Shugaban Kasar Amurka Donald Trump Ya Kamu da Cutar CVI, Kafarsa Ta Fara Kumbura

Shugaban Kasar Amurka Donald Trump Ya Kamu da Cutar CVI, Kafarsa Ta Fara Kumbura

  • Gwaje gwajen likitoci ya gano cewa Shugaban kasar Amurka Donald Trump na fama da ciwon "chronic venous insufficiency"
  • Fadar White House ta bayyana cewa likitoci sun gudanar da gwaje-gwaje kan Trump bayan ƙafafu da hannayensa sun fara kumbura
  • Duk da haka, likitan Trump ya ce babu wata barazana kamar ciwon jijiyoyi mai tsanani ko gazawar zuciya, ko kuma ciwon koda

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Amurka - An gano Shugaban Amurka Donald Trump yana dauke da ciwon "Chronic Venous Insufficiency" bayan an yi gwaje-gwaje kan kumburin ƙafafu da hannayensa.

A ranar Alhamis, kakakin Fadar White House, Karoline Leavitt, ta kira cutar CVI da "gama gari" inda jijiyoyin jini da suka lalace ke hana jini gudana yadda ya kamata.

Bayan gwaje-gwaje, an tabbatar da cewa Shugaban Amurka Donald Trump ya gamu da cutar CVI.
Shugaban kasar Amurka, Donald Trump mai shekaru 79 ya kamu da cutar CVI. Hoto: Getty Images
Source: Getty Images

Bincike game da lafiyar Donald Trump

Kara karanta wannan

London Clinic: Abubuwan mamaki game da asibitin da Muhammadu Buhari ya rasu

Da take karanta wata wasiƙa daga Kyaftin Sean Barbabella, likitan Trump, Leavitt ta ce cutar CVI tana da yawa "a tsakanin mutanen da suka haura shekaru 70" inji rahoton CNN.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Hukumar lafiya ta Fadar White House ta gudanar da "cikakken bincike, ciki har da nazarin jijiyoyin jinin kafarsa da hannu," ga Trump, mai shekaru 79.

Wasikar Kyaftin Barbabella, wacce Fadar White House ta fitar daga baya, ta bayyana cewa:

"An yi amfani da na'urar duban jijiyoyin jini (Doppler ultrasounds) a dukkan ƙafafunsa kuma sun nuna cewa akwai cutar 'chronic venous insufficiency'."

Binciken ya zo ne bayan da Shugaba Trump ya lura "ƙafafunsa ta wajen idon sahu sun fara kumbura" a cikin makonnin baya-bayan nan, in ji Leavitt.

"Abu mai muhimmanci shi ne, babu wata shaida ta cutar DVT, kuma cutar jijiyoyin jinin ba ta yi muni ba. Gwajin da aka yi ya nuna komai yana tafiya dai dai wadaida a jikinsa."

An yiwa Shugaba Trump gwajin zuciya

Jaridar Aljazeera ta rahoto Fadar White House ta ce an yiwa Trump gwajin zuciya kuma likitansa Barbabella ya rubuta cewa"

Kara karanta wannan

Bidiyo: Yadda aka fito da gawar Buhari daga jirgi da manyan mutanen da aka gani

"Ba a gano alamun gazawar zuciya, lalacewar koda, ko cutar dukkanin sassan jiki ba."

Kakakin ta kuma amsa tambayoyi game da raunukan da ke hannun Trump, waɗanda suka haifar da hasashe game da lafiyarsa.

Leavitt ta ce:

"Raunukan ƙaramin ciwo ne daga yawan musabaha da kuma amfani da aspirin, wanda ake sha a matsayin wani ɓangare na tsarin rigakafin cututtukan zuciya."

Trump mai shekaru 79 shi ne mutum mafi tsufa a tarihin Amurka da ya riƙe shugabancin ƙasa kuma ya rika amfani da shekarun tsohon Shugaba Joe Biden a matsayin wani abin caccaka a zaɓen 2024.

Fadar White House ta ce cutar CVI da ta kama Donald Trump tana kama mafi yawan wadanda suka haura shekaru 70
Shugaban kasar Amurka, Donald Trump yana gudanar da aikace-aikace a Fadar White House. Hoto: Getty Images
Source: Facebook

Menene 'Chronic Venous Insufficiency'?

Cutar chronic venous insufficiency na faruwa ne idan jijiyoyin jini ba sa aiki yadda ya kamata, wanda hakan zai iya sa jini ya taru ko ya daskare a cikin jijiyoyin.

Kusan mutane 150,000 ke kamuwa da cutar a kowace shekara a Amurka, kuma haɗarinta na ƙaruwa da shekaru. Ana magance ta da magunguna ko tiyata idan ta tsananta.

Alamominta sun haɗa da kumburi a ƙafa ko gwiwa, ciwo ko kumburin jijiyoyi, jin nauyi ko sauyin fata.

Kara karanta wannan

An yi wa Buhari sallar jana'iza a Gombe yayin da ake jiran gawar shi a Daura

Ko da yake ba dole ba ne a shari’a, amma ya zama ruwan dare a Amurka shugabannin ƙasa na bayyana lafiyarsu kowace shekara.

Ambaliyar ruwa ta kashe mutane 120 a Amurka

A wani labarin, mun ruwaito cewa, Donald Trump, ya kai ziyara jihar Texas domin duba mummunar ambaliya da ta hallaka mutane 120 tare da ɓacewar wasu 160.

Trump zai gana da iyalan waɗanda abin ya shafa da kuma jami’an ceto a Kudancin Texas, inda kogin Guadalupe ya yi ambaliya tare da haddasa mummunan lahani.

Rahotanni sun bayyana cewa ambaliyar ta kashe yara 36 a sansanin Camp Mystic, wanda ke zama mafi girman iftila'i tun bayan da Trump ya hau karagar mulkin Amurka.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza (Hausa Editor) Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i. Imel: sanihamzafuntua@gmail.com