Masana Harkokokin Lafiya Sun Gano Wani Magani Da yake Rage Kamuwa Da Cutar 'Kanjamau

Masana Harkokokin Lafiya Sun Gano Wani Magani Da yake Rage Kamuwa Da Cutar 'Kanjamau

  • Duk da ci gaban da duniya tayi, har yanzu ba'a gano takamaimai maganin cutar 'kanjamau ba
  • Masana da masu bincike kan cututtuka masu yaduwa sun fito da hanyoyi masu yawa wanda zasu taimaka wajen yakar cutar ko kuma samu kariya daga daukarta
  • Nan ma, masana ne sukai wani bincike tare da gano yadda mai dauke da cutar ko wanda bai da ita zai iya kare kansa ko kuma ya rage tasirinta

Kungiyar bayar da magani da rigakafin kanjamau ta NHVMAS, tace zoben PrEP, wanda aka fi sani da zoben mahaifa, kan iya rage hatsarin kamuwa da cutar kanjamau ga mata indai sukai amfani da shi yadda ya kamata.

PrEp kwayan magani ne da ake amfani da shi a mahaifa dan kare yadda kwayoyin halittar cutar kan iya shiga ko cutar da wanda yai mu'amala da cutar ta hanyar tarayya ko kuma allura. Kamar yadda jaridar Vanguard ta rawito.

Kara karanta wannan

Yan Sanda Sun Kama Kasurgumin Dan Bindiga a Kaduna, Sun Kwato Bindigogin AK47 Guda 4

Babbar daraktar cibiyar NHVMAS, Florita Dureke ce tace hakan yayin da ake wa mata 'yan jarida bita a jihar Lagos.

Kanjamau
Masana Harkokokin Lafiya Sun Gano Wani Magani Da yake Rage Kamuwa Da Cutar 'Kanjamau Hoto: HIV.GOV
Asali: UGC

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Ta ce yanayin yaduwar cutar ya karu a tsakanin mata da kashi 1.4, ma'ana cutar na yaduwa sosai a tsakaninsu.

Dureke ta ce a wanda suke a tsakanin shekaru 15 zuwa 49 sun fi samun damar rayuwa da cutar ba tare da wata babbar illa ba, ba kaman maza da a kowanne shekaru tana iya yi musu barazana ba.

"Kundin Bayanan masu cutar ya nuna masu dauke da cutar mata ne da kaso 3.3, kuma yawancin shekarunsu ba su wuce 35-39, ba kaman maza ba ba da yawancinsu masu shekara 50 ne zuwa 54 wato 2.3 cikin kason mata"
"A bangaren mata masu kananun shekaru kuwa kason da suke da shi cikin masu dauke da cutar bai fi 1.3 ba, amma ba kamar maza masu kananun shekaru da suke da kaso 0.4 na cikin adadin ba.

Kara karanta wannan

Ku Zabe Ni Zaku Samu Tsayayyiyar Wutar Lantarki Ba Tangarda, Inji Tinubu

Dureke ta ci gaba da cewa in mata zasu ringa amfanin da wannan abun to za'a samu gaggarumin canji bisa ga yadda take yaduwa a tsakanin mata.

Wata kafar www.hiv.gov tace mutum zai iya amfani da PrEP idan sha'awarsa ta motsa mkuma bashi da kanjamau, kuma wadda zasuyi mu'amalar tana shi ko yana da shi.

Shin Wannan Maganin Yana Da Illa

PrEP yana da tasiri sosai kuma yana rage hatsarin kamuwa da cutar ko da ta yin mu'amalar auratayya ne da kashi 99 cikin dari.

Dureke tace kamar yadda ake amfani da maganunuwan kayyade iyali da suka cika kasuwa kuma ba'a ganin illarsu, haka wannan ma yake da wannan yanayin na rashin cutarwa, kawai dai shima yana da mataki mataki wato iya kudinka iya shagalinka.

Dureke tace wannan maganin da ake amfani da shi wanda wasu hadar kungiyoyi na IPM suka samar, kuma hukumar lafiya ta duniya ta amince musu ya shafe shekaru sama 18 ana amffani da shi kuma garariya garau yake ba wata matsala.

Za'a a iya sa PrEP kuma a cire shi ba tare da wata tangarda ba, kai ba ma tare da taimakon wani ko wata jami'ar lafiya ba inji Dureke. kuma baya takurawa yayin mu'amala.

Asali: Legit.ng

Authors:
AbdulRahman Rashida avatar

AbdulRahman Rashida

Online view pixel