Makaman da Isra'ila Ta Harba Iran Sun Gaza Tashi, Sun Rufto kan Yahudawa
- Wasu makamai masu linzami da Isra’ila ke niyyar harbawa Iran sun kasa tashi mai nisa, inda suka faɗi cikin Tel Aviv suka yi mummunar ɓarna
- Rahotanni sun bayyana cewa Isra’ila na fuskantar ƙarancin makaman kare kai ake amfani da su wajen harbo makamai masu linzami
- Hakan na faruwa ne yayin da yawan hare-haren Iran ya kai fiye da jirage marasa matuka 370, lamarin da ya kashe mutane 24 a Isra’ila ya jikkata fiye da 500
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
FCT, Abuja - Yayin da rikici tsakanin Isra’ila da Iran ya shiga kwana na shida, wani lamari mai cike da rudani ya faru a Isra'ila.
Rahotanni sun nuna cewa wasu makamai masu linzami da Isra’ila ta harba suka kasa tashi mai nisa suka faɗi a cikin Tel Aviv.

Kara karanta wannan
Iran na ci gaba da kai hare hare, yahudawa sun fara guduwa daga gidajensu a Isra'ila

Source: Getty Images
Bidiyon da TRT Hausa ta wallafa a X ya nuna cewa kuskuren ya haddasa mummunan ɓarna da firgici ga al’ummar birnin da ke matsayin babban birnin tattalin arzikin ƙasar.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Bayanai daga Times of Israel sun nuna cewa akwai ƙarancin makaman kariya ake amfani da su wajen harbo makaman Iran a Isra'ila.
Makaman kariya sun ragu sosai a Isra'ila
Rahoton ya bayyana cewa Isra’ila ta kusa ƙarar da makaman kariya da suke hana hana makamai masu linzami shiga cikin ƙasar.
A cewar wani jami’in Amurka da ba a bayyana sunansa ba, gwamnatin Amurka ta dade da sanin cewa Isra’ila na dab da karar da waɗannan makamai, kuma tuni ta fara ƙoƙarin taimaka mata.
Sai dai rahoton ya nuna cewa ko Amurka kanta na fuskantar ƙarancin waɗannan makamai, bayan tura wa Isra’ila da dama.
A halin yanzu, akwai damuwa cewa ko Amurka za ta iya ci gaba da tallafa wa Isra’ila muddin harin Iran ya ci gaba da tsananta.
Harin Iran ya yi kamari a Isra’ila
Tun daga ranar Juma’a da Isra’ila ta fara wani babban farmaki da nufin kawar da barazanar Iran da shirin nukiliyarta, Iran ta mayar da martani da makamai sama da 370.
Wannan ya sa Isra’ila ke cikin matsanancin hali wajen iya harbo dukkan makaman da ke shigowa daga Iran.

Source: Getty Images
A halin yanzu, Isra’ila na amfani da dabarar barin wasu makaman su fāɗi a wuraren da babu mutane domin ba su da isassun makaman harbo su duka.
Amma wannan dabarar ta gaza a wasu lokuta, inda wasu makaman suka faɗi a yankunan jama’a kamar yadda aka gani a Tel Aviv.
Ana hasashen Isra’ila za ta fuskanci ƙalubale
Wani rahoto daga Washington Post ya nuna cewa Isra’ila na da isassun makaman kariya da za su iya amfani da su na tsawon kwanaki 10 zuwa 12 idan harin Iran ya ci gaba.
Ana ganin bayan haka, dole ne Amurka ta shiga da hannunta ko ta sake tura musu makaman kariya.

Kara karanta wannan
Gaza: Tankokin yakin Isra'ila sun bude wuta kan Falasdinawa, mutane da dama sun rasu
Hukumar Tsaron Isra’ila ta ce tana da shiri na fuskantar kowanne hali, amma ta ƙi yin tsokaci a kan halin da makaman su ke ciki.
Majalisar Amurka ta gargadi Trump kan Iran
A wani rahoton, kun ji cewa wasu 'yan majalisar Amurka sun yi yunkurin hana shugaba Donald Trump shiga yaki da Iran.
'Yan majalisar sun ce yakin bai shafi Amurka kai tsaye ba kuma ba za su bari Trump ya kutsa cikinsa ba tare da izini ba.
Hakan na zuwa ne yayin da shugaban Amurka ya yi wani jawabin cewa suna da cikakken iko da sararin samaniyar Iran a yanzu.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng
