Wayar N750,000 da Apple tayi sun fara kamawa da wuta kamar yadda na Samsung suka yi a baya

Wayar N750,000 da Apple tayi sun fara kamawa da wuta kamar yadda na Samsung suka yi a baya

- Wani mutum ya bayyana yanda wayar sa kirar IPhone Xs Max ta kone

- Yayi wa kamfanin na Apple rahoton abinda ya faru

- Wayar dai ta kama da wuta ne a cikin aljihun wandon sa

Wayar N750,000 da Apple tayi sun fara kamawa da wuta kamar yadda na Samsung suka yi a baya
Wayar N750,000 da Apple tayi sun fara kamawa da wuta kamar yadda na Samsung suka yi a baya
Asali: UGC

Wani mutum ya bayyana yanda wayar sa kirar IPhone Xs Max ta kone.

An bayyana cewa wannan abu ya faru ne a ranar 12 ga watan Disemba a kusa da Columbus dake Ohia.

Wayar N750,000 da Apple tayi sun fara kamawa da wuta kamar yadda na Samsung suka yi a baya
Wayar N750,000 da Apple tayi sun fara kamawa da wuta kamar yadda na Samsung suka yi a baya
Asali: Instagram

Kamfanin Apple na fuskantar barazana a sanadiyyar wani mutum da Ohio daya bayyana cewa wayar sa kirar IPhone Xs Max wadda take da sati Uku a wajen sa ta kama da wuta a cikin aljihun wandon sa.

Wayar N750,000 da Apple tayi sun fara kamawa da wuta kamar yadda na Samsung suka yi a baya
Wayar N750,000 da Apple tayi sun fara kamawa da wuta kamar yadda na Samsung suka yi a baya
Asali: Facebook

Josh Hillard dan Columbus ya bayyana cewa ya fara jin zafi mai yawa da kuma kauri yana fitowa daga cikin wayar tashi daga baya kuma ta fara fitar da Kore da Yellow din hayaki.

Wayar N750,000 da Apple tayi sun fara kamawa da wuta kamar yadda na Samsung suka yi a baya
Wayar N750,000 da Apple tayi sun fara kamawa da wuta kamar yadda na Samsung suka yi a baya
Asali: Instagram

Na gaggauta fita daga inda nake sannan nayi saurin cire takalma na da wando inda wani abokin aikina ya taimakamin wajen kashe wutar.

Duk da cewar an kashe wutar wani waje a wando na ya kone sannan na samu rauni a duwawu na.

DUBA WANNAN: Dalilin da yasa ake so ku baiwa jarirai nono-zalla har wata shida

Hillard ya kara da cewa yayiwa kamfanin na Apple rahoton abinda ya faru inda wakilan kamfanin suka bashi wata wayar,amma a halin yanzu yana kokarin daukar matakin daya kamata akan kamfanin .

Wannan shine karo na farko da waya kirar IPhone Xs Max ta kama da wuta amma ba shine karo na farko ba ga ragowar wayoyi.

Ba da dadewa ba Samsung suka daina samar da Galaxy Note 7 a dalilin kamawa da wuta da takeyi

Shafin NAIJ.com Hausa ne ya koma LEGIT.ng Hausa

Latsa kuga sabuwar manhajar Legit.ng Hausa a wayarku ta salula: https://play.google.com/store/apps/details?id=ng.legit.hausa&hl=en

Shafukanmu na dandalin sada zumunta sune:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel