Asiri Ya Tonu: An Fallasa Yadda Tsohon Manajan NNPCL Ya Tura N3.1bn zuwa Amurka
- Wata kotun tarayyar Amurka, ta samu tsohon babban manajan kamfanin NNPCL da laifin karɓar rashawar dala miliyan 2.1
- An samu Paulinus Okoronkwo da laifuffukan da suka haɗa da satar kuɗi, karya dokar haraji da kuma kawo tsaiko a bincike
- Yayin da shari'ar a ta zo karshe a ranar 1 ga Disamba, 2025, an bayyana irin hukuncin da alkalin zai iya yanke wa Okoronkwo
Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida
Amurka – Wata kotun tarayya a jihar California ta samu Paulinus Iheanacho Okoronkwo, tsohon babban manajan kamfanin NNPCL, da laifin karɓar rashawar dala miliyan 2.1 da ta shafi hakar mai a Najeriya.
Okoronkwo, mai shekara 58, ya kasance ɗan asalin Najeriya kuma mai katin shaidar zama ɗan ƙasar Amurka, kuma yana aikin lauyanci a birnin Los Angeles.

Source: Twitter
Tuhumar da ake yi wa tsohon jami'in NNPCL
Kotun ta tabbatar da cewa Okoronkwo ya aikata laifuffuka da dama ciki har da laifin satar kuɗi sau uku, kauce wa biyan haraji sau ɗaya, da kuma kawo tsaiko a bincike, inji rahoton Daily Trust.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Bayan shari’ar da ta ɗauki kwana huɗu a watan Agusta, masu gabatar da ƙara sun gabatar da hujjoji cewa Okoronkwo ya karɓi dala miliyan 2.1 a Oktoba, 2015 daga kamfanin Addax Petroleum, reshen kamfanin Sinopec na kasar Sin.
Bayanan kotu sun nuna cewa an tura kuɗin zuwa asusun lauyan kamfaninsa da ke Los Angeles a matsayin kuɗin bada shawara, duk da cewa ba haka abin yake ba.
Masu gabatar da ƙara sun shaida wa kotu cewa an ajiye kudin a kamfanin Okoronkwo ne domin Addax ya ki biyan harajin kudin a harkar hakar mai da yake yi a Najeriya.
Bincike ya gano cewa shugabannin Addax sun yi ƙarya a kan ma’amalar, sun ruɗi masu duba kuɗi, sannan suka kori ma’aikatan da suka nuna basu gamsu da harkallar ba..

Kara karanta wannan
Kotun Amurka ta kama tsohon shugaba a NNPCL da cin hanci, zai sha daurin sama da shekaru 10
Okoronkwo ya yi amfani da kudin rashawa
Rahotanni sun ƙara nuna cewa a watan Nuwamba 2017, Okoronkwo ya yi amfani da kusan dala 983,000 wajen biyan kuɗin farko na sayen wani gida a garin Valencia, California.
Premium Times ta kuma rahoto cewa bai bayyana wannan kuɗin a matsayin kudin shiga a bayanin harajin kamfaninsa na shekarar 2015 ba.
A 2022, lokacin da jami’an tsaro suka titsiye shi, ya ƙi yarda cewa kuɗin nasa ne, ya ce na wani abokin harkarsa ne, lamarin da ya kawo tsaiko a binciken.

Source: Getty Images
Hukuncin da tsohon jami'in NNPCL zai fuskanta
Alƙalin kotun, John F. Walter, wanda ya jagoranci shari’ar, ya sanya 1 ga Disamba, 2025, a matsayin ranar da zai yanke hukunci.
Okoronkwo na iya fuskantar ɗaurin shekaru 25 a kurkuku: shekaru 10 kan laifin satar kuɗi, shekaru 10 kan hana bincike tafiya, da shekaru 5 kan kauce wa biyan haraji.
Wannan shari'ar rashawar ta zama mai girma da ta shafi bangaren mai a Najeriya tare da kamfanonin ƙasashen waje, abin da zai iya girgiza sahihancin wannan fanni.
Tsohon shugaban NNPCL ya shiga hannun EFCC
A wani labarin, mun ruwaito cewa, tsohon shugaban NNPCL, Mele Kyari, ya shiga hannun hukumar da ke yaki da cin hanci da rashawa ta EFCC a Abuja.
An ce jami'an EFCC sun titsiye Mele Kyari a ofishinsu, inda ya amsa tambayoyi kan yadda wasu al'amura suka gudana a NNPCL lokacin da yake shugabantar kamfanin.
A baya kotu ta taba bayar da umarnin rufe asusun banki da aka danganta su da Mele Kyari bayan EFCC ta bukaci hakan, kan wani binciken rashawa da take yi.
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Asali: Legit.ng

