Netanyahu Ya Yi Korafi bayan Iran Ta Yi Luguden Wuta da Sassafe a Kasar Isra'ila
- Firaministan Isra’ila, Benjamin Netanyahu, ya zargi Iran da kai harin makami mai linzami a asibitin Soroka da yankunan fararen hula a ƙasar
- Ministan tsaron Isra’ila, Israel Katz, ya ce Ali Khamenei yana ɓoye yayin da yake bada umarnin kai farmaki kan asibitoci da gidajen fararen hula
- Isra’ila ta ce za ta kai farmaki kan manyan ababen more rayuwa da cibiyoyin gwamnati a Tehran domin rage barazanar kasar Iran ga tsaronta
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
Iran - Rikicin da ke tsakanin Isra’ila da Iran ya sake daukar sabon salo yayin da Firaministan Isra’ila da ministan tsaronta suka fitar da sababbin kalamai masu zafi kan shugabannin Iran.
Ministan tsaron Isra'ila ya yi magana kan shugabannin Iran, musamman jagoran juyin juya halinta, Ayatollah Ali Khamenei.

Source: Getty Images
Rahoton Economic Times ya nuna cewa Isra’ila ta zargi Iran da kai hari kai tsaye kan asibitin Soroka da ke Beersheba da kuma yankuna da ke da cunkoson jama'a a tsakiyar ƙasar.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Wannan zargin dai na zuwa ne a daidai lokacin da Amurka ke ci gaba da yin tir da harin da Iran ke kaiwa, tare da bayyana yiwuwar shiga cikin yakin domin mara wa Isra’ila baya.
Isra’ila ta ce Khamenei ya buya a Iran
Iran International ta rahoto cewa Ministan tsaron Isra’ila, Israel Katz ya ce Khamenei ya ɓuya a wani gini da ke da kariya mai ƙarfi yayin da yake bada umarnin kai hari ga fararen hula.
Ya ce:
“Wannan ɗaya ne daga cikin manyan laifukan yaƙi, kuma za a hukunta Khamenei saboda haka.”
Katz ya kara da cewa shi da Firaminista Netanyahu sun umurci rundunar sojinsu da ta ƙara kaimi wajen kai farmaki kan muhimman gine-gine da cibiyoyin gwamnati a Iran, ciki har da Tehran.

Kara karanta wannan
An gano makamin nukiliyan Iran da ya gagari Isra'ila, kasa 1 ce za ta iya tarwatsa shi
Netanyahu: 'Za mu rama harin da aka kai mana'
A wani bayani da ya yi, Netanyahu ya bayyana cewa Iran ta kai hari da makamai kan asibiti da gidajen fararen hula.
Ya ce:
“Da safiyar yau, masu mulkin Iran sun harba makamai kan Asibitin Soroka da kuma al’ummar da ke tsakiyar ƙasar. Za mu rama wannan hari yadda ya dace.”
Netanyahu ya yi barazanar cewa gwamnatin sa za ta "yi martani mai tsanani kan masu mulkin danniya a Tehran" saboda wannan harin da ya ce ba zai yi shiru a kai ba.

Source: AFP
Duk da zargin da Isra’ila ke yi wa Iran, akwai masu sukar lamurranta da ke tunatar da irin hare-haren da Isra’ila ke kaiwa a zirin Gaza, inda ake zargin ta da kai hari asibitoci da makarantu.
Koriya ta Arewa ta gargadi Isra'ila da Amurka
A wani labarin, mun kawo muku cewa kasar Koriya ta Arewa ta nuna goyon baya ga Iran a yakin da take yi da Isra'ila.
Gwamnatin Koriya ta Arewa karkashin Kim Jong Un ta gargadi Amurka kan maganganun da Donald Trump ke yi na shirin shiga yakin.
Koriya ta Arewa ta ce Iran na da cikakken yanci ta kare kanta daga hare haren da Isra'ila ta fara kai mata a makon da ya wuce.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng

