Ana Batun Kashe Shi, Shugaban Iran, Khamenei Ya Yi Martani Mai Zafi bayan Barazanar Trump

Ana Batun Kashe Shi, Shugaban Iran, Khamenei Ya Yi Martani Mai Zafi bayan Barazanar Trump

  • Ayatollah Ali Khamenei ya bayyana cewa Iran a shirye take wajen ci gaba da fafatawa da ƙasar Iran
  • Jagoran juyin juya halin na Iran ya bayyana cewa ba za su nuna tausayi a yaƙin da suke yi da ƙasar Isra'ila
  • Kalaman Khamenei na zuwa bayan barazanar da Donald Trump ya yi ta cewa Amurka ta san inda yake ɓoye

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

Ƙasar Iran - Jagoran juyin juya hali na Iran, Ayatollah Ali Khamenei, ya bayyana cewa ƙasarsa ta shirya tsaf don ci gaba da fafatawa da Isra’ila.

Ayatollah Khamenei ya bayyana cewa Iran ba za ta nuna tausayi ba yayin da rikicin da ke tsakanin ƙasashen biyu ke ƙara tsananta.

Khamenei ya yi barazana ga Israila
Khamenei ya ce ba za a nunawa Israila tausayi ba Hoto: Getty Images
Source: Getty Images

Khamenei ya bayyana hakan ne a cikin wasu saƙonni da ya fitar a shafinsa na X a daren ranar Talata.

Kara karanta wannan

An taɓo Trump daga Najeriya, tsohon minista ya yi zazzafan martani kan yaƙin Iran da Isra'ila

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Wannan furuci ya zo ne jim kaɗan bayan da shugaban ƙasar Amurka, Donald Trump, ya yi barazanar neman miƙa wuya daga Iran ba tare da wani sharaɗi ba.

Donald Trump ya bayyana cewa Amurka ta san inda Khamenei ke ɓuya, amma ba ta da niyyar kai masa hari a yanzu.

Ali Hosseini Khamenei ya sha alwashi

Sai dai Khamenei, cikin saƙonnin da ya fitar da daddare a ranar Talata, ya wallafa wani hoto wanda ke nuna wuta na sauka daga sama a kan wani tsohon birni, yayin da wani mutum ɗauke da takobi ke shigowa ƙofar birnin.

A wani saƙon na daban da ya rubuta cikin harshen Turanci, jagoran na Iran ya yi barazana ga Isra’ila, yana mai cewa ƙasarsa ba za ta nuna musu tausayi ba.

Ya rubuta cewa:

“Dole ne mu mayar da martani mai ƙarfi ga haramtacciyar gwamnatin Yahudawa. Ba za mu nuna musu tausayi ba."

Kara karanta wannan

Wata sabuwa: Trump ya yi maganar yiwuwar kashe Shugaban Iran, Ayatollah Khamenei

A halin da ake ciki kuwa, rahotanni daga kafafen yada labarai na nuna cewa talabijin na gwamnati a Iran ya fitar da wata sanarwa mai ban tsoro wadda ke cewa:

"Yau da daddare, wani babban abin mamaki zai faru, wanda duniya za ta ci gaba da tunawa har tsawon ƙarnuka."
Iran ta shirya kai hare-hare kan Isra'ila
Khamenei ya ce Iran ba za ta tausayawa Isra'ila ba Hoto: @khamenei_ir
Source: Getty Images

Ana zargin Amurka na iya shiga yaƙin Iran-Isra'ila

Rahotanni sun bayyana cewa hakan na faruwa ne a daidai lokacin da gwamnatin Trump ke nazarin yiwuwar shiga yaƙin da ke faruwa a Gabas ta Tsakiya kai tsaye, ta hanyar kai hari kan Iran.

Tashar CNN ta ruwaito cewa an tura jiragen yaƙin Amurka guda huɗu na B-52 Stratofortress zuwa sansanin Diego Garcia da ke cikin Tekun Indiya, wani wuri mai mahimmanci da ke kusa da inda za a iya kai farmaki kan Iran.

A baya shugaban Amurka ya kira ga ɗaukacin ƴan ƙasar Iran da su bar babban birnin Tehran, yana gargaɗin cewa rikici na ƙara tsananta, tare da zargin gwamnatin Iran da rashin amincewa da yarjejeniyar nukiliya da Amurka.

Kasar Iran ta kai hare-hare kan Isra'ila

A wani labarin kuma, kun ji cewa ƙasar Iran ta ƙara kai zafafan hare-hare kan abokiyar gabarta watau Israila.

Kara karanta wannan

Sanata ya gano matsalar da ke ta'azzara rashin tsaro a Najeriya

Iran ta harba jerin makamai masu linzami da jirage marasa matuƙa yayin da ake ci gaba da gwabza faɗa tsakanin ɓangarorin biyu.

Dakarun rundunar IRGC na Iran ne suka jagoranci ƙaddamar da harin wanda aka yi wa laƙabi da 'Operatioɓ True Promise'.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal (Hausa Editor) Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng