Rasha Ta Samar Da Rigakafin Cutar Daji, An Bayyana Fasahar Da Ta Yi Amfani da Ita

Rasha Ta Samar Da Rigakafin Cutar Daji, An Bayyana Fasahar Da Ta Yi Amfani da Ita

  • Bayan shafe shakara da shekaru, masana kimiyya a Rasha sun samar da sabon rigakafin cututtukan daji mai suna "Enteromix"
  • Maganin rigakafin ya dogara ne da fasahar mRNA, wadda aka yi amfani da ita a wasu mgungunan rigakafin COVID-19
  • An ce gwajin farko ya nuna cewa maganin yana rage girman cutar daji da kuma inganta tsawon rayuwar masu fama da cutar
  • Dr. Shamsuddeen Abubakar daga Katsina, ya ce karancin kudi, rashin dakunan bincike na zamani ke dakile samar da rigakafi a Najeriya

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Moscow - Masana kimiyya a ƙasar Rasha sun ƙirƙiro sabon maganin rigakafin cutar daji wanda a yanzu ya kai matakin da za a iya amfani da shi kan marasa lafiya.

Hukumar Kula da Lafiya da Ilimin Halittu ta Tarayyar Rasha (FMBA), ta sanar da cewa, asibitoci za su fara amfani da sabon rigakafin, bayan amincewa da shi.

Kara karanta wannan

'Abubuwa 4 ne ke rura wutar ta'addanci,' Gwamna Uba Sani ya nemo mafita ga Arewa

Masana kimiyya a Rasha sun samar da sabon rigakafin cutar daji, mai suna Enteromix
Masana sun samar da sabon rigakafin cutar daji a kasar Rasha. Hoto: Wilpunt, THOM LEACH / SCIENCE PHOTO LIBRARY
Source: Getty Images

Rasha ta samar da rigakafin cutar kansa

Shugabar FMBA, Veronika Skvortsova, ta bayyana hakan a taron tattalin arziki na Gabas, kamar yadda kamfanin dillancin labarai na Rasha, TASS ya ruwaito.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Maganin rigakafin, mai suna Enteromix, ya dogara ne da fasahar mRNA—irin wacce aka yi amfani da ita a wasu magungunan rigakafin COVID-19.

Madadin amfani da kwayar cuta da aka raunana, maganin rigakafin mRNA yana koya wa kwayoyin halittar jikin mutum su samar da sinadarin da ke haddasa maganin cutar daji.

Skvortsova ta ce an samar da maganin rigakafin, bayan bincike na shekaru da dama, ciki har da gwajin farko na shekaru uku da ake bukata.

Sakamako ya nuna maganin ya na aiki

Gwajin ya nuna cewa maganin yana da aminci har ma da tasiri ga marasa lafiya, kuma yana saurin yin aiki, a kan cutar daji.

A wasu lokuta, tsiron cutar daji na raguwa a hankali da kashi 60% zuwa 80%, ya danganci irin nau'in cutar dajin.

Kara karanta wannan

Tinubu ya waiwayi daliban da aka sace lokacin Jonathan, ya ba su tallafin N1.85bn

Masu bincike sun kuma lura da yadda tsawon rayuwar mutanen da aka yi wa gwajin ya karu, inji rahoton India Today.

Wani muhimmin abu game da sabon maganin rigakafin shi ne cewa za a tsara shi ga kowane marar lafiya, daidai da RNA na mutum. Ana ɗaukar maganin a matsayin wani sabon ci gaba a fannin lafiya.

Masana kimiyya a Rasha sun ce yanzu za a iya fara amfani da wannan rigakafi ga mutane a asibitoci.
Wasu masana kimiyya suna nuna gwajin da suka yi a dakin gwaje gwaje. Hoto: Getty Images
Source: Getty Images

Za a fara gwaji kan masu cutar kansa

An ce za a fara gwajin maganin ne a kan masu cutar daji ta hanji, wanda ke nufin cutar daji ta babban hanji.

Ana kuma ci gaba da aiki kan maganin cututtukan glioblastoma, wata cutar daji ce mai saurin girma a kwakwalwa, da kuma wasu nau'ikan cutar daji ta melanoma (cutar daji ta fata mai tsanani), ciki har da cutar melanoma ta ido.

An sanar da hakan ne a yayin babban taron tattalin arziki na Gabas karo na 10 a Vladivostok, wanda ya samu halartar baki sama da 8,400 daga kasashe sama da 75.

Me ya sa ba a samar da rigakafi a Najeriya?

Kara karanta wannan

Yadda shugaba Tinubu ke yawan nadin mukamai ya warware daga baya

A zantawar Legit Hausa da Shamsuddeen Abubakar, wani malamin asibiti daga Katsina, kan abin da ya sa Najeriya ba ta iya kirkirar rigakafin cututtuka, kamar cutar daji, da sauransu, ya ce:

“Babbar matsalar Najeriya ita ce ƙarancin kayan bincike da cibiyoyi na zamani da za su tallafa wa masana.
"Uwa uba,, kuɗin da gwamnati ke warewa ga kiwon lafiya bai wuce kashi 5% ba, alhali bincike kadai yana bukatar kuɗaɗe masu yawa, balle a zo maganar gwaje gwaje.
"Haka kuma, yawan ficewar ƙwararrun masana zuwa ƙasashen waje da ƙarancin saka hannun jari daga manyan kamfanonin magunguna suna ci gaba da jinkirta ci gaban samar da rigakafi a nan Najeriya."

Amurka ta kirkiro rigakafin HIV

A wani labarin, mun ruwaito cewa, hukumar FDA ta amince da lenacapavir (Yeztugo), matsayin allurar rigakafin kamuwa da cutar HIV.

Yayin da ake gwaje-gwaje, allurar ta nuna tasiri na 100% ga mata da 96% ga maza masu jima'i da maza, kuma yana ɗorewa a jiki fiye da PrEP.

UNAIDS ta yi kira ga kamfanin Gilead da ya rage farashin lenacapavir daga $28,218 zuwa tsakanin $25-$46 don ya zamo mai araha ga kowa.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza (Hausa Editor) Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i. Imel: sanihamzafuntua@gmail.com