Wani kamfanin a Amurka zai taimaka wurin inganta harkar sufurin jirgin kasa a Najeriya

Wani kamfanin a Amurka zai taimaka wurin inganta harkar sufurin jirgin kasa a Najeriya

- Shahararren kamfanin nan na kasar Amurka wato General Electronics ya rattaba hannu akan wata yarjejeniya ta zuba jari domin inganta harkar sufurin jirgin kasa a Najeriya tare da hadin guiwar gwamnatin Najeriya

Wani kamfanin a Amurka zai taimaka wurin inganta harkar sufurin jirgin kasa a Najeriya
Wani kamfanin a Amurka zai taimaka wurin inganta harkar sufurin jirgin kasa a Najeriya

Shahararren kamfanin nan na kasar Amurka wato General Electronics ya rattaba hannu akan wata yarjejeniya ta zuba jari domin inganta harkar sufurin jirgin kasa a Najeriya tare da hadin guiwar gwamnatin Najeriya.

DUBA WANNAN: Wata kungiya ta bukaci da a tsige gwamna Ganduje

An gabatar da bikin rattaba hannu kan yarjejeniyar ne a birnin Washington, taron daya samu harlatar wakilan kamfanin na General Electronics da kuma Ministan Sufuri na Najeriya Rotimi Amaechi. A watan Mayun bara ne kamfanin na General Electronics ya samu nasarar samun kwangilar aikin gina hanyoyin jiragen kasa, da kuma kwangilar samar da sababbin jirage na zamani wanda zasu yi aiki a fadin kasar.

An kulla yarjejeniyar ne akan samar da sababbin kawunan jirage guda 10 da tarago guda 200 wadanda zasu taimakawa wadanda ake amfani dasu a yanzu haka. Hakazalika akwai yiwuwar bayan an kammala aikin jiragen da hanyoyin , safarar dakon kaya da ake yi masu nauyin ton 50,000 zai karu zuwa 500,000.

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng