Amurka Ta Fara Shirin Yaki, Ana Fargabar za Ta Hadu da Isra'ila a Yiwa Iran Taron Dangi
- Rahotanni sun nuna cewa jami’an gwamnatin Amurka na shirin kai hari kasar Iran a karshen mako mai zuwa
- Lamarin na zuwa a lokacin da yakin Isra'ila da Iran ke kara kamari a kwanaki na shida bayan harba makami a Tehran
- A ranar Laraba, an ji Shugaban Amurka, Donald Trump ya ce bai yanke shawarar ko zai shiga yakin ba tukunna
A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.
Kasar Amurka– Majiyoyi masu tushe sun ce jami’an gwamnatin Amurka na shirin don kai hari kan ƙasar Iran a cikin ‘yan kwanaki masu zuwa.
Wannan na zuwa ne a yayin da rikicin tsakanin Iran da Isra’ila ke ci gaba da ƙamari, inda ake harba manyan makamai kasashen biyu.

Source: Getty Images
Bloomberg ta ruwaito wasu daga cikin majiyoyin sun bayyana Amurka na shirin kai harin ne a karshen mako.

Kara karanta wannan
Kasar Iran ta canza ra'ayi game da tayin Trump, ta yi maganar yiwuwar sulhu da Isra'ila
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Amurka na shirin kai hari a Iran
The Economic Times ta wallafa cewa wasu jami'ai sun bayyana cewa tabbas akwai shirin kai har Iran, sai dai lamarin na iya sauyawa gwargwadon yadda yanayi zai kaya.
Da yake zantawa da manema labarai a gaban Fadar White House a ranar Laraba, shugaban Amurka, Donald Trump ya ki bayyana wa a fili ko zai kaddamar da harin.

Source: Facebook
Ya ce:
"Zan iya yin hakan. Ko kuma ba zan yi ba. Wato, babu wanda ya san abin da zan yi."
Wannan furuci na Trump ya nuna sauyin matsaya idan aka kwatanta da makon da ya gabata, inda yake goyon bayan tattaunawar diflomasiyya tsakanin Iran da Isra'ila.
Donald Trump ya goyi bayan Isra'ila
Trump, wanda ya dade yana goyon bayan kauracewa shiga rikicin ƙasashen waje, ya fara nuna sha'awar kai hari Iran bayan kusan mako guda tana fafatawa da Isra'ila.
Masana da masu sharhi a kan diflomasiyya a ganin sabuwar matsayar tasa zai kara dagula lamarin rikicin yankin Gabas ta Tsakiya.
A gefe guda, Ministan Harkokin Wajen Iran, Abbas Araghchi, ya bayyana cewa ƙasarsu na nan a kan ba wa diflomasiyya damar samar da sulhu.
Ya ce:
"Iran ba ta son faɗa da Amurka. Muna so mu warware matsaloli ta hanyar diflomasiyya."
Masana sun nuna damuwa cewa kai harin Amurka kan Iran na iya janyo rikicin ya ƙara faɗaɗa zuwa sauran ƙasashen yankin, wanda zai iya haifar da rikicin duniya.
Amurka ta 'hana' kashe shugaban Iran
A wani labarin, mun wallafa cewa Shugaban Amurka Donald Trump ya hana wani shirin da kasar Isra’ila ta kitsa na kashe jagoran addini na Iran, Ayatollah Ali Khamenei.
A cewar wani babban jami’in gwamnatin Amurka da ya nemi a sakaya sunansa, Isra’ila ta shaida wa Amurka cewa sun kammala shirin hallaka jagoran.
Fadar White House ta fitar da matsaya inda ta bayyana cewa Trump bai goyi bayan wannan shiri ba, kuma ya bukaci Isra’ila da su dakatar da aiwatar da shi.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng
