Abubuwan da ba Ku Sani ba game da Zohran Mamdani, Sabon Magajin Garin New York
Tun daga lokacin da Zohran Mamdani, ɗan siyasar jam’iyyar Democrat mai ra’ayin gurguzu, ya shiga takarar kujerar magajin garin New York City, ya shiga takun saka da Shugaban Amurka, Donald Trump.
A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.
United States of America – Tun bayan da ya ayyana aniyarsa na neman zama Magajin Garin New York, tauraruwar Zohran Mamadani ta kara haskawa a kasar Amurka.

Source: Facebook
Legit ta tattaro takaitaccen tarihin rayuwar Mamdani da yadda siyasarsa ta yi karfi, har ya iya kayar da fitattun masu kudi da Donald Trump da suka yi ta kokarin kawar da siyasarsa.
Takaitaccen tarihin Zohran Mamdani
An haifi sabon Magajin Garin New York, Zohran Mamdani a Kampala, Uganda, a ranar 18 ga watan Oktoba, 1991.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
BBC ta ruwaito cewa iyayensa su ne Mahmood Mamdani, wani malamin jami’a kuma mai binciken harkokin Afrika, da Mira Nair, fitacciyar ’yar wasan kwaikwayo da mai shirya fina-finai.
Dukkanin iyayensa 'yan asalin kasar Indiya ne da suka zauna a Uganda, Afrika ta gabas kafin su yi kaura zuwa Amurka.
Sun yi ƙaura zuwa Cape Town, da ke Afrika ta Kudu, yana da shekaru biyar, sannan daga nan ya koma Amurka yana da shekaru bakwai, inda suka zauna a birnin New York.
Ya kammala karatun sakandare a Bronx High School of Science, sannan ya samu digiri na farko a harkokin Afrika daga Kwalejin Bowdoin da ke jihar Maine, a shekara ta 2014.
A wannan jami'a ne ya samar da kungiya mai fafutuka a kan Falasdinawa kuma zama cikakken dan kasar Amurka a shekarar 2018.
Mista Zohran Mamdani kafin siyasa
Kafin ya shiga siyasa, Mamdani ya yi aiki a bangaren samar da gidaje inda ya rika taimaka'yan haya daga masu gidaje da ke kokarin cutar da su, tare da kwato masu 'yanci.

Kara karanta wannan
'Yan majalisar Amurka sun taso Miyetti Allah a gaba kan zargin kisan kiristoci a Najeriya
The Guardian ta wallafa cewa Mamdani ya hadu da matarsa Rama Duwaji, ‘yar asalin Siriya mai fasahar zane da tukwane, ta manhajar Hinge.
Siyasar Zohran Mamdani
Bayan ya yi aiki a matsayin mai ba da shawara kan gidaje da kuma mawaki, Mamdani ya fara shiga harkokin siyasa a birnin New York.
Ya fara daukar tafarkin siyasa ta hanyar zama darektan yaƙin neman zaɓe ga Khader El-Yateem da Ross Barkan.
A shekara ta 2020, Mamdani ya lashe zaɓen Majalisar Dokoki ta Jihar New York inda ya doke Aravella Simotas, wadda ta rike kujerar tsawon wa’adin shekaru biyar.
Bayan doke 'yar jam'iyyar Demcorat a karon farko, 'yan mazabarsa sun sake zabensa inda ya koma kujerar ba tare da hamayya ba a shekarun 2022 da 2024.
Neman takarar kujerar magajin garin New York
A watan Oktoba 2024, Mamdani ya bayyana aniyarsa ta neman kujerar magajin garin birnin New York a zaɓen shekara ta 2025.
A watan Yuni 2025, ya samu nasara mai banmamaki a zaben fitar da gwani na jam’iyyar Democrat, inda ya doke tsohon gwamnan jihar New York, Andrew Cuomo.
A ranar 4 ga Nuwamba, 2025, Mamdani ya lashe babban zaɓen da kuri’u 50.4%, inda ya doke Cuomo 'dan takara mai zaman kansa da Curtis Sliwa, ɗan takarar jam’iyyar Republican.
Manufofin siyasar Mamdani
Daga cikin manufofin da Zohran Mamdani ya tallata kansa da su a wajen 'yan New York akwai sufurin bas kyauta a cikin gari da kuma kulawa ga yara kyauta ga iyalai.
Sauran sun hada da samar da shagunan kayan masarufi mallakin gwamnati, tabbatar da 'yanci da kariya ga masu auren jinsi da saukaka batun biyan kudin haya.
Mamdani ya kuma tabbatar wa da magoya baya da sauran mazauna New York cewa za a inganta tsaron al'umma baki daya da kara mafi ƙarancin albashi zuwa $30 a shekara ta 2030.
Ya kuma bayyana goyon bayansa ga ƙarin haraji ga kamfanoni da kuma mutanen da ke samun fiye da dala miliyan ɗaya a shekara.
Mamdani shi ne ɗan Indiya na farko, ɗan Afirka na farko, Musulmi na farko, matashi na farko, kuma ɗan Democratic Socialist na biyu da ya zama magajin garin New York, bayan David Dinkins.
Ana sa ran zai shiga ofis a ranar 1 ga Janairu, 2026.
Mamdani ya zama sabon Magajin Garin New York
A baya, mun wallafa cewa ɗan takarar jam’iyyar Democratic Party, Zohran Mamdani, ya samu nasara a zaben Magajin Gari duk da wani muhimmin ƙalubale daga Donald Trump.
Shugaban Amurka, Donald Trump ya sha yin barazanar cewa idan Zohran Mamdani ya samu nasara, zai rage ko hana tallafin kuɗi zuwa birnin saboda dalilai irin na sa.
Wannan nasara na Mamdani na iya zama alamar sauyi a siyasar birni da kuma cewa ana samu ƙarin wakilci ga al’ummomin da ba a saba gani ba cikin shugabanci a Amurka ba.
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng


