Rashawa: Kotu Ta Yanke wa Tsohon Shugaban Kasa Hukuncin Zaman Gidan Yari a Faransa
- Tsohon shugaban Faransa Nicolas Sarkozy ya fara zaman gidan yari, inda ake sa ran zai yi watanni
- Kotu dai ta samu Sarkozy da laifin karbar kudin kamfen daga marigayi Muammar Gaddafi na Libya
- Sarkozy ya musanta zarge-zargen, yana mai cewa ba shi da laifi kuma gaskiya za ta yi halin ta nan gaba
Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida
Faransa - Kotu ta yanke hukuncin zaman gidan yari kan tsohon shugaban kasar Faransa, Nicolas Sarkozy.
Sarkozy ya zama shugaban kasa na farko daga wata kasar Tarayyar Turai (EU) da aka daure a gidan yari.

Source: Twitter
An daure tsohon shugaban Faransa
Wani bidiyo da jaridar AFP ta wallafa a shafinta na X ya nuna lokacin da aka shigar da Sarkozy gidan yarin La Santé da ke birnin Paris a ranar Talata.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Kotu ta samu Sarkozy, wanda ya jagoranci Faransa daga 2007 zuwa 2012, da laifin karbar haramtaccen kudin kamfen daga tsohon shugaban Libya, Marigayi Muammar Gaddafi.
An tabbatar da ganin Sarkozy, mai shekara 70, yana barin gidansa tare da rakiyar ’yan sanda a kan babura, kafin ya shiga gidan yari cikin tsaro mai tsauri.
An kuma rahoto cewa, ana shigar da tsohon shugaban kasar cikin gidan yarin, aka rika jiyo fursunoni suna ihu daga cikin dakunansu, suna cewa:
“Barka da zuwa, Sarkozy!. Sarkozy ya iso!”
"Ba ni da laifi" - Tsohon shugaban Faransa
Sai dai, a wani sakon da ya wallafa a shafinsa na X (tsohon Twitter) yayin da ake kai shi gidan yari, Sarkozy ya ce:
“Ba tsohon shugaban kasa ne ake kullewa a gidan yari a safiyar yau ba, sai dai mutum mai gaskiya. Ba ni da haufi, gaskiya za ta yi halinta.”
An yanke masa hukuncin daurin shekaru biyar a watan Satumba saboda hada baki wajen karbar kudin kamfen daga gwamnatin Gaddafi don zaben shugaban kasa na 2007.
Bayan hukuncin, Sarkozy ya ce:
“Zan kwana a gidan yari, amma ba tare da wani zullumi ba – ba zan ji wata kunya ba, don ban aikata laifin komai ba.”
Tsohon shugaban Faransa da masoyansa
Tun da safiyar Talata, magoya bayansa da iyalinsa sun taru a wajen gidansa, suna dauke da hotunansa cike da damuwa da halin da yake ciki.
Matarsa, Carla Bruni, ta rike hannunsa yayin da yake barin gida, lokacin da jama’a ke cewa:
“Nicolas! Nicolas! A saki Nicolas!”
Wasu kuma suka rera taken kasa na Faransa yayin da makwabta ke kallo daga tagoginsu.
Wata mata mai suna Flora Amanou (41) ta ce:
“Wannan rana ce mai cike da bakin ciki ga Faransa da dimokuradiyyarta.”

Source: Twitter
"Za a tsare shi tsawon makonni uku"
Lauyansa, Christophe Ingrain, ya tabbatar da cewa an gabatar da bukatar belinsa nan take, amma kotun daukaka kara na iya daukar wata biyu kafin ta yanke hukunci kan sakin nasa.
“Zai kasance a cikin gidan yarin na akalla makonni uku zuwa wata daya,” in ji Ingrain.
Rahotanni sun nuna cewa Sarkozy zai kasance cikin dakinsa mai matukar tsaro don gujewa hulɗa da sauran fursunoni.
Faransa za ta horar da NDLEA
A wani labarin, mun ruwaito cewa, Faransa za ta ba jami'an NDLEA horo kan kwarewar aiki, amfani a kayan aiki domin yakar ta’ammali da miyagun kwayoyi.
Laftanal Janar Regis Colcombet ya ce wannan matakin na daga cikin yarjejeniyoyin da aka cimma tsakanin Faransa da Shugaba Bola Tinubu.
Shugaban NDLEA, Janar Buba Marwa (Mai ritaya) ya bukaci karin horo kan dabarun aiki, binciken intanet da kuma fasahar zamani.
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng


