Yakin Israila: Abin da Ya Sa Amurka ta ke Tsoron Iran a Duniya Inji Bulama Bukarti
- Fitaccen lauya, Bulama Bukarti ya ce Amurka na tsoron Iran ne saboda tasirinta da za ta iya yi wajen jawo wa tattalin arzikin Turai matsala
- Haka kuma Amurka na fargabar shigar da sojojinta Iran saboda sanin karfin soji da Iran take da shi, wanda ke nufin sai dai a yi ragas
- Barista Bulama Bukarti na wannan batu ne bayan Amurka ta shigar wa Isra'ila yakin da take yi da Iran ta haifar jefa mata bama-bamai
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.
Kasar Iran – Fitaccen lauya mai kare hakkin dan Adam, Bulama Bukarti, ya zargi Amurka da yin gaban kanta wajen kai hari kan Iran ba tare da bin ka'ida ko wata hujja ba.
Baristan ya bayyana cewa Amurka ta gaggauta kai harin ne saboda tsoron tasirin Iran bisa wasu dalilai na siyasa da tattalin arziki da take ganin za su iya yi mata illa.

Kara karanta wannan
Koriya ta Arewa za ta taimaki shirin makamin nukiliya a Iran bayan harin Isra'ila da Amurka

Source: Getty Images
A shirin Fashin Baki da ya wallafa a shafinsa na Facebook, Bulama Bukarti ya ce Amurka na tsoron yadda Iran ke da iko da zirin Hormuz.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Bukarti ya ce Hormuz wuri ne mai matukar muhimmanci wajen jigilar danyen man fetur zuwa kasashe daban-daban, musamman Turai.
Meyasa kasar Amurka ta ke tsoron Iran?
A shirin da su Bulama Bukarti suka yi wanda Abdullahi Giggs ya wallafa gutsuren a Facebook, lauyan ya ce tattalin arzikin kasashen Turai zai gamu da koma baya idan Iran ta rufe zirin Hormuz.

Source: Getty Images
A cewarsa:
"Kusan duka man da ke zuwa kasashen Turai sai ya bi ta wannan tsibiri. Kwata-kwata zirin bai wuce kilomita 30 ba, kuma Iran na iya toshe wannan wuri gaba ɗaya.”
“A baya ma, ta taba toshe shi ta hanyar saka bama-bamai a cikin ruwa — wanda duk wani jirgin da ya zo, zai tashi da shi zai tashi.”
Bulama Bukarti ya kara da cewa Iran na da damar sanya makamai da za su iya harbo kowanne jirgi da ke kokarin wucewa da mai ta zirin.
Yadda matakin Iran zai iya illata Turai
Fitaccen lauyan ya kara da cewa rufe zirin Hormuz zai iya lalata tattalin arzikin kasashen Turai ta hanyar hana shigar da mai da iskar gas — lamarin da zai haifar da dakushewar ci gaban su.
Ya ce:
“Idan aka toshe wannan hanya, har wutar lantarki da ake cewa ba a dauke wa a Turai da Amurka sai ta dauku. Saboda idan aka hana shigar da man fetur da gas, tattalin arzikinsu zai gamu da mummunar illa.”
Ya kara da cewa hakan zai shafi manyan kamfanonin Amurka da asibitocinsu, inda zai haifar da asarar biliyoyin, ko ma tiriliyoyin daloli a kullum.
Amurka za ta ji tsoron tunkarar sojojin Iran
Bukarti ya ce Turawa na cikin fargaba kada Iran ta fadada harin zuwa kasashen Larabawa da suke da kawance da su a Gabas ta Tsakiya.
Ya kara da cewa Amurka ma na da imanin cewa ba za ta iya samun nasara a yaki da Iran ba.

Kara karanta wannan
Gwamnan Binuwai ya dakatar da hadiminsa da ake zargi da tilasta wa mata lalata da shi
Lauyan ya ce Iran na da karfin soji da zai iya ragargaza sojojin Amurka da kawayenta idan suka kuskura suka shigo cikin kasar domin neman kifar da gwamnati.
Masanin shari'a da tsaron ya yi wannan magana ne ganin yadda sojojin kasashen yamma suka sha wahala lokacin da suka shiga kasashen yankin a 2003.
Koriya ta Arewa na goyon bayan Iran
A baya, mun wallafa cewa gwamnatin Koriya ta Arewa ta bayyana fushinta kan harin da Amurka ta kai wa cibiyoyin nukiliyar Iran, tana mai zarginta da karya doka.
Ta zargi Isra’ila da tayar da zaune tsaye a yankin Gabas ta Tsakiya da goyon bayan Amurka da sauran ƙasashen Turai da suka bar Yahudawan na cin karensu babu babbaka.
Iran da Koriya ta Arewa na da dangantaka mai karfi tun shekaru da dama da suka gabata, kuma akwai zargin cewa suna hada kai a fannonin soji, ciki har da kera makaman nukiliya.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng
