Da Dumi-Dumi: An dakile yunkurin kisar gillar da aka yi niyyar yiwa shugaban kasar Madagascar
- An kama wasu mutane da suke shirin kashe shugaban kasar Madagascar, Andry Rajoelina
- Jami'an tsaro na kasar ta Madagascar sun ce wadanda aka kama akwai yan kasar da yan kasar waje
- Ofishin babban mai bincike na kasar Madagascar ta tabbatar da kamen tana mai cewa an fara bincike
Masu bincike a ofishin babban mai bincike na kasar Madagascar sun ce an dakile yunkurin kisar gilla kan Shugaba Andry Rajoelina, sun kuma kama mutane da dama ciki har da yan kasar waje, Daily Trust ta ruwaito.
The Punch ta ruwaito cewa akwai yan kasar Faransa biyu cikin wadanda aka kama da zargin kashe shugaban kasar kamar yadda majiyoyi na diflomasiyya suka bayyana a ranar Talata.
Wani sanarwar da Berthine Razafiarivony ta fitar a ranar Talata ta ce:
"An kama yan kasar Madagascar da yan kasar waje da dama a ranar Talata 20 ga watan Yuli, a wani binciken da aka yi kan harin da aka kaiwa hukumar tsaro ta kasar."
Ta kara da cewa:
"A wannan matakin na bincike, da ake kan yi, ofishin babban mai bincike na kasar ta bada tabbacin yin karin bayani a kan lamarin."
A ranar bikin zagayowar ranar samun yancin kasar a ranar 26 ga watan Yuni, jami'an tsaro na kasar sun sanar da cewa sun dakile yunkurin kashe mai gidansu, General Richard Ravalomanana, wanda kuma na hannun daman shugaban kasa ne.
An Kama Ƴan Ƙasar Isra’ila 3 Da Ke Da Alaƙa Da Ƙungiyar IPOB Ta Nnamdi Kanu
A wani labarin daban, hukumar yan sandan farin kaya ta DSS ta kama wasu mutane uku yan asalin kasr Isra'ila masu shirya fim kan zarginsu da alaka da kungiyar 'yan aware masu son kafa kasar Biafra wato IPOB, Daily Trust ta ruwaito.
Yan kasar na Isra'ila, Rudy Rochman, dan gwagwarmaya na Isra'ila; Noam Leibman, mai hada fim da David Benaym, Dan jarida dan kasar Faransa-Isra'ila, an kama su ne a ranar 9 ga watan Yuli lokacin da suka ziyarci kauyen Ogidi da ke karamar hukumar Idemili ta jihar Anambra.
An ce yan kasar wajen sun baro fili n tashin jirage na Ben Gurion a Isra'ila ne a ranar 5 ga watan Yuli sannan suka iso Nigeria a ranar 6 ga watan Yuli domin nadar wani fim mai suna 'We Were Never Lost'.
Asali: Legit.ng