Tarihin yadda Farmakin Kawo Daukin Amurka Ya Yi Tasiri wajen Sauya Wasu Kasashen Duniya
Amurka - Gwamnatin Amurka ta yi barazanar kawo farmakin sojoji Najeriya domin kare rayukan kiristoci da take zargin ana yi wa kisan kare dangi.
CHECK OUT: How to Start Earning with Copywriting in Just 7 Days – Even if You’re a Complete Beginner
Hakan dai ya biyo bayan matakin da shugaban Amurka, Donald Trump ya dauka na sanya Najeriya cikin jerin kasashen da, "Ake da Babban Damuwa kan Yancin Addini."

Source: Twitter
Amurka ta yi wa Najeriya barazana
A rahoton Reuters, Shugaba Trump ya yi barazanar dakatar da duk wani tallafin kasashen ketare da ke shiga Najeriya, tare da turo sojoji don kawar da yan ta'adda masu kashe kiristoci.
Wannan al'amari ya ja hankalin manyan mutane da malamai, wadanda suka nuna damuwa tare da musanta ikirarin cewa ana yi wa kiristoci kisan kare dangi.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Tun farko dai gwamnatin Najeriya ta musanta wannan zargi, tana mai cewa kasar ba ta nuna wariyar addini kuma hare-haren suna shafar kowane bangare.
Sai dai duk da haka Trump ya ce idan gwamnatin Najeriya ba ta dakatar da zaluntar kiristoci ba, zai aika sojojin Amurka domin share ‘yan ta’adda masu kisan gilla.
Tarihin farmakin Amurka a wasu kasashe
A wannan rahoton, Legit Hausa ta tattaro muku yadda matakin soji da Amurka ta dauka a wasu kasashe ya taimaka wajen yakar yan ta'adda amma kuma ya haifar da matsaloli da asarar rayuka.
1. Iraq
A farkon 1980s, gwamnatin Amurka ta kulla kyakkyawar alaka da hulɗa diflomasiyya da gwamnatin Saddam Hussein musamman a lokacin Yaƙin Iran da Iraq (1980–1988).
Sai dai dangantakar Amurka da Saddam ta lalace ƙwarai sakamakon mamaye kasar Kuwait a Agusta 1990, bisa umarnin shugaban ƙasar,
Wannan ya jawo Yaƙin Gulf (1990–1991) karkashin jagorancin ƙasashen haɗin gwiwa (da Amurka ta jagoranta) wanda ya kori sojojin Iraq daga Kuwait.
Amurka ta zargi Saddam da mallakar makaman kare dangi da haɗin gwiwa da ƙungiyar Al‑Qa'ida duk da babu hujjoji masu ƙarfi kan hakan, cewar rahoton Al-Jazeera.

Source: Getty Images
A 2003, rundunar ƙasashen haɗin gwiwa karkashin jagorancin Amurka ta kai farmaki Iraq, inda aka kifar da gwamnatin Saddam Hussein.
An kama Saddam a ranar 13 Disamba, 2003 tare da gurfanar da shi a kotu a Iraq kan laifuffukan kisan kiyashi da sauran laifuffuka, sannan aka yanke masa hukuncin kisa.
Bayan farmakin 2003 karkashin jagorancin Amurka wanda ya rushe mulkin Saddam, an kafa mulki na wucin gadi ta hannun Coalition Provisional Authority.
Daga baya, a rana 28 ga Mayu 2004, Ayad Allawi ya zama Firaministan Wucin Gadi na Iraq, kafin a gudanar da zaɓuɓɓuka na ƙasa baki ɗaya.
Sai dai taimakon Amurka musamman na farmakin sojoji ya kara rura wutar rashin tsaro da farfadowar kungiyar ta'addanci ta ISIS a Iraq, kamar yadda jaridar Time ta kawo.

Source: Twitter
2. Afghanistan
Bayan shafe shekaru masu tsawo ana rikici a Afghanistan tun daga 2001, Amurka ta kai farmakin sojoji domin taimaka wa kasar wajen farfado da tsarin mulki da zaman lafiya.
Amurka ta jagoranci kai hare-hare da dama tare da dakarun Afghanistan wajen ƙwace iko daga hannun ‘yan ta’adda da kuma lalata ƙungiyoyin da ke barazana ga zaman lafiya.
A rahoton da ma'aikatar tsaron Amurka ta wallata a shafin yanar gizo, ta ce manufar ita ce idan Afghanistan ta samu kwanciyar hankali, za ta guje wa zama mafakar ‘yan ta’adda.
Daya daga cikin manyan matsalolin farmakin sojojin Amurka a Afganistan shi ne kashe fararen hula da raunata wasu da dama.
Duk da kalubale, horo da taimakon da aka bayar tsawon shekaru ya ƙara ƙarfin dakarun ƙasar Afghanistan kafin janyewar sojojin Amurka a shekara ta 2021.
Bayan janye sojojin Amurka, kungiyar Taliban ta kwace kusan dukan lardunan Afganistan, kuma ta kafa sabuwar gwamnati da sunan Islamic Emirate of Afghanistan.
Tsohon shugaban Afghanistan, Ashraf Ghani ya fice daga ƙasar bayan Taliban ta karbe ragamar mulki, kamar yadda jaridar PBS ta rahoto.
3. Libya
Kasar Libya na daya daga cikin kasashen da Amurka ta dauki matakin sojoji domin kawo daidaito da tsaro bayan hambarar da gwamnatin Mu'ammar Gaddafi a 2011.
Libya ta fada cikin rikici, rabuwar kai tsakanin gwamnatoci biyu, da yaduwar kungiyoyin ‘yan bindiga da masu tayar da kayar baya bayan kifar da Gaddafi, in ji rahoton jaridar Libya Review.

Source: Getty Images
A cikin wannan hali, gwamnatin Amurka ta kai dauki Libya ta fuskar tsaro da farmakin soji, domin taimaka wa kasar wajen farfaɗowa daga rikicin da ta fada.
Daya daga cikin manyan abubuwan da Amurka ta tura Libya shi ne tallafin sojojin sama da na ruwa wajen yakar kungiyoyin ta’addanci, musamman Islamic State (IS).
A 2016, karkashin Operation Odyssey Lightning, Amurka ta kai hare-hare ta sama don taimakawa gwamnatin National Accord (GNA) ta sake kwace birnin Sirte daga hannun IS.
Sai dai, ana ganin zaman lafiya zai tabbata a kasar ne idan ‘yan Libya suka haɗa kai, suka gina gwamnati ɗaya, kuma suka dogara da kansu wajen kawo gyara da adalci.
4. Syria
Tun bayan barkewar yakin basasa a Syria a shekara ta 2011, gwamnatin Amurka ta shiga cikin rikicin ta hanyoyi daban-daban.
Sojojin Amurka sun yi aiki tare da rundunar kasar Syria (SDF), wato haɗakar Kurds da Larabawa, wajen yaki da ISIS.
Wannan haɗin gwiwa ta taimaka wajen kwato birane da kauyuka, rage ƙarfin ISIS, da hana su sake karbe mulkin kasar.
Rahoton New York Post ya nuna cewa Amurka ta kai hare-hare ta sama da da ƙasa don lalata cibiyoyin ISIS da kare yankunan da aka kwato daga sake komawa hannunsu.

Source: Getty Images
Tun daga fara tsoma-bakin Amurka cikin yakin Syria, farmakin sama, amfani da jirage mara matuki da ƙungiyoyin haɗin gwiwa suka yi, an samu nasarori amma kuma sun jawo manyan matsaloli.
Rahotanni daga ƙungiyoyin kare hakkin ɗan Adam sun nuna cewa farmakin da sojojin Amurka suka kai Syria ya yi ajalin fararen hula da yawa.
A rahoton da Amnesty International ta wallafa shafinta na yanzar gizo, ta ce akalla fararen hula 300 suka mutu a harin da Amurka da kawayenta suka kai Syria tsakanin 2014 zuwa 2016.
5. Harin da Amurka ta kai wa Al-Awlaki
Anwar Al-Awlaki ɗan ƙasar Amurka ne, an haife shi a New Mexico, USA, a shekarar 1971. Mahaifinsa ɗan kasar Yemen ne kuma ya zama ɗan siyasa kuma malamin jami’a.
Awlaki ya yi karatu a Amurka, ya zama malamin addinin Musulunci (imam), sannan daga baya ya fara shahara a a duniya saboda hudubobinsa da ake yada wa a Intanet.
Daga baya hukumomin tsaron Amurka suka zarge shi da tallafawa al-Qaeda da shirya kai hare-hare a kasar.

Source: Twitter
A shekara ta 2011, sojojin Amurka suka kashe shi a wani harin jirgin yaki da suka kai a Yemen, kamar yadda jaridar Times of Israel ta ruwaito.
Abin da ya fi tayar da hankali shi ne, ba a gurfanar da Al-Awlaki a kotu ba, ba a tabbatar da laifinsa ta hanyar shari’a ba, amma duk da haka Amurka ta kashe shi a farmakin sama.
Wata biyu bayan kashe mahaifinsa (Oktoba 2011), wani harin jirgin sojojin Amurka a Yemen ya kashe dan Al-Awlaki mai suna Abdulrahman, dan shekara 16 tare da wasu ‘yan uwansa.
Gwamnatin Amurka ta ce ba shi ta nufa ba, "kuskuren sirri" aka samu, amma iyalinsa da lauyoyinsu suka ce babu adalci kuma ba a binciki lamarin yadda ya kamata ba.
Haka nan kuma sojojin Amurka sun kashe Nawar "Nora" al-Awlaki, 'yar Anwar al-Awlaki mai shekaru 8, a ranar 29 ga Janairu, 2017, a lokacin wani hari da aka kai a Yakla.

Kara karanta wannan
Kiristoci: Peter Obi ya fadi matsayarsa kan yunkurin Amurka na kawo farmaki Najeriya
Gwamnatin Amurka karkashin jagorancin Shugaba Donald Trump ta ce an kai harin kan kungiyar Al-Qa'ida amma ba don kashe yarinyar ba.
6. Farmakin sirrin kashe Osama a Pakistan
A ranar 11 ga Satumba, 2001, ‘yan ta’addan Al-Qa’ida suka kai mummunan hari da jiragen sama a Cibiyar Kasuwanci ta Duniya da kuma Pentagon, inda aka rasa rayukan mutane sama da 3,000.
Wannan hari ne ya zama mafi girma a tarihin Amurka, wanda ya sa kasar ta ayyana Yaƙin Duniya Kan Ta’addanci.
Bayan haka, Amurka ta fara aiki tare da ƙasashe da dama, ciki har da Pakistan, Afghanistan, da wasu ƙasashen Larabawa ta hanyar tallafin soja, kayan aiki, da bayanan leken asiri domin yaƙar ’yan ta’adda.

Source: Twitter
Ba tare da sanar da gwamnatin Pakistan ba, Amurka tashi da jiragen Black Hawk daga Afghanistan zuwa Abbottabad cikin dare, inda suka shiga gidan Osama, suka kashe shi, rahoton Al-Jazeera.
Duk da cewa sojojin Amurka sun kawar da Osama bin Laden da rage ƙarfin al-Qa’ida, amma hare-harensu ya kashe fararen hula da dama tare da jefa miliyoyin mutane cikin kunci.
Ya ƙara ƙiyayya da rashin fahimta tsakanin Amurka da musulmai kuma bai magance tushen ta’addanci, talauci, rashin ilimi, da rashin adalci ba.
Sojojin Amurka sun tsara kawo hari Najeriya
A wani rahoton, kun ji cewa rundunar sojin Amurka ta gabatar da cikakken shiri ga ma’aikatar yaki domin yiwuwar kai hare-hare Najeriya.
Rahotanni sun nuna cewa kwamandan rundunar sojin Amurka mai yaki a Afirka ya aika da na'ukan farmaki uku ga ministan ma’aikatar, Pete Hegseth, a farkon wannan makon.
A karkashin wannan tsari, Amurka za ta iya amfani da jiragen yaki masu linzami ko masu nisan zango domin kai hare-hare Arewacin Najeriya.
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Asali: Legit.ng






