Coronavirus: Madagascar ta bukaci Najeriya ta biya kudin maganin da ta aiko

Coronavirus: Madagascar ta bukaci Najeriya ta biya kudin maganin da ta aiko

Kasar Madagascar ta nemi Najeriya da ta biya Yuro 170,000 na adadin maganin gargajiya na cutar korona da ta aikowa gwamnatin tarayyar kasar a karshen makon da ya gabata.

A rahoton da jaridar The Nation ta ruwaito, har kawo yanzu ba a san iyaka adadin maganin da gwamnatin Madagascar ta turo wa Najeriya ba wanda ya ratso ta kasar Guinea Bissau.

Shugaban Guinea Bissau, Umaro Sissoco Embalo, wanda ya ziyarci shugaba Muhammadu Buhari a fadar Villa da ke birnin Abuja a ranar Asabar, shi ne ya kawo kasafin maganin na Madagascar da aka ware wa Najeriya.

Sai dai mun ji cewa shugaba Buhari yayin karbar kunshin maganin ya ce ba za a fara amfani da shi a kasar nan ba kai tsaye har sai kwararrun mahukunta da masana kimiya sun bayar da tabbaci a kansa.

Wata majiyar rahoto ta bayyana cewa, a yanzu Najeriya ta fahimci cewa, wannan magani da ta karba ba kyauta bane kuma an sanya mata farashi na makudan kudi sannan kuma har ta karbi daftari na biyan kudin.

Kasar Madagascar ta bukaci gwamnatin Najeriya ta biya Yuro 170,000 kimanin Naira 78, 200,000 kenan na kudin adadin maganin da ta aiko.

Shugaba Buhari yayin karbar bakuncin shugaban Guinea Bissau cikin fadar Villa a karshen makon da ya gabata
Shugaba Buhari yayin karbar bakuncin shugaban Guinea Bissau cikin fadar Villa a karshen makon da ya gabata
Asali: Twitter

Majiyar ta ce kuma dole sai Najeriya ta biya wannan kudi sanadiyar yadda kasar Madagascar ta samu madogara daga kungiyar kasashen Afirka AU.

Ta ce: "An nemi mu biya kudin magunguna da har yanzu ba a tabbatar da su ba kasar mu. Tunda kungiyar AU ta ba da umarnin rarraba magungunan zuwa kasashen Afirka, a yanzu ba mu da wani zabi face mu biya."

KARANTA KUMA: Coronavirus: Garkuwar jikin marasa lafiya kawai muke bunkasa wa - Farfesa Alonge

A wani rahoton da jaridar Daily Trust ta ruwaito a makon jiya, gwamnatin Najeriya ta ce ba ita ta nemi a kawo mata maganin korona na kasar Madagascar ba.

Gwamnatin ta ce shugaban kasar Madagascar ne ya aiko mata da maganin gargajiyar kyauta ba tare da ta kashe ko sisin kobo ba.

Sakataren Gwamnatin Tarayya kuma shugaban kwamitin kar-ta-kwana da fadar shugaban kasa ta kafa don yaki da cutar a Najeriya, Boss Mustapha, shi ne ya bayyana hakan cikin birnin Abuja a ranar Alhamis, 14 ga watan Mayu.

Sanarwar Sakataren Gwamnatin ta zo ne a yayin zaman karin haske kashi na 31 kan halin da ake ciki dangane da cutar korona a kasar.

Mista Mustapha ya ce Gwamnatin Madagascar ta turo da maganin Najeriya kyauta kuma ba tare da an nemi bukatar hakan ba.

Har ila yau dai Hukumar Lafiya ta Duniya, WHO ta na nan dai a kan bakanta na cewa kawo yanzu ba a samu wani maganin cutar korona ba, saboda haka mutane su guji amfani da maganin da ba shi da tabbas.

Hakan ya sanya WHO ta yi watsi da ikirarin da shugaban Madagascar ya yi na cewa maganin gargajiya da aka samar a kasarsa na iya warkar da masu cutar sarkewar numfashi ta korona.

Kasar Madagascar dai wani tsibiri ne a tsakiyar tekun Indiya da ke da nisan kilomita 400 daga gabashin Afirka, al’ummar kasar sun kai miliyan 26 tun kidayar da aka gudanar a shekarar 2018.

Madagascar ta binciko wannan magani na gargajiya daga wani ganye wanda ta sarrafa shi kamar ganyen shayi, kuma ta sanya masa suna COVID-Organics.

A ranar Litinin, 20 ga watan Afrilun bana, shugaban kasar Andry Rajoelina ya kaddamar da maganin, wanda suke amfani da shi wajen magance cutar ta korona.

A zahiri dai wannan magani yana dauke da sunadarin artemisia, wanda akasari ake amfani da shi don maganin zazzabin cizon sauro, kuma Cibiyar bincike ta kasar ita ce ta binciko maganin.

Duk da tasirin wannan maganin a kasar Madagascar na warkar da masu cutar korona, Hukumar Lafiyar na ci gaba da jaddada cewa, maganin bai samu tabbacin masana kimiyya ba saboda haka bai inganta ba.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel