Ta Faru Ta Ƙare: An Gano Abu 1 da Ya Jawo Mutuwar Mutane Sama da 250 a Hatsari

Ta Faru Ta Ƙare: An Gano Abu 1 da Ya Jawo Mutuwar Mutane Sama da 250 a Hatsari

  • Hukumomin Indiya sun fitar da rahoton binciken farko kan hatsarin jirgin Air India da ya faru a watan da ya gabata
  • Rahoton ya nuna cewa kashe hanyar da ke kai mai zuwa injunan jirgin ne ya jawo hatsarin, wanda ya yi ajalin mutane 260
  • Jirgin saman ya tashi daga filin jirgin Ahmedabad da nufin zuwa birnin Landan, amma ya faɗo a wata kwaleji da ke kusa da wurin

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

India - An gano cewa danna madannin katse tafiyar mai zuwa injunan jirgin ne ya haddasa haɗarin jirgin saman Air India da ya faru a watan da ya gabata.

Hakan na kunshe ne a rahoton binciken farko da hukumomin India suka fitar kan hatsarin jirgin saman wanda ya yi sanadin mutuwar mutane 260.

Jirgin saman Air India.
Katse hanyar tura mai zuw injuna ne ya haddasa hatsarin jirgin Air India Hoto: Getty Images
Source: UGC

Tribune Online ta tattaro cewa jirgin da ke kan hanyarsa ta zuwa London ya fado kasa jim kaɗan bayan ya tashi daga filin jirgin sama na Ahmedabad.

Kara karanta wannan

Mummunan iftila'i ya sauka kasar Amuka, mutane 120 sun mutu, an nemi 160 an rasa

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Duka fasinjoji da ma’aikatan jirgin sun mutu, sai mutum guda kacal da ya tsira, cewar rahoton Aljazeera.

Abin da ya jawo hatsarin jirgin Air India

Rahoton Hukumar Binciken Hadurran Jiragen Sama ta Indiya ya nuna cewa ana zargin an danna madannan sarrafa mai na jirgin Boeing 787 Dreamliner, wanda hakan ya hana injunan jirgin samun isasshen mai.

Masu bincike sun sami damar ciro bayanai daga akwatunan rikodin na jirgin, wanda ya ƙunshi bayanai da sautunan murya da aka dauka har da lokacin da hatsarin ya faru.

An bayyana cewa jirgin ya kai gudun 180 knots (kimanin kilomita 333 a awa ɗaya) lokacin da aka sauya madannan mai daga RUN zuwa CUTOFF a jere da tazara na daƙiƙa ɗaya.

"A cikin sautin na'urar kokpit ɗin, an ji ɗaya daga cikin matukan jirgin yana tambayar ɗan uwansa dalilin da yasa ya danna madannan. Sai ɗayan ya ce ba shi ya danna ba,” in ji rahoton.

Kara karanta wannan

Sojoji sun yi ruwan wuta kan 'yan ta'adda da ke hijira a tsakanin Kebbi da Zamfara

Yadda matuƙan jirgin suka koƙarta

Bayan ‘yan daƙiƙu, an dawo da maɓallan madannan zuwa matsayin da ya dace, kuma injunan sun fara ƙoƙarin sake kunna kansu lokacin da jirgin ya fado ƙasa.

A jirgin mai lamba 787, madaɓɓan katse iskar mai suna a tsakanin kujerun matuka biyu. An killace su da sandar ƙarfe da mabuɗai domin hana kuskuren amfani da su.

Madannan datse tafiyar mai zuwa injin jirgin sama.
Hukumomin India sun sako rahoton farko kan hatsarin jirgin Air India Hoto: @tparon
Source: Twitter

Rahoton ya kara da cewa:

“Idan aka dawo da madannan mai daga CUTOFF zuwa RUN a lokacin da jirgi ke cikin tafiya, kowanne inji yana komawa sarrafa kansa don sake kunnuwa da dawo da ƙarfin gudu.
"A lokacin da injunan suka fara ƙoƙarin sake kunna kansu, ɗaya daga cikin matuka jirgin ya yi saurin neman agajin gaggawa. Mai sarrafa jiragen sama ya nemi lambar kiran jirgin, amma bai samu amsa ba, daga na aka hangi jirgin ya kife."

Kyaftin din jirgin yana da shekaru 56 kuma ya tuƙa jirgi sama na sa’o’i 15,000 a tarihin aikknsa yayin da matukin jirgin na biyu kuma yana da shekaru 32 da fiye da sa’o’i 3,400 na tuƙi.

Kara karanta wannan

Babbar magana: 'Yan acaba za su yi fito na fito da 'yan sanda, hukuma ta yi gargadi

Jirgin helokwafta ya yi hatsari a India

A wani labarin, kun ji cewa wani jirgin sama mai saukar ungulu ya fado a wani yankin tsaunuka na jihar Uttarakhand da ke arewacin kasar India.

Wannan mumminan hatsarin dai ya yi sanadin mutuwar duka mutane bakwai da ke cikin jirgin, ciki har da wata yarinya ‘yar shekara biyu.

Rahotanni sun bayyana cewa jirgin ya tashi ne da misalin karfe 5:20 na safe agogon kasar India, sannan ya rikto ƙasa bayan ya yi tafiyar mintuna 10 kacal.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262