Dama Ta Samu: An Buɗe Hanyoyi 3 da Mutane Za Su Riƙa Samun Kudi a WhatsApp

Dama Ta Samu: An Buɗe Hanyoyi 3 da Mutane Za Su Riƙa Samun Kudi a WhatsApp

  • Kamfanin Meta ya kirkiro hanyoyin uku da masu amfani da manhajar sadarwa ta WhatsApp za su rika samun kudi
  • A wata sanarwa da kamfanin ya fitar, ya ce sabon tsarin zai ba masu kirkirar bidiyon nishaɗi, ƴan kasuwa da masu talla dama
  • Meta ya bayyana cewa wannan tsari ba zai shafi sakonnin sirri da mutane ke aikawa junansu ba, tare da tabbatar da tsaron bayanai

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Kamfanin Meta, mamallakin WhatsApp, Facebook da Instagram, ya sanar sabuwar hanya da za a fara tallata kaya kai tsaye a cikin WhatsApp.

Meta ya kawo sabon tsari da zai bai wa masu amfani da WhatsApp damar samun kuɗi ta manhajar.

Meta ya kawo sabon tsari a Whatsapp.
Kamfanin Meta ya kirkiro hanyoyin samun kudi a manhajar Whatsapp Hoto: Getty Image
Source: Getty Images

Hakan na kunshe ne a wata sanarwa da WhatsApp ɗin ya wallafa a shafinsa na yanar gizo-gizo ranar Litinin da ta gabata.

Kara karanta wannan

Isra'ila: Iran ta umarci jama'a su daina amfani da whatsApp, ta fadi sharrin manhajar

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Hanyoyi 3 da za ku samu kudi a WhatsApp

Meta ya ce wannan sabon tsarin zai bai wa rukunin mutane damar samun kuɗin shiga da WhatsApp, wanda suka haɗa da masu ƙirƙirar abin nishaɗi, ’yan kasuwa, da kuma masu talla.

1. Ajin farko shi ne masu ƙirƙiro bidiyo ko masu gina tashar kallo watau "Channels," inda za a buƙaci masu sha’awa su biya kuɗi kafin su kalli bidiyo.

Wannan yana nufin cewa masu ƙirƙira za su iya tara kuɗi daga masu kallon abubuwan da suka wallafa.

2. Aji na biyu kuwa, shi ne tashoshin talla – kamfanoni da ƙananan ’yan kasuwa za su rika tallata hajarsu a wata sabuwar hanyar da WhatsApp zai ƙirƙira.

3. Aji na uku kuma, ya shafi talla a kan “Status” – kamar yadda ake yi a Instagram, za a iya saka tallace-tallace a cikin labarin “status” na WhatsApp don jawo hankalin masu amfani.

Kara karanta wannan

'Dangote zai samar da ayyuka ga matasa a shirin raba mai kyauta,' Masana

Abin da wannan tsari ya ƙunsa a WhatsApp

Meta ya ce waɗannan sababbin matakai za su taimaka wajen buɗe ƙarin damar samun kuɗi ba tare da kawo cikas ga sirrin saƙonni da tsaron bayanai ba.

A cewar kamfanin:

“Tuni muka dade muna shirin yadda za mu bai wa masu amfani da WhatsApp damar yin kasuwanci a manhajar, ba tare da ya shafi saƙon sirri ba.”

A cikin sabon tsarin, za a ba mutane damar biyan kuɗi don kallon abubuwan da suka fi sha’awa, samun labarai da wasanni daga manyan kafafe da yin talla da ganin tallace-tallacen wasu, a farashi daban-daban.

Sai kuma damar amfani da "status" wajen yaɗa hajoji kai tsaye ga abokai da abokan kasuwanci.

Kamfanin Meta ya kara gyara Whatsapp.
Kamfanin Meta na kara gyara Whatsapp domin shiga jerin manhajojin kasuwanci Hoto: Getty Image
Source: Facebook

Meta ya ƙara da cewa duk da za a buƙaci wasu bayanai kamar garin da mutum ke zaune za a ci gaba da kare lambobin waya da cikakken bayanan na sirri.

"Za mu buƙaci bayanai kamar suna, gari ko ƙasa domin tallan ya dace da wanda aka yi domin shi. Amma ba za mu taɓa ba da lambobin wayarku ba ga kowa,” in ji Meta.

Kara karanta wannan

Yaki ya barke tsakanin Rasha da Ukraine, makami mai linzami ya kashe mutane 15

WhatsApp ya sanya Hausa a jerin harsunansa

A wani labarin, kun ji cewa WhatsApp ya sanya Hausa a jerin harsunan da za a riƙa amfani da su wajen mu'amala da mamhajar.

WhatsApp ya ce ya yi karin harsuna uku na duniya wadanda daya daga ciki shine Hausa. Sauran biyun kuma su ne Amharic da Oromo.

Harshen Hausa dai a kullum na kara shiga duniya, inda kamfanoni da ma'aikatu ke amfani dashi wajen sadarwa.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262