Ministoci, Tsohon Ɗan Majalisa da Mutum 5 Sun Mutu a Mummunan Hatsarin Jirgin Sama a Ghana

Ministoci, Tsohon Ɗan Majalisa da Mutum 5 Sun Mutu a Mummunan Hatsarin Jirgin Sama a Ghana

  • An samu mummunan hatsarin jirgin sama a yankin Ashanti da ke kasar Ghana mai makwabtaka da Najeriya a yau Laraba 6 ga watan Agustan 2025
  • Ministan tsaro da na muhalli a ƙasar Ghana sun mutu tare da wasu mutum shida a hatsarin wanda ya daga hankulan jama'a
  • Sojojin Ghana sun ce jirgin Z9 na daga Accra zuwa Obuasi ya bace daga sama, inda yake dauke da mutane takwas ciki har da mukarraban gwamnati

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.

Accra, Ghana - Wani mummunan hatsarin jirgin sama ya faru a kasar Ghana inda aka rasa rayuka da dama ciki har da mukarraban gwamnati.

Majiyoyi sun ce jami'ai biyu na gwamnatin Ghana sun rasu bayan hatsarin ya afku a yankin Ashanti da ke Kudancin kasar.

Ministocin Ghana 2 sun mutu a hatsarin jirgin sama
Mutane 8 sun mutu a hatsarin jirgin sama a Ghana ciki har da ministoci. Hoto: John Dramani Mahama.
Source: Twitter

An rasa rayukan ministocin Ghana a hatsari

Kara karanta wannan

Mutuwar Ministoci 2 lokaci guda ta girgiza Shugaba Tinubu, ya yi masu addu'a

Rahoton CNN Africa ya ce Ministan Tsaro, Edward Omane Boamah da Ministan Muhalli Ibrahim Murtala Mohammed na daga cikin wadanda suka mutu.

Har ila yau, wasu mutane shida sun rasa rayukansu a hatsarin jirgin sama a yankin Ashanti da ke Kudancin kasar.

Lamarin ya faru ne a ranar Laraba 6 ga watan Agustan 2025 kamar yadda shugaban ma’aikatan gwamnatin kasar Ghana ya tabbatar.

Rundunar sojojin kasar Ghana ta ce tun da farko a ranar Laraba jirgin ta bace da ke hanyarsa daga babban birnin Accra zuwa Obuasi, wani gari da ake hakar ma’adinai a Kudancin Ghana.

An rasa rayukan wasu ministoci a Ghana
Ministoci 2 sun rasa rayukansu a hatsarin jirgin sama a Ghana. Hoto: John Dramani Mahama.
Source: Facebook

Hatsarin jirgi: Gwamnatin Ghana ta fitar da sanarwa

Rahoton ya ce jirgin saman da ya yi hatsarin na dauke da fasinjoji biyar da ma’aikatan jirgin uku wanda ya ta da hankulan jama'a a Ghana.

Shugaban ma’aikata, Julius Debrah ya bayyana a cikin wani faifan bidiyo cewa za a dinga daga tutar kasar rabin sanda har sai an bayar da wata sanarwa.

Rahoton GhanaTV3 ya tabbatar da cewa shugaban kasar, John Dramani Mahama ya ba da umarnin saukar da tuta rabin sanda domin karrama wadanda suka rasu.

Kara karanta wannan

Fasinjojin Kano 22 sun mutu a hanyar Neja, tirela dauke da mutum 42 ta yi hatsari

Mahama ya shiga damuwa kan rashin ministoci

Mahama ya nuna jimaminsa kan rashin da aka yi inda ya tura sakon ta'aziyya ga iyalan wadanda hatsarin ya rutsa da su.

Rahoton ya ce:

"Shugaba John Dramani Mahama ya bayar da umarnin a sauke dukkan tutocin ƙasar rabin sanda domin girmama waɗanda suka mutu a hatsarin jirgin sama na sojoji."

Ghana: An yi zanga-zangar korar yan Najeriya

Mun ba ku labarin cewa wasu yan kasar Ghana sun gudanar da zanga-zanga, suna zargin wasu 'yan Najeriya da tsafi da kuma lalata da 'yan mata wanda ya yi yawa.

Masu zanga-zangar sun dauki wasu alluna, suna cewa yan Najeriya na jawo sace yara, barna a kasuwanni da kuma cin zarafin 'yan kasar wanda suka ce ba zai yiwu ba.

Wata mata da ta yi magana a bidiyon ta ce 'ba za ku zo ƙasarmu ku rika aikata komai ba', 'Yan Najeriya dole su tafi domin suna neman mamaye ko ina a kasar.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 5 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.