Madagascar: Halin da Ake Ciki da Sojoji Suka Kori Shugaban kasa daga Fadarsa

Madagascar: Halin da Ake Ciki da Sojoji Suka Kori Shugaban kasa daga Fadarsa

  • Rahotannin sun tabbatar da cewa majalisar dokoki a kasar Madagascar ta tsige shugaban kasar yayin zamanta
  • Rundunar sojojin Madagascar ta karɓi mulki bayan majalisar ta tsige shugaba Andry Rajoelina daga mukaminsa
  • Shugaban ƙasa Rajoelina ya bayyana cewa har yanzu yana kan mulki, ya kuma kira matakin sojojin a matsayin yunƙurin juyin mulki

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.

Antananarivo, Madagascar - Rundunar sojojin ƙasar Madagascar ta yi magana bayan tsige shugaban kasar a makon nan.

Rundunar ta tabbatar da cewa ta karɓi ragamar mulki bayan majalisar dokokin ƙasar ta kada ƙuri’a domin tsige shugaba Andry Rajoelina.

Sojoji sun kwace iko a kasar Madagascar
Shugaban Madagascar yayin faretin sojoji a kasar. Hoto: Chesnot.
Source: Getty Images

Rahoton Aljazerra ya tabbatar da haka inda ya ce hakan ya biyo bayan shafe makonni ana zanga-zangar adawa da gwamnatinsa.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Majalisa ta tsige Shugaban Madagascar Rajoelina

Majalisar dokokin ƙasar ta kada ƙuri’a domin tsige shugaban ƙasa bisa zargin sakaci da aikinsa, duk da cewa fadar shugaban ƙasa ta yi ƙoƙarin hana zaman majalisar.

Kara karanta wannan

Bakary: Dan adawar Kamaru ya ce ya kayar da Paul Biya a zaben shugaban kasa

Majalisar ta samu ƙuri’u 130 na goyon baya, sama da yadda kundin tsarin mulki ke buƙata, kafin kotun tsarin mulki ta tabbatar da tsige shugaban ƙasa da kuma ikon kwamandan CAPSAT.

Rajoelina, wanda ake cewa ya gudu zuwa waje, ya bayyana cikin wata hira cewa yana “cikin aminci” domin kare rayuwarsa, kuma ba zai sauka daga mulki ba.

Matasa sun yi zanga-zangar neman sauyi a Madagascar
Shugaban Madagascar da aka tsige, Rajoelina da matasa masu zanga-zanga. Hoto: FITA/AFP.
Source: Twitter

Madagascar: Fadar shugaban kasa ta yi martani

Wasu suna ta murna titunan babban birnin ƙasar Madagascar bayan kwamandan rundunar CAPSAT, wadda ta haɗu da masu zanga-zanga a karshen mako, ya bayyana cewa rundunarsu ce yanzu ke mulkin ƙasar.

Fadar shugaban ƙasa ta bayyana wannan mataki a matsayin “yunƙurin juyin mulki”, inda ta ce shugaba Rajoelina “yana nan daram a matsayin shugaban ƙasa.”

Rajoelina, mai shekara 51, ya ƙi amincewa da muradin masu zanga-zanga da ke neman ya sauka daga mulki saboda matsalar wutar lantarki da ƙarancin ruwa, lamarin da ya jawo ƙungiyoyi da dama su shiga jerin gwano tun daga 25 ga Satumba.

A gaban fadar shugaban ƙasa, kwamandan CAPSAT, Kanal Michael Randrianirina, ya karanta sanarwa da ta soke kundin tsarin mulkin ƙasar, yana mai cewa za a kafa kwamitin mulki da zai ƙunshi jami’an soji da ‘yan sanda.

Kara karanta wannan

Amupitan: Lauyoyi na shirin kawo cikas ga tabbatar da nadin shugaban INEC a majalisa

Ya ce:

“Mun karɓi mulki. Za mu kafa gwamnati ta farar hula bayan ‘yan kwanaki domin ci gaba da gudanar da mulkin ƙasa.”

Bayan haka, motocin yaƙi da na sojoji suna ci gaba da zagaye birnin, yayin da jama’a ke murna da daga tutoci suna taya su farin ciki, cewar Africanews.

Ana fama da yunwa a Madagascar

A baya mun kawo muku wani rahoton bincike da Legit Hausa tayi game da kasashen da suka fi fama da yunwa a Afirka.

Kasar Madagascar na daga cikin kasashen biyar da aka lissafo da suka cikin bala'in yunwa da ya ke tayar da hankula.

Madagascar ita ce ta uku a jerin kasashen Afirka biyar da suke cikin halin yunwa bayan Somalia da kuma kasar Chadi.

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 5 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.