Ana tsakiyar Rikicin Iran da Isra'ila, Tinubu Zai Shilla zuwa Saint Lucia a Watan nan

Ana tsakiyar Rikicin Iran da Isra'ila, Tinubu Zai Shilla zuwa Saint Lucia a Watan nan

  • Shugaba Bola Tinubu zai kai ziyarar mako guda zuwa Saint Lucia daga 28 ga Yuni zuwa 4 ga Yuli, don aiki da hutu a lokaci guda
  • Firayim Ministan Saint Lucia ya bayyana cewa wannan ziyarar ta Tinubu ce irinta ta farko da shugaban Najeriya zai kai Caribbean
  • Ziyarar za ta haɗa da jawabi a majalisa da ganawa da shugabannin OECS, yayin da Saint Lucia ke son yaukaka alaka da Najeriya

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Saint Lucia - Shugaban Najeriya, Bola Ahmed Tinubu, zai kai ziyarar mako guda zuwa ƙasar tsibirin Caribbean, Saint Lucia, daga ranar 28 ga Yuni zuwa 4 ga Yuli, 2025.

An rahoto cewa Tinubu zai shafe kwanaki biyu yana ziyarar aiki, yayin da kuma zai shafe ragowar sauran kwanaki yana hutawa.

Shugaba Bola Tinubu zai kai ziyarar mako 1 zuwa kasar Saint Lucia
Tinubu na dagawa wadanda suka yi masa rakiya hannu yayin da zai hau jirgin sama. Hoto: @aonanuga1956
Source: Twitter

Bola Tinubu zai kai ziyarar mako 1 Saint Lucia

Kara karanta wannan

Ajiye Shettima: Fadar shugaban kasa ta ce Tinubu zai sanar da mataimaki a 2026

Firayim Ministan Saint Lucia, Philip J. Pierre, ne ya bayyana hakan yayin wani taron manema labarai kafin zaman majalisar ministocinsa, a cewar rahoton St. Lucia Times.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Philip J. Pierre ya ce wannan ziyarar ita ce irinta ta farko da wani shugaban Najeriya zai kai zuwa yankin Caribbean, domin ƙarfafa haɗin kai tsakanin Afrika da yankin.

A cewar jaridar, shugaban zai shafe kwanaki biyu, daga 30 ga Yuni zuwa 1 ga Yuli yana gudanar da ayyukan gwamnati, yayin da sauran kwanakin zai yi hutu a sirrance.

Tinubu zai gana da shugabannin Caribbean

Shugaban Saint Lucia ya bayyana wannan ziyarar a matsayin “ta musamman mai cike da tarihi,” wadda za ta zurfafa dangantakar al’adu da tarihi tsakanin Saint Lucia da Najeriya.

Ziyarar kwanaki biyun za ta haɗa da jawabin Tinubu a gaban haɗaɗɗiyar majalisar dokokin Saint Lucia wato majalisar wakilai da majalisar dattawa a zauren taro na William Jefferson Clinton Ballroom da ke Sandals Grande, Gros Islet.

Firayim Ministan ya ce ya aika wa dukkanin shugabannin ƙasashen da ke cikin kungiyar OECS (kungiyar kasashen Gabashin Caribbean) katin gayyata domin su halarci taron tattaunawa da Tinubu.

Kara karanta wannan

Peter Obi ya yabi Tinubu kan zuwa Benue, ya bukaci shugaban kasa ya ziyarci Neja

The Cable ta rahoto cewa kasashen da ke cikin OECS sun haɗa da: Antigua and Barbuda, Dominica, Grenada, Montserrat, Saint Kitts da Nevis, Saint Lucia, da Saint Vincent and Grenadines.

Shugaban kasar Saint Lucia, Philip J. Pierre ya ce yana fatan Najeriya za ta kulla alaka mai karfi da kasarsa
Shugaban kasar Saint Lucia, Philip J. Pierre yayin da yake jawabi kan kasafin 2023. Hoto: @PhilipJPierreLC
Source: Twitter

Saint Lucia na son karfafa alaka da Najeriya

Pierre ya kara da cewa:

“Ziyarar shugaban Najeriya wata dama ce ta musamman da za ta ƙarfafa alaƙa tsakanin nahiyar Afirka da Caribbean.
"A matsayarmu na ‘yan asalin Afirka, akwai zurfin dangantaka tsakanin al’ummarmu da Najeriya, musamman ta fuskar tarihi da al’adu.”

Ziyarar Tinubu na zuwa ne a daidai lokacin da Najeriya ke fama da ƙalubale iri-iri, ciki har da harin kisan kiyashi da aka kai a jihar Benue a ranar 14 ga Yuni, wanda ya yi sanadin mutuwar kusan mutane 200.

A jawabin sa, Pierre ya ce ya na fatan tattaunawa da Tinubu kan yadda za a kafa ingantacciyar haɗin gwiwa a fannonin ci gaban tattalin arziki, ilimi, gina ababen more rayuwa, da musayar diflomasiyya.

Za a kwaso 'yan Najeriya daga Iran da Isra'ila

A wani labarin, mun ruwaito cewa, Shugaba Bola Tinubu ya ba ma'aikatar harkokin waje umarnin kwaso 'yan Najeriya daga kasashen Iran da Isra'ila.

Kara karanta wannan

Zargi ya dawo kan Zulum: An taso gwamna a gaba bayan kai wa Ganduje hari

Tinubu ya ba da wannan umarnin ne yayin da rikici tsakanin Iran da Isra'ila ya tsananta, wanda ya yi sanadin mutuwar daruruwan mutane daga bangarorin biyu.

Gwamnatin tarayya ta yi kira ga Isra'ila da Iran da su tsagaita wuta, tare da jaddada goyon bayanta ga warware rikicin ta hanyar sulhu.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza (Hausa Editor) Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i. Imel: sanihamzafuntua@gmail.com