Duk wanda ya kirkiro rigakafin Coronavirus zai samu N36m - FG

Duk wanda ya kirkiro rigakafin Coronavirus zai samu N36m - FG

- Gwamnatin tarayya ta yi alkawarin bawa duk wanda ya kirkiro rigakafin cutar Coronavirus kyautar N36m

- Gwamnatin ta ce ya zama dole kasar ta zama mai hangen nesa da kasancewa cikin shiri ko da za a samu bullar cutar

- Gwamnatin ta ce akwai tsirai da dama a cikin daji a kasar kuma akwai yiwuwar a samu maganin cutar daga cikinsu

Gwamnatin tarayyar Najeriya ta yi alkawarin bawa duk wani kwararren mai binciken kimiyya dan Najeriya da ya kirkiro rigakafin cutar Coronavirus zunzurutun kudi Naira miliyan 36.

Ministan Kimiyya da Fasaha ta kasar, Dakta Ogbonnaya Onu ne ya yi wannan alkawarin a ranar Alhamis a Abuja a wurin bikin yaye daya daga cikin direktocin ma'aikatar, Injiniya A. Oyefeso da ya yi ritaya daga aikin gwamnati.

Duk wanda ya gano rigakafin Coronavirus zai samu N36m - FG
Duk wanda ya gano rigakafin Coronavirus zai samu N36m - FG
Asali: Depositphotos

DUBA WANNAN: PDP ta yi martani kan ihun da 'yan Maiduguri suka yi wa Buhari

Onu ya ce akwai bukatar Najeriya ta fara tunani mai zurfi da hangen nesa domin ta kare mutanen kasar daga kamuwa da cutar da Corona.

Ya ce gwamnati za ta rika bawa masu binciken kimiyya a kasar tallafi domin a taimaka musu su rika kirkirar magunguna domin magance cututtukan da ke adabar mutanen kasar.

Ya ce, "Mun yi alkawarin za mu bawa duk wani mai binciken kimiyya dan Najeriya da ya kirkiro rigakafin cutar Coronavirus kudi Naira miliyan 36.

"Mu na da tsirai da yawa a kasar nan, wane ya sani ko za a iya samun maganin cutar da dajin da muke da su.

"Mu na kallubalantar kwararrun masu binciken kimiyya na kasar nan da su kirkiro da maganin cutar kuma kasarsu za ta karrama su kamar yadda ya dace."

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel