An Harbe Tsohon Shugaban Majalisar Tarayya har Lahira, Shugaban Ƙasa Ya Girgiza a Ukraine
- An harbe tsohon kakakin majalisar tarayyar Ukraine, Andriy Parubiy, har lahira a Lviv, lamarin da ya jefa ƙasar a jimami
- Gwamnati ta yi alƙawarin gudanar da bincike, yayin da Shugaba Volodymyr Zelenskiy ya aike da sako ga iyalan marigayin
- An ce Parubiy, wanda ya jagoranci zanga-zangar Euromaidan, ya kasance ginshiki wajen kare ‘yancin kai a ƙasar Ukraine
Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida
Ukraine - An shiga cikin alhini a Ukraine a ranar Asabar bayan kisan gilla da aka yi wa Andriy Parubiy, tsohon kakakin majalisar tarayya na kasar, wanda aka harbe a birnin Lviv.
Ofishin Babban Lauyan Ƙasa ya tabbatar da cewa wani ɗan bindiga ne ya bude masa wuta da ƙarfe 12:00 na rana, inda ya kashe shi a wurin sannan ya tsere.

Source: Getty Images
An kashe tsohon shugaban majalisar tarayya
Shugaba Volodymyr Zelenskiy ya tabbatar da aukuwar lamarin a shafinsa na X, inda ya taya iyalan marigayin jaje, yana mai cewa:
“Ministan Harkokin Cikin Gida na Ukraine, Ihor Klymenko, da Babban Mai Shigar da Kara, Ruslan Kravchenko, sun bayar da rahoton farko kan mummunan kisan da aka yi a Lviv. An kashe Andriy Parubiy. Ina mika ta’aziyyata ga iyalansa da masoyansa.
“An tura dukkan kayan aiki da jami’an tsaro domin gudanar da bincike tare da kamo wanda ya aikata wannan ta’asa.”
Parubiy, mai shekara 54, ya rike mukamin Kakakin Majalisar Tarayya daga 2016 zuwa 2019, sannan kuma ya kasance Sakataren Majalisar Tsaron Ƙasa a 2014.
Babu tabbacin alaka da yakin Rasha
Ya rike wannan babban mukami ne a lokacin da Rasha ta mamaye yankin Crimea tare da barkewar yaki a gabashin Ukraine, inji rahoton Reuters.
Haka kuma, yana ɗaya daga cikin shugabannin zanga-zangar Euromaidan ta shekarar 2013–2014 wacce ta kifar da gwamnatin da ke goyon bayan Rasha, ta kuma karfafa alakar Ukraine da Tarayyar Turai.
Hukumomi ba su tabbatar ko kisan yana da alaka da yakin Rasha a Ukraine ba, amma gwamnan Lviv, Andriy Sadovyi, ya ce gano wanda ya aikata laifin da kuma dalilinsa shi ne babban abin da ya kamata a mayar da hankali a kai.
Ya ce:
“Wannan lamari ne na tsaro a ƙasar da ke cikin yaƙi, inda babu wani wuri da ya zama mai tsaro ga ƴan kasa.”

Source: Getty Images
Ana ta'aziyyar tsohon shugaban majalisa
Tsohon shugaban ƙasa Petro Poroshenko ya bayyana mutuwar Parubiy a matsayin “babban rashi ga Ukraine,” inda ya ce marigayin jagora ne mai hangen nesa da kishin ƙasa.
Ministan Harkokin Waje, Andrii Sybiha, ya ce:
“Patriot ne da kuma ɗan siyasa wanda ya bayar da gagarumar gudunmawa wajen kare ‘yanci, ‘yancin kai da zaman lafiyar Ukraine. Tabbas sunansa zai kasance cikin littafin tarihin ƙasar.”
Sojojin Ukaraine sun cafke dan Najeriya
A wani labarin, mun ruwaito cewa, sojojin Ukraine sun cafke wani matashi ɗan Najeriya da ke yaƙi a bangaren sojojin Rasha a yankin Zaporizhzhia.
An bayyana cewa ya shiga rundunar Rasha ne domin rage masa hukuncin gidan yari bayan an kama shi da laifin miyagun ƙwayoyi.
Rahotanni da suka fito sun sun ce Rasha ta ɗauki dubban 'yan ƙasashen waje domin tura su zuwa fagen yaƙi a Ukraine.
Asali: Legit.ng

