A Karshe, Amurka Ta Kirkiro Allurar da ke Kare Mutane daga Kamuwa da Cutar HIV
- Hukumar FDA ta amince da lenacapavir (Yeztugo), matsayin allurar rigakafin kamuwa da cutar HIV, wadda za a rika yinta sau biyu a shekara
- Yayin da ake gwaje-gwaje, allurar ta nuna tasiri na 100% ga mata da 96% ga maza masu jima'i da maza, kuma yana ɗorewa a jiki fiye da PrEP
- UNAIDS ta yi kira ga kamfanin Gilead da ya rage farashin lenacapavir daga $28,218 zuwa tsakanin $25-$46 don ya zamo mai araha ga kowa
Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida
Amurka - A ranar 18 ga Yuni, hukumar kula da abinci da magunguna ta Amurka (FDA) ta amince da magani na farko da ke hana kamuwa da cutar HIV wanda ake bukatar shan sa sau biyu kacal a shekara.
Mutanen da ke cikin hadarin kamuwa da HIV za su iya karɓar allurar Lenacapavir, wadda ake sayarwa da sunan Yeztugo, sau ɗaya duk bayan watanni shida.

Source: Getty Images
An samu maganin hana kamuwa da HIV
A sanarwar da ta fitar a shafinta na intanet, majalisar lafiya ta duniya (WHO) ta bayyana wannan mataki a matsayin babban ci gaba wajen yaki da HIV, wanda zai iya canza akalar yaduwar cutar a duniya baki ɗaya.
Duk da cewa magungunan HIV na yau da kullum sun taimaka wa miliyoyin mutane wajen rage yawan kwayar cutar a jikin su zuwa matakin da ba za su iya yadata ba, buƙatar shan kwayoyi kullum na haifar da matsala wajen kiyaye shan su yadda ya kamata.
A bincike guda biyu da aka gudanar, masana daga kamfanin Gilead, wanda ya kirkiro Lenacapavir, sun tabbatar da cewa maganin ya kare mata daga kamuwa da HIV da kashi 100.
Idan aka kwatanta da magungunan rigakafin HIV na yau da kullum (PrEP), Lenacapavir ya kuma kare maza masu neman maza da kashi 96.
Sai dai ƙungiyoyi da hukumomin yaki da cutar AIDS na duniya sun nuna damuwa cewa fa’idar wannan magani na iya raguwa, duba da cewa Amurka ta yanke tallafin da ta ke bayarwa a wasu shirye-shiryen yaki da cutar HIV.
Lenacapavir: Daga magani zuwa rigakafi
FDA ta amince da Lenacapavir tun 2022 a matsayin magani ga masu HIV da cutar ta yi ki karbar wasu magunguna irinsu PrEP.
Yayin da aka ke cigaba da nazarin maganin, masana daga Gilead sun gano cewa yana da wasu manyan halaye guda biyu: yana ɗorewa a jikin mutum, kuma yana hana kwayar cutar HIV yaduwa.
“Muna ganin babban sakamako ne bayan allura ɗaya,” in ji Tomas Cihlar, mataimakin shugaban sashen Virology a Gilead.
Ya kara da cewa:
“Ya kare dabbobi daga kamuwa da HIV, nan ne muka fahimci cewa dole mu himmatu wajen amfani da wannan magani don rigakafi ga mutane.”

Source: Twitter
UNAIDS ta bukaci a rage farashin lenacapavir
A wata hira da New York Times, kamfanin Gilead Sciences ya bayyana cewa farashin lenacapavir zai kasance $28,218 (N43.7m) ga kowane mutum a shekara.
Amma a cikin wani rahoto da aka wallafa a mujallar The Lancet HIV a wannan mako, masana sun gano cewa nau’in lenacapavir na bayan fage, zai iya kai $35–$46 (N54,200-N71,200) kacal a shekara, kuma yana iya sauka har $25 (N38,700) idan akwai buƙata daga mutane miliyan biyar zuwa 10 a shekarar farko.
Winnie Byanyima, babbar daraktar hukumar UNAIDS kuma mataimakiyar babban sakataren Majalisar Ɗinkin Duniya, ta bayyana cewa:
“Idan wannan magani mai canza rayuwa ya ci gaba da kasancewa mai tsada, to ba zai canza komai ba. Ina kira ga Gilead da su yi abin da ya dace: su rage farashi, su ƙara yawan samar da shi, su kuma tabbatar da cewa duniya na da damar kawar da cutar AIDS.”
'Sai malamai sun tashi tsaye" - Malam Buhari
Malam Buhari Abba, malami kuma limamin masallaci a Katsina, ya shaida wa Legit Hausa cewa, wannan ci gaba ne aka samu a kimiyance, amma barazana ne ga tarbiya.
Malam Buhari Abba, ya ce duk wani magana da zai kawo waraka ga wata cuta, ana maraba da shi, amma dole ne a yi taka tsantsan da abin da ka iya haddasawa a cikin al'umma.
"Ni ina maraba da wannan maganin, saboda akwai mutane masu yawan gaske da ke mutuwa saboda wannan lalura. Sai dai, a hannu daya, ina cike da zulumi gaskiya.
"Fito da wannan magani zai kara yawaitar fasikanci, zina-zinace za su yawaita sosai, musamman saboda an san cewa ai yanzu akwai rigakafin cutar.
"Mutane da dama suna kame kansu daga zina saboda tsoron wannan cutar, to me kake tunanin zai faru idan aka ce masu akwai rigakafi? Ka ga ai sai yadda hali ya yi."
- Malam Buhari Abba.
Malam Buhari ya ce dole ne malamai su tashi tsaye wajen wa'azi da jan hankalin mutane kan illar zina ga imani da kuma munin sakamakonta a lahira.
Ya ce:
"Malamai su fara tashi tsaye tun yanzu. A rika wa'azi dare da rana, a fadawa mutane illa da masifar zina, hakan zai sa ko da rigakafin ya zo, ba lallai zinar ta yi tasiri ba."
Mutane miliyan 2 ke dauke da HIV a Najeriya
A wani labarin, mun ruwaito cewa, hukumar NACA ta nuna cewa jihar Rivers ce ke kan gaba wajen yawan masu dauke da HIV da jimillar mutane 208,767, sai jihohin Benue da Akwa Ibom.
Yawan masu dauke da kwayar cutar HIV a Najeriya ya haura miliyan biyu, wanda ke nuna bukatar karin wayar da kai, saukin gwaji da samun magani cikin gaggawa.
Abuja, Legas da Anambra na daga cikin wuraren da cutar ke yaduwa sosai, yayin da Jihar Kano ke da mutum 53,972 da ke dauke da cutar a halin yanzu.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng



