Kotun Amurka Ta Kama Tsohon Shugaba a NNPCL da Cin Hanci, Zai Sha Daurin sama da Shekaru 10
- Tsohon Janar Manaja a kamfanin mai na kasa, NNPCL, Paulinus Okoronkwo ya ga ta kansa bayan kotun Amurka ta kama shi da cin hanci
- Kotun ta tabbatar da cewa Paulinus Okoronkwo ya karbi cin hanci daga wani kamfanin China domin ba shi damar hakar danyen mai
- Baya ga wannan laifin, an kuma kama shi da kauce wa biyan haraji da kuma halatta kudin haram, har da kawo tsaiko a bincikensa
A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.
US, California – Wata kotu a ƙasar Amurka ta samu tsohon Janar Manaja a kamfanin mai na kasa, NNPCL, Paulinus Okoronkwo, da laifin karɓar rashawa ta Dala miliyan 2.
Kotu ta tabbatar da cewa ya karbi cin hancin ne daga kamfanin man fetur na Addax Petroleum, wani reshe na kamfanin Sinopec mallakin gwamnatin kasar China.

Source: Facebook
The Cable ta wallafa cewa kotun ta samu Okoronkwo da laifin halatta kuɗin, kauce wa biyan haraji, da kuma hana bincike ya gudana yadda ya kamata.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Tsohon Janar Manajan NNPCL ya shiga matsala
Arise News ta wallafa cewa lauyoyin gwamnati sun bayyana cewa an tura kuɗin ne cikin asusun lauyoyi mallakar ofishin Okoronkwo da ke Los Angeles a watan Oktoban 2015.
An mika kudin ne da sunan "kudin shawarwari", duk da cewa a gaskiya rashawa ce domin kamfanin Addax ya samu damar hakar danyen mai cikin sauki a Najeriya.
Masu gabatar da ƙara sun gabatar da shaidu cewa shugabannin Addax sun ƙirƙiri takardu na karya domin su nuna cewa kudin na aiki ne da lauyoyi.

Source: Facebook
Sannan kamfanin ya kori wasu daga cikin ma'aikatansa da ya nemi bayani kan sahihancin takardun da dalilin da zai sa a biya kudin.
Wata sanarwa daga ofishin Lauyan Gwamnatin Tarayya a yankin Central District na California ta bayyana cewa:

Kara karanta wannan
Jerin jihohin da mafi karancin albashi ya kusa N100,000 ko sama da haka a Najeriya
“Addax ta ƙididdige cewa za ta iya rasa biliyoyin Dala idan ba ta samu kwangilar hakar mai a Najeriya ba, shi ya sa ta yi amfani da wannan hanyar domin samun amincewar hukumomi ta hannun Okoronkwo.”
Tsohon Janar Manajan NNPCL ya daƙile binciken
A cewar rahoton, Okoronkwo ya yi amfani da $983,200 daga cikin kudin haramun wajen siyan gida a Valencia, California a watan Nuwamba 2017, amma ya ƙi bayyana kuɗin a takardar harajin 2015.
Baya ga haka, a shekarar 2022, ya yi ƙarya ga jami’an bincike, yana cewa bai taɓa amfani da kuɗin wajen siyan gida ba.
Mai shari'a Jaji John Walter ya sanya ranar 1 ga Disamba don yanke hukunci yayin da Okoronkwo na iya fuskantar shekaru 10 a gidan yari kan kowane laifi na halatta kuɗin haram.
Sai kuma karin wasu shekaru 10 a kan hana bincike, da shekaru biyar a kan kauce wa biyan haraji da ake zarginsa da aikata wa.
An yi zanga-zangar dawo da tsohon shugaban NNPCL
A wani labarin, kun ji wasu ‘yan Najeriya sun gudanar da zanga-zanga a gaban ofisoshin jakadancin ketare a dalilin tsohon shugaban NNPCL, Mele Kyari.
Wadannan mutane sun yi zargin cewa Kyari ya tsere daga Najeriya domin kaucewa fuskantar shari’a kan almundahana da wawurar kudin kamfanin na man fetur.
Kungiyar ta bukaci hukumomin Birtaniya su dage wajen ganin gaskiya ta yi halinta a tuhumar da ake yi wa Kyari wanda aka maye gurbinsa a kwanakin baya.
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng

