Mummunan Iftila'i Ya Sauka Kasar Amuka, Mutane 120 Sun Mutu, an Nemi 160 an Rasa

Mummunan Iftila'i Ya Sauka Kasar Amuka, Mutane 120 Sun Mutu, an Nemi 160 an Rasa

  • Shugaba Donald Trump ya ziyarci Texas domin duba ambaliyar da ta yi sanadin mutuwar mutane 120 tare da bacewar wasu 160
  • Trump zai gana da iyalan mamata da jami’an ceto a yankin Kudancin Texas, inda kogin Guadalupe ya balle, ya haifar da barna mai yawa
  • Rahoto ya nuna cewa ambaliyar ta kashe yara 36 da ke sansanin Camp Mystic, mafi munin iftila'i tun bayan da Trump ya hau mulki

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Amurka - Shugaban ƙasar Amurka, Donald Trump, ya tashi da safiyar Juma’a zuwa Texas domin duba barnar da ambaliya ta yi a ranar 4 ga watan Yuli.

An ce wannan mummunar ambaliyar ruwan ta yi sanadin mutuwar akalla mutane 120, yayin da ake neman sama da mutane 160.

Trump ya shilla Texas domin duba barnar da ambaliya ta yi bayan mutuwar akalla mutum 120
Ambaliyar ruwa ta hallaka akalla mutane 120 yayin da 160 suka bace a Amurka. Hoto: Getty Images
Source: Getty Images

Trump ya tafi Texas bayan ambaliyar ruwa

Kara karanta wannan

Tashin hankali: Fulani makiyaya sun bankawa gidaje 100 wuta, mutum 1 ya mutu a Taraba

Ziyarar tasa na zuwa ne bayan mako guda da ake ta tambayoyi game da matakan gwamnati na shawo kan wannan bala’i, yayin da ake ci gaba da neman wadanda suka bace, inji rahoton Reuters.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Dubban jami’an ceto ne suka kwashe kwanaki suna bincike cikin laka da baraguzai a sassan yankin Hill Country na Texas, amma ba a gano ko mutum daya da ya tsira ba.

Ruwan sama mai ƙarfi ya sauko a daren Juma’ar da ta gabata, inda ruwa ya cika kogin Guadalupe da safiyar ranar bikin ‘yancin kan Amurka, wanda ya balle a birnin na Texas.

Wannan ne bala’in da ya fi muni cikin kusan watanni shida da Trump ya shafe a ofis a matsayin shugaban ƙasa.

Abubuwan da Trump zai yi a Texas

“Abin tausayi ne ƙwarai. Ba wanda zai iya tsammanin saukar ruwa mai yawa haka cikin ɗan ƙanƙanin lokaci,” in ji Trump ga ‘yan jarida yayin da yake barin Fadar White House.

Wata majiya daga Fadar White House ta bayyana cewa Trump zai gana da iyalan waɗanda suka rasa rayuka da kuma jami’an ceto a yankin Kudancin tsakiyar Texas da ambaliyar ta fi shafa.

Kara karanta wannan

Sojoji, 'yan sanda sun gwabza fada da 'yan bindiga a Katsina, an rasa rayuka 36

Hakanan, zai saurari bayani daga jami’an ƙasa da na jihar tare da zagaya wuraren da abin ya fi shafa a ƙaramar hukumar Kerr, inda ambaliyar ta yi wa barna.

Yadda dam ya fashe, ruwa ya afka cikin gari

An san wannan yanki da suna “garin ambaliya,” saboda yawan ambaliyar ruwa da ke faruwa a can, wanda ke haddasa asara mai yawa a tarihin Amurka.

A ranar 4 ga watan Yuli, fiye da kafa goma na ruwa ya sauko cikin kasa da sa’a guda, a cewar rahoton BBC.

Na’urorin awon ruwa sun nuna yadda ruwan dam din ya haura daga kafa 1 zuwa kafa 34 (mita 10.4) cikin ‘yan sa’o’i kaɗan, wanda ya sa ya balle tare da afkawa cikin gari.

Jami’an ƙaramar hukumar Kerr sun bayyana cewa fiye da mutane 160 har yanzu ba a san inda suke ba, ko da yake masana sun ce yawan waɗanda ake kiran bacewa bayan irin wannan bala’i yakan fi ainihin adadi.

Amurka ta gamu da mummunar ambaliya a Texas, mafi muni tun bayan hawan Trump mulki
An Shiga Tashin Hankali a Amurka, Mummunar Ambaliyar Ruwa Ta Hallaka Turawa 120. Hoto: Getty Images
Source: Getty Images

Mahukunta na fuskantar suka a Texas

Cikin waɗanda suka mutu, akwai akalla yara 36 – wadanda da dama daga cikinsu dalibai ne a Camp Mystic, wani sansanin addinin Kirista da ke bakin kogin, wanda aka kafa fiye da shekaru 100 da suka gabata.

Kara karanta wannan

Gwamna ya fitar da N7.7bn, zai siyo jiragen sama masu gano maɓoyar ƴan bindiga

Jami’an ƙasa da na jihar sun fuskanci suka saboda ambaliyar, musamman kan kin daukar matakai wajen gargadin jama’a game da hauhawar ruwa da ambaliya.

An rahoto cewa ƙaramar hukumar Kerr ta ƙi kafa tsarin gargadi na gaggawa, saboda ta gaza samun tallafin kuɗi daga jihar domin aiwatar da tsarin.

Ambaliya za ta yi barna a jihohin Najeriya 20

A gida Najeriya, mun ruwaito cewa, NiMet ta gargadi jihohi 20 game da yiwuwar ambaliyar ruwa a watan Yuli 2025, inda Sokoto ke cikin matsanancin haɗarin ambaliyar.

Hukumar ta lissafa Kaduna, Zamfara, Yobe, da sauran jihohi 16 a matsayin jihohin da za su iya fuskantar ambaliyar ruwa a cikin wannan wata.

NiMet ta ba da shawarwari kan tsaftace magudanan ruwa, guje wa tuki yayin da ake ruwa, da yin kaura daga wuraren da ambaliya za ta shafa.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza (Hausa Editor) Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i. Imel: sanihamzafuntua@gmail.com