Ta Haura N1m: Abubuwa 10 da Ya Kamata Ku Sani game da Sababbin Wayoyin iPhone 17
- Kamfanin Apple ya sanar da fitar da sababbin wayoyin iPhone 17 da suka fi na baya sirantar jiki, karfin batiri da kuma kyawun launi
- Farashin sababbin wayoyin iPhone 17 zai fara ne daga ₦1.3m a Najeriya, kuma za a fara sayar da su a duniya daga karshen Satumba
- Legit Hausa ta jero muhimman abubuwa 10 da ya kamata ku sani game da iPhone 17, iPhone 17 Air, iPhone 17 Pro da iPhone 17 Pro Max
Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida
India - Daga fitowar iPhone ta farko zuwa sababbin wayoyin zamani, kamfanin Apple ya sake ɗaukar hankali yayin da ya ƙaddamar da iPhone 17 series.
Ga masoya Apple, za a iya cewa, kamfanin ya share masu hawa a bana, domin wayoyin iPhone 17 sun zo da siririn jiki, ingantattun kyamarori, da kuma batir mai karfi.

Source: UGC
Apple ya kaddamar da wayoyin iPhone 17
Rahoton The Economic Times ya nuna cewa rukunin wayoyin iPhone 17 da za a kaddamar a yau Talata, sun hada da: iPhone 17 normal, iPhone 17 Air, iPhone 17 Pro, da iPhone 17 Pro Max.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Yayin da za a fara sayar da su a duniya a karshen Satumba, 2025, a na sa ran farashinta zai fara daga $1,099 (₦1.6m) a Najeriya, amma zai danganta da nau'in wayar da girman kwakwalwarta.
An ce an samu karin $100 kan iPhone 16 Pro da aka fara sayarwa a baya, kuma hakan ya faru ne saboda sauya karfin ajiyarta daga 128GB zuwa 256GB a sabuwar iPhone 17 Pro.
Baya ga wayoyin iPhone 17 da za a fara sayarwa, hakazalika, kamfanin Apple zai kaddamar da sabon agogon Apple Watch, da na'urar sauraroron sauti ta AirPods da aka sabunta.
Farashin sababbin wayoyin iPhone 17
- iPhone 17: Farashinta zai fara daga $799 (₦1.2m)
- iPhone 17 Air: Farashinta zai fara daga $899 and $949 (₦1.5m da ₦1.43m)
- iPhone 17 Pro: Farashinta zai fara daga $1,099 (₦1.6m)
- iPhone 17 Pro Max: Farashinta zai fara daga $1,199 (₦1.8m)
Abubuwa 10 game da wayoyin iPhone 17
Ga masoya wayoyin iPhone, ga wasu muhimman abubuwa 10 da ya kamata ku sani game da sababbin wayoyin iPhone 17.
1. Mafi sirintar iPhone
iPhone 17 Air tana da kaurin 5.5mm kacal, wanda ya sa ta zama wayar iPhone mafi siranta da kamfanin Apple ya taɓa yi a tarihi.
2. An samar da su a Indiya
A karon farko a tarihi, ana samar da dukkanin nau'ikan iPhone 17 a Indiya, bisa haɗin gwiwa da kamfanonin Foxconn da Tata.
3. Ingantaccen manuni
Ana sa ran kowane nau'in iPhone 17 zai zo da allon manuni na OLED na 120Hz, wanda ke sa saurin tabawa, yin sama da kasa da kuma buga wasanni.
4. Kamarar gaba mai karfi
An inganta kamarar gaba zuwa megapixels 24 don ɗaukar hotuna da kuma kiran bidiyo masu kyau, inji rahoton Times of India.

Source: UGC
5. Sabon tsarin kamarar baya
Nau'ikan iPhone 17 Pro da Pro Max sun sami sabon tsarin kamarorin baya da suka zo a kwance kuma za su iya ɗaukar bidiyo a cikin 8K tare da karfin zuƙo hoto har zuwa 8x.
6. Babban batiri ga Pro Max
Ana sa ran iPhone 17 Pro Max za ta zo da batiri mai ƙarfin 5,000mAh, wanda shine mafi girma da aka taɓa samu a wayar iPhone.
7. Sabbin kayayyaki
Ana sa ran kamfanin Apple zai canza amfani da karfe mai nauyi na Titanium, ya koma karfe mai sauƙin amfani (aluminium) a nau'ikan Pro don sa wayoyin su zama marasa nauyi da kuma kyau.
8. Na’urar sarrafa waya mai sauri
Sabuwar na'urar A19 ce za ta zamo mai sarrafa iPhone 17 da Air, yayin da nau'ikan Pro kuma za su kasance da na'urar A19 Pro mai sauri da inganci.
9. Babu nau'in 'Plus' a wannan shekara
Kamfanin Apple ya cire nau'in 'Plus' a wannan shekara. A maimakon haka, iPhone 17 Air ce ta maye gurbinsa, wadda ke tsakanin nau'ukan wayar ta asali da kuma Pro.
10. Sabbin kalolin jiki
An kyautata zaton cewa launukan tsanwa da kore na daga cikin sababbin launukan wayoyin iPhone 17.

Kara karanta wannan
Duniya ta yi sabon attajirin da ya fi kowa kudi, an sha gaban Elon Musk mai N570tr
Ko talaka zai iya sayen iPhone?
Legit Hausa ta tattauna da wasu 'yan Arewa, wadanda wasusun ma'aikata ne kan ko za su iya tara kudin sayen sabuwar iPhone 17.
Amina Lawal, da ke sana'ar dinki, ta ce:
"Ko da wasa, ba zan ma gwada ba. Duk so na da waya, ba zan iya cire Naira miliyan 1.8 na sayi iPhone 17 ba. To balle a ce wai har in rika tara N70,000 a wata, gwanda na ci a ciki na gaskiya."
Imram Yunusa, daga Funtua, ya ce:
"Duk da albashi na ya haura N70,000, amma gaskiya ba zan iya yin asusun sayen iPhone 17 ba, wannan ba irin wayarmu ba ce, ta masu samu sama da N500,000 ce a wata."
Amma, Nafisa Kabir, da ke jihar Bauchi, ta ce:
"Sosai ma, zan iya. Ai wallahi, ko da bashi ne sai na hada kudin nan. Ni fa ka san, ba na so ana yin abu ana bari na a baya, da a ba ni labari, gwanda ni na bayar, yawwa. Don haka, tsaf zan tara kudin. Kai ni tuni na fara taru, zan bayar da tawa, iPhone 15, in yi ciko, me ya fi raina?."
Talaka zai shekara 3 kafin ya saye iPhone
A wani labarin, mun ruwaito cewa, sai talakan Najeriya ya shafe shekara uku yana tara N30,000 duk wata kafin ya iya sayen iPhone 14.
Wannan lissafin, an yi shi ne a shekarar 2022, lokacin da kamfanin Apple ya saki sabababbin wayoyin iPhone 14, kuma lokacin mafi karancin albashi yana a N30,000.
A lokacin, an rahoto cewa, farashin iPhone 14 Pro a Najeriya ya kai NGN1,440,000 a jihar Legas da kuma NGN1,540,000 a wajen jihar (6GB RAM + 256GB ROM.)
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Asali: Legit.ng



