Jirgin Kasa Ya Yi Hadari a Abuja, Ya Latse Jariran Tagwaye Sun Mutu

Jirgin Kasa Ya Yi Hadari a Abuja, Ya Latse Jariran Tagwaye Sun Mutu

  • A ranar Asabar da ta wuce aka samu hatsarin jirgin kasa a yankin Kuchiko dake Bwari a birnin tarayya Abuja
  • Hatsarin ya lakume rayukan yara mata, Hassana da Hussaina, da suke ƙoƙarin cika shekaru biyu da haihuwa
  • Shaidar gani da ido, Andrew Dogonyaro ya bayyanawa jami'an tsaro da manema labarai yadda hatsarin ya faru

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

A ranar Asabar da ta wuce aka wayi gari da hatsarin jirgin kasa a yankin Kuchiko dake Bwari a birnin tarayya Abuja.

Jirgin kasa
Yara mata 2 sun mutu bayan hatsarin jirgin kasa a Abuja. Hoto: Kaduna Political Affairs
Asali: Facebook

Jirgin kasa ya kashe tagwaye a Abuja

Jaridar Daily Trust ta ruwaito cewa jirgin kasan ya murkushe wasu mata yan biyu har lahira yayin da hatsarin ya auku.

Kara karanta wannan

Jerin alkawuran da Shugaba Bola Tinubu ya gagara cikawa cikin shakara 1

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Rahotanni sun tabbatar da cewa yaran za su cika shekaru biyu da haihuwa ne a watan Yunin nan mai zuwa.

Yadda hatsarin jirgin kasan ya faru

Wani shaidar gani da ido, Andrew Dogonyaro ya bayyanawa jami'an tsaron birnin tarayya cewa lamarin ya faru ne da misalin karfe 10:00 na safe.

Andrew Dogonyaro ya kara da cewa dama yaran sun saba fita zuwa makwabta da kan su a wasu lokutan.

A cewarsa, ranar da hatsarin ya faru, jirgin kasan ya kunna kararrawa da ya ga yara sun nufo shi, wani mutumi ma a gefe ya yi yunkurin ceto yaran amma ƙaddara ta riga fata.

Bayan hatsarin ya faru, Andrew ya tabbatar da cewa sun sanar da jami'an tsaro a Sabon Bwari da Sabon Wuse, da ke yankin jihar Neja.

Yan sanda sun tabbatar da hatsarin jirgin

Kara karanta wannan

Rikicin Kano: Abin da Sarki Sanusi II ya faɗawa manyan jami'an tsaro a fadarsa

Kakakin yan sanda a jihar Neja, Wasiu Abiodun ya tabbatar da faruwar lamarin inda ya ce sun samu labarin hatsarin jirgin kasan da ya kashe yara Hassana da Hussaina.

Ya ce a halin yanzu za su mika rahoton hatsarin ga jami'an tashar jirgin kasa da ke Kubwa a birnin tarayya Abuja.

Yan sanda sun kama kasurgumin dan ta'adda

A wani rahoton, kun ji cewa rundunar 'yan sanda ta samu nasarar kama Ibrahim Abdullahi (Mandi) wanda ake zargin ya jagoranci kai harin jirgin kasan Abuja-Kaduna.

Yan sanda sun kama Mandi tare da kwato bindiga kirar AK-47 guda 48 a wajensa a hanyar shiga Kaduna daga Abuja ta sha-tale-talen Rido.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng

Online view pixel