Sabbin wayoyin salular da kamfanin Apple ya fitar, 'yan Najeriya suna rububi

Sabbin wayoyin salular da kamfanin Apple ya fitar, 'yan Najeriya suna rububi

- 'Yan Najeriya akwai karyar babbar waya

- Najeriya tafi kowacce kasa yawan ta;lakawa a duniya

- Wayoyin suna iya sayawa mutum mota

Sabbin wayoyin salular da kamfanin Apple ya fitar, 'yan Najeriya suna rububi
Sabbin wayoyin salular da kamfanin Apple ya fitar, 'yan Najeriya suna rububi
Asali: Depositphotos

Kamfanin Amurka mai qera wayoyin salula na zamani, ya fidda sabbin wayoyin salula wadanda suka zarta na baya a kyau, qarko da zamanancewa, a cewarsa.

Sai dai kamar yadda aka sani, 'yan Najeriya na kan gaba wajen harigido da rububin sayen wadannan wayoyi, wadanda kudinsu ya doshi miliyan daya na nairori.

Ita dai kasar Najeriya, kasa ce da tafi kowa yaan talakawa da marasa aiki yi da kuma yawan marasa ilimin tattalin arziki, amma hakan bai hana masu son holewa sheqe ayarsu ba.

DUBA WANNAN: Banbancin addini ya raba aure

Wayoyin, wadanda ake kira iphone X series, XS, S Max sun fi kowacce tsada, inda kowacce daya kan kai kudi har $999, wanda yake kusan N360,000 na nairori.

Mafi karancin albashi a kasar nan har yanzu N18,000 ne, kuma N400,000 zata saya wa mai karamin karfi motar hawa ko tasi.

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel