiristoci ya fusata.

A wannan karon, abin da ya fusata shi ne gargadin da abokiyar kasuwancin Najeriya, wato China ta yi wa Donald Trump na ya daina tsoma baki a cikin abin da bai shafe su ba.

Kara karanta wannan

Trump: Najeriya ta gana da jakadun kasashe, an yi maganar Shari'ar Musulunci

Amurka ta dura a kan China saboda kare martabar Najeriya
Xi Jinping na kasar China, Bola Tinubu na Najeriya, 'Dan Majalisar Amurka Riley Moore Hoto; General BMB/Bayo Onanuga/Riley Moore
Source: Facebook

AIT ta wallafa cewa Moore ya yi martani, inda ya ce gwamnatin China ba ta da hurumin koya wa Amurka yadda za ta tsara harkokin ƙasashen waje.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

'Dan majalisar Amurka ya gargadi China

Moore ya ce gwamnatin China na zaluntar mabiya addini da kabilu daban-daban a ƙasarta, yana kawo misalai da kama Kiristoci har guda 30 saboda addininsu.

Ya kara da cewa haka kuma kasar ta China na tsangwamar kalbilu daban-daban, saboda haka ba ta da bakin magana a kan batun Najeriya.

Trump na kokarin nuna wa duniya cewa ana kshe kiristoci a Najeriya
Hoton Shugaban Amurka, Donald J Trump Hoto: Donald J Trump
Source: Twitter

Ya ce:

“Shugaba Trump ya yi daidai wajen kare ‘yan’uwa Kiristoci da ake azabtarwa da ma kashe su saboda addininsu. Ba za mu bari mulkin kama karya ta Communist ta ce za ta koya mana darasi ba, musamman wadda ta kama shugabannin Kiristoci 30 kuma take tura kabilu cikin sansanin gyaran hali.”

Matsalolin diflomasiyya tsakanin Amurka da Najeriya

Furucin Moore ya kara zafafa rikicin diflomasiyya da tsamin dangantaka tsakanin Amurka da Najeriya bayan barazanar Shugaba Trump na daukar matakin soja kan kasar.

Kara karanta wannan

'Yan majalisar Amurka sun taso Miyetti Allah a gaba kan zargin kisan kiristoci a Najeriya

Gwamnatin Shugaba Bola Ahmed Tinubu ta musanta zargin da Amurka ta yi mata, tana mai cewa tana daukar matakan tsaro da suka dace don kare fararen hula da Kiristoci.

A baya, Moore ya bayyana cewa sake sanya Najeriya a matsayin kasar da ke kashe kiristoci zai tilastawa gwamnatin Najeriya daukar matakai na kare mabiya addinin da hukunta masu laifi.

Sai dai China tana ganin ba hurumin Amurka ba ne ta yi wa kasa mai cin gashin kanta barazana da cewa za a sanya mata takunkumi ko kawo mata hari saboda matsalar cikin gida.

'Yan majalisar Amurka sun dura kan Najeriya

A baya, mun wallafa cewa Majalisar wakilan Amurka ta gabatar da bukata ga Ma’aikatar harkokin waje da ta harkokin kudin kasar da su sanya takunkumi kan wasu kungiyoyi da mutane a Najeriya.

Daga cikin kungiyoyin da suka tsone wa 'yan majalisar ido kuma suka bukaci a dauki mataki a kansu akwai MACBAN da Miyetti Allah saboda zargin aikata ayyukan ta'addanci a kasar nan.

A cikin kudirin H. Res. 860, an ambaci yadda ake zargin 'ya'yan kungiyoyin da kai hare‑hare kan Kiristoci da musulmai masu saukin ra’ayi a sassan jihohin Filato da Binuwai da ke Najeriya.,

Kara karanta wannan

Femi Falana: Babban lauya ya fallasa Trump kan zargin kisan Kirsitoci

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Ahmad avatar

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano. aisha.ahmad@corp.legit.ng