Wata Sabuwa: Isra'ila na Neman Jawo Yaki, Ta Harba Bama Bamai kan Kasar Qatar
- Isra'ila ta yi yunkurin kashe shugabannin kungiyar Hamas da suka je tattaunawa kan zaman lafiya a birnin Doha na Qatar
- Rundunar sojin Isra'ila ta tabbatar da kai hari kan yankin da jagororin Hamas ke zaune a babban birnin kasar Qatar ranar Litinin
- Qatar ta yi Allah wadai da wannan dabi'a ta Isra'ila, tana mai cewa ba za ta lamunci a yi barazana ga tsaron kasar ba
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Doha, Qatar - Isra’ila ta tabbatar da kai wani mummunan hari a Doha, babban birnin kasar Qatar a daren jiya Litinin, 8 ga watan Satumba, 2025.
Kasar yahudawan watau Isra'ila ta bayyana cewa ta harba bama-bamai kan birnin Doha ne da nufin sheke wasu shugabannin kungiyar Hamas da ke Qatar.

Source: Getty Images
Rahotanni daga Al Jazeera, gidan talabijin na Qatar, sun bayyana cewa fashe-fashe sun girgiza unguwar Katara, yankin da aka kai harin a cikin birnin Doha.
Me yasa Isra'ila ta kai hari cikin Qatar?
An ruwaito cewa jagororin Hamas sun je Doha ne domin tattaunawa kan kudurin yarjejeniyar tsagaita wuta a Gaza na baya bayan nan.
Sojojin Isra’ila sun ce harin wani yunkuri ne na kashe shugabannin Hamas da suka dade suna jagorantar ayyukan kungiyar.
Rundunar ta ce za ta ci gaba da daukar matakan da suka dace domin “murkushe kungiyar ta’addanci ta Hamas.”
Gwamnatin Qatar ta yi tir da harin Isra'la
Sai dai gwamnatin Qatar ta yi Allah wadai da harin, tana mai bayyana shi a matsayin “laifi da ya saba wa dokokin kasa da kasa.”
Mai magana da yawun ma’aikatar harkokin wajen Qatar, Majed Al Ansari, ya bayyana cewa:
“Wannan harin ya saba wa ka’idoji da dokokin kasa da kasa, kuma barazana ce ga tsaron Qatar da mazaunanta. Isra’ila na nuna halin ganganci da rashin mutunta kasashe.”
Al Ansari ya kara da cewa ginin da Isra'ila ta kai hari shi ne masaukin da aka bai wa mambobin kwamitin zaman lafiya na Hamas.

Source: Twitter
Qatar na kokarin sulhunta Isra'ila da Hamas
Ya tabbatar da cewa Qatar ba za ta lamunci irin wannan dabi’a ta Isra’ila ba, inda ya ce an fara gudanar da bincike, kuma za a bayyana karin bayani daga baya.
Qatar na taka muhimmiyar rawa a tattaunawar sulhu tsakanin Hamas da Isra’ila tare da hadin gwiwar Amurka, babbar mai goyon bayan Isra’ila, in ji rahoton BBC News.
Rahotanni sun nuna cewa shugabannin Hamas da Isra'ila ta kai wannan hari domin kashe su suna cikin Doha domin ci gaba da tattaunawar zaman lafiya.
Faransa da Saudiyya za su nemawa Falasdinu yanci
A baya, kun ji cewa shugaban Faransa, Emmanuel Macron, da Yariman Saudiyya, Mohammed bin Salman, za su jagoranci taron nemawa Falasdinawa yanci.
Hakan na zuwa ne yayin da aka shirin taron kasa da kasa da zai gudana a birnin New York a ranar 22 ga watan Satumba 2025.
Macron ya kuma yi tsokaci kan matakin Amurka na hana jami’an Falasdinu shiga kasar domin halartar taron, wanda ya kira da abin da bai dace ba.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng

