Jirgin Ƙasa Dauke da Fasinjoji 100 Ya Yi Hatsari Yana cikin Gudu, An Rasa Rayuka
- Jirgin kasa ya yi hatsari a Kudancin Jamus inda mutane uku suka mutu, wasu da dama suka jikkata a ranar Lahadi, 27 ga Yulin 2025
- Ana zargin jirgin dauke da fasinjoji 100 ya sauka daga hanyarsa ne sakamakon zabtarewar kasa da aka samu saboda ambaliyar ruwa
- Firayim Minista, Friedrich Merz da kamfanin jirgin sun jajantawa wadanda abin ya shafa, yayin da hukumomi ke kokarin ceto karin mutane
Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida
Jamus - Mutane uku sun mutu yayin da wasu da dama suka jikkata sakamakon hatsarin jirgin kasa da ya kauce hanya a Kudu maso Yammacin Jamus, a ranar Lahadi.
‘Yan sandan tarayya da na jiha sun bayyana cewa ana ci gaba da bincike don gano musabbabin hatsarin da ya faru a kusa da garin Riedlingen, kimanin kilomita 158 daga yammacin Munich.

Kara karanta wannan
Yan bindiga sun saɓa alƙawari, sun yanka mutum 38 bayan dafe miliyoyin kuɗin fansa

Source: Getty Images
Jirgin kasa ya yi hatsari a Kudancin Jamus
Hotunan da aka dauka daga wurin sun nuna yadda sassan jirgin suka karkata gefe, inda masu ceto ke haurowa saman taragon jirgin suna zakulo fasinjoji, inji rahoton Reuters.
Wani bangare na jirgin da ke dauke da kimanin mutane 100 ya kauce wa hanya ne tsakanin garuruwan Riedlingen da Munderkingen, a kusa da iyakar Jamus da Faransa da kuma Switzerland, a cewar ‘yan sanda na birnin Stuttgart.
An ce an samu guguwa da ruwan sama mai karfi a yankin kafin faruwar hatsarin, kuma ana tunanin hakan na da nasaba da hatsarin jirgin.
Ana zargin ambaliya ta jawo hatsarin
Ministan harkokin cikin gida na jihar Baden-Württemberg, Thomas Strobl, ya ce:
"An sami ruwan sama mai tsanani a yankin, don haka ba za a iya yanke tsammanin cewa hakan ne ya jawo karkacewar jirgin ta hanyar zabtarewar kasa ba. Amma dai ana ci gaba da gudanar da bincike a kai."

Kara karanta wannan
Gwamnonin 1999 sun nemi Tinubu ya ajiye raba tallafi, ya samar da ayyuka ga matasa
‘Yan sandan Ulm da lauyoyin gwamnati na Ravensburg sun bayyana cewa:
“An yi imani da cewa ruwan sama mai yawa ne ya jawo wata magudanar ruwa ta yi ambaliya, wanda hakan ya haddasa zabtarewar kasa a bakin layin dogon, wanda ya jawo hatsarin.”
Firayim Ministan Jamus ya magantu
Firayim Ministan kasar Jamus, Friedrich Merz, ya bayyana alhininsa a shafinsa na X, inda ya ce yana makokin wadanda suka rasa rayukansu tare da jajanta wa iyalansu.
Ya rubuta cewa:
“Hatsarin jirgin a gundumar Biberach ya girgiza ni. Ina samun rahoto kai tsaye daga ministan harkokin cikin gida da ministan sufuri, kuma na ba da umarnin su tallafa wa jami’an ceto da duk wani abu da ake bukata.
"Muna makokin wadanda suka rasu. Ina mika ta’aziyya ga ‘yan uwansu.”

Source: Getty Images
An kwashe dukkan fasinjoji daga jirgin
Kamfanin jiragen kasa na Jamus, Deutsche Bahn, ya ce yana aiki tare da masu bincike, kuma ya mika ta’aziyyarsa ga iyalan mamatan.
Sanarwarsu ta ce:
"Zuciyarmu na tare da wadanda suka jikkata da iyalan wadanda suka rasu. Muna godiya ga jami’an ceto bisa daukin gaggawar da suka kai."
Ministan cikin gida, Thomas Strobl, wanda ke wurin da hatsarin ya faru, ya kara shaidawa manema labarai cewa an kwashe dukkanin fasinjojin da ke cikin taragon jirgin.
Sai dai ya ce dole ne a daga taragon jirgin domin tabbatar da babu wanda ya makale a kasa, a cewar rahoton AP News.
“Yanzu haka, muna da mutane uku da suka mutu, sannan wasu da dama sun jikkata, ciki har da wadanda suka samu mummunan rauni.
"An kwashe dukkanin fasinjoji daga jirgin, sai dai yanzu ana bukatar daga taragon domin tabbatar da babu wanda ke karkashinsu.”
- Thomas Strobl.
Jirgin ruwa ya yi hatsari a jihar Neja
A wani labarin, mun ruwaito cewa, an samu mummunan hatsarin jirgin ruwa a karamar hukumar Shiroro da ke jihar Neja, a ranar Asabar, 25 ga Yulin 2025.
Ana fargabar cewa fasinjoji da dama sun rasa rayukansu a hatsarin, ciki har da mutane goma 'yan gida guda bayan jirgin ya kife a tsakiyar teku.
Hatsarin ya tayar da hankali a yankin, yayin da ake ci gaba da kokarin ceto wadanda ke da rai ko gano gawarwarkin wadanda hatsarin ya rutsa da su.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng
