Iran Ta Yi Wa Isra'ila Ɓarna bayan Harin Makami Mai Linzami da Ta Harba Ƙasar
- Wani asibiti a Beersheba, Isra’ila ya gamu da hari yayin da Iran ta harba makamai masu linzami, lamarin da ya jikkata mutane da dama
- Ministan tsaron Isra’ila ya ce “ba za a bar Ayatullah Ali Khamenei ya ci gaba da rayuwa ba,” saboda hare-hare
- Sojojin Isra’ila sun kai farmaki kan sansanonin nukiliyar Iran da suka hada da Arak da Natanz, yayin da Iran ke fargabar hare-haren Amurka
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.
Tel Aviv, Israel - Harin da kasar Iran ta kai wa Isra'ila ya jawo mata asara yayin da ake ci gaba da rikici.
Wani asibiti a garin Beersheba na Isra’ila ya gamu da hari yayin da kasar Iran ta harba makamai masu linzami.

Source: Getty Images
An samu raunuka da Iran ta farmaki Isra'ila
Rahoton BBC News ya ce Iran ta ce harin ya nufi wani sansanin soja kusa da asibitin, ba asibitin kansa ba.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Majiyoyi sun tabbatar da cewa an samu raunuka a sassa daban-daban na Isra’ila sakamakon harin da aka kai.
Ministan Tsaron Isra’ila, Israel Katz, ya ce:
“Ba za a bar Khamenei ya ci gaba da rayuwa ba.”
A lokaci guda, rundunar sojojin Isra’ila ta ce ta kai farmaki kan sansanonin nukiliyar Iran da suka hada da Arak da kuma Natanz.
Hukumomin Isra'ila sun soki hare-haren Iran
Mataimakin ministan harkokin wajen Isra’ila ya ce harin da aka kai Soroka “na gangan ne” kuma “laifi ne.”
Firayim Minista Netanyahu ya ce:
“Za mu sakawa masu mulkin danniya na Tehran daidai da abin da suka aikata.”
Ministan tsaro, Katz ya kara da cewa:
“Khamenei yana bayyana burinsa na hallaka Isra’ila, shi da kansa ke ba da umarnin kai hari kan asibitoci.”
Hukumar asibiti ta ce gobara ta hallaka wasu sassa, ta fasa tagogi da rushe rufin gine-gine, wani sashe na asibitin ya lalace matuka.

Kara karanta wannan
Ukraine ta faɗi matsalar da za ta faɗa kan rikicin Isra'ila da Iran, ta kama layinta
Shugaban asibitin, Farfesa Shlomi Codish, ya ce za a mayar da marasa lafiya 200 zuwa wasu cibiyoyin.

Source: Getty Images
Yadda makaman Iran ke barna a Isra'ila
A safiyar Alhamis, wani makami mai linzami daga Iran ya bugi Ramat Gan, gabashin Tel Aviv, inda gilashi da sandar lantarki suka fadi.
Hukumomi a Iran suka ce kimanin mutane 20 ne suka ji rauni a harin yankin, yayin da aka samu lalacewar gine-gine da kayan lantarki.
Rundunar Isra’ila ta gargadi mazauna garuruwan Arak da Khondab na Iran da su bar wurin, kafin farmakin da suka kai.
Sansanonin da aka kai wa farmaki sun hada da wani sinadari mai nauyi da ke cikin wani bincike da ake gudanarwa.
Rasha ta goyi bayan kasar Iran
Kun ji cewa shugabannin Rasha da China sun caccaki hare-haren Isra’ila a kan Iran, suna masu kira da a bi hanyar diflomasiyya wajen warware rikicin.
Kasar ta fitar da gargadi mai ƙarfi ga Amurka da ka da ta tsoma baki a rikicin, tana cewa hakan zai janyo mummunan rikici a fadin duniya.
Shugaban Rasha, Vladimir Putin ya nemi zama mai sasantawa tsakanin Isra’ila da Iran, bayan tattaunawa da Netanyahu da shugaban Iran.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng
