Sheikh Gumi da Wasu Fitattun Malamai 16 da Saudiyya Ta Taba Hana Su Aikin Hajji
Kaduna - A ranar 26 ga Mayun 2025, Saudiya ta hana Sheikh Ahmad Gumi, fitaccen malamin Musuluncin nan na Kaduna, shiga Madina domin aikin Hajjin 2025.
Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida
Duk da cewa lamarin Sheikh Gumi ya dauki hankalin jama'a sosai, sai dai ba shi ne malamin Musulunci na farko da ya taba fuskantar irin haka ba.

Source: Twitter
Jaridar Vanguard ta ruwaito cewa jami’an shige da fice na Saudiyya ne suka dakatar da Gumi a filin jirgin saman Prince Mohammad Bin Abdulaziz da ke Madina a daren Asabar, kuma aka koro shi daga kasar.
An hana Ahmad Gumi yin aikin Hajji duk da yana da ingantacciyar bizar Hajji kuma yana cikin tawagar da hukumar Hajji ta kasa (NAHCON) ta dauki nauyinsu.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
An mayar da Gumi gida Najeriya cikin jirgin Umza Air da ya yi jigilarsa tun farko, wanda hakan ya hana shi yin aikin Hajji – daya daga cikin shika-shikan Musulunci biyar.
Sheikh Gumi ya danganta wannan matakin na hukumomin Saudiyya da ra’ayoyinsa kan siyasar duniya da suka ce suna hana su jin dadin zuwansa kasar a lokacin Hajji.
A cikin wani rubutu da ya wallafa a shafinsa na Facebook, Gumi ya ce:
“Sakamakon wasu dalilai da suka shafi ra’ayoyina kan siyasar duniya, hukumomin Saudiyya ba sa so na halarci Hajji duk da sun ba ni biza.”
Gumi na da tarihin fadin ra’ayoyi masu tayar da kura, ciki har da suka ga manufofin Saudiyya, shisshigin kasashen Yamma da Gabas ta Tsakiya, da kuma kiran da yake yi a tattauna da ‘yan bindiga a Arewacin Najeriya.
Masu sharhi na ganin cewa kalamansa masu tsauri kan harkokin kasa da kasa – ciki har da kin amincewarsa da shirin kafa kasashe biyu tsakanin Isra’ila da Falasɗinu da suka kan sauye-sauyen da Saudiyya ke yi – na iya janyo masa wannan matsala.
Wasu malaman Musulunci da aka hana yin Hajji
Duk da cewa lamarin Sheikh Gumi ya dauki hankalin jama'a sosai, sai dai ba shi ne na farko da ya taba fuskantar irin haka ba.
A cikin ‘yan shekarun baya, kasar Saudiyya ta hana wasu manyan malaman Musulunci yin aikin Hajji, musamman idan akwai sabani na ra’ayi ko siyasa tsakaninsu.
Ga bayani dalla-dalla kan wasu daga cikin shahararrun malaman da aka hana, kodayake ba a cika samun cikakkun bayanai ba sai dai misalai kamar na Gumi.
1. Sheikh Yusuf al-Qaradawi (Masar/Qatar)
Dalilin hana shi Hajji:
Sheikh Yusuf al-Qaradawi, babban malamin addini dan asalin Masar da ke zaune a Qatar, an hana shi shiga Saudiyya domin Hajji a shekarar 2018.
Rahotanni sun bayyana cewa an hana shi shiga Madina ne saboda alakarsa da kungiyar Muslim Brotherhood, watau 'yan Shi'a, da kuma sukar da yake yi wa manufofin Saudiyya.
Saudiyya ta ayyana kungiyar Shi'a a matsayin kungiyar ta’addanci, kuma kasancewar Qaradawi yana goyon bayan kungiyar da kuma sukar manufofin Saudiyya na cikin gida da waje, hakan ya sa aka hana shi yin aikin Hajji.
Tasirin hakan ga mabiyansa:
Hana Qaradawi yin Hajji ya shafi kungiyoyin Shi'a a duniya da kuma mabiyansa, musamman a Qatar da sauran wuraren da ke da goyon bayan kungiyar.

Kara karanta wannan
Ambaliya: Ana tsoron rayuka sama da 50 sun salwanta bayan gano gawarwaki 15 a Neja
Masu goyon bayansa sun fassara hana shi aikin Hajji a matsayin yunkuri na dakile ‘yancin fadin albarkacin baki cikin addini.
Lamarin ya tayar da muhawara game da yadda Saudiyya ke sarrafa wuraren ibada da kuma matsin lamba da ta ke sa wa masu sabani da ita.
Hakan ya taimaka wajen kara rikicin diflomasiyya da ke tsakanin Saudiyya da Qatar a lokacin rikicin Gabar Tekun Gulf daga 2017 zuwa 2021.
2. Sheikh Salman al-Ouda (Saudiyya)
Dalilin hana shi aikin Hajji:
Sheikh Salman al-Ouda, malamin addini ne daga Saudiyya, ya samu takunkumi na hana shi yin Hajji bayan da aka kama shi a 2017 tare da daure shi.
Ko da yake ba a bayyana hana shi Hajji kai tsaye ba, amma kasancewarsa a gidan yari ya hana shi halartar wannan ibada.
Hukumomin Saudiyya sun zarge shi da goyon bayan ta’addanci da yada ra’ayoyi masu raba kan al’umma, musamman saboda ra’ayoyinsa na gyara da kuma shakku kan alakar sa da 'yan Shi'a.
Ya kuma caccaki barazaar da Saudiyya ta yi wa Qatar, wanda hakan ya zama daya daga cikin dalilan cafke shi.
Tasirin hakan ga mabiyansa:
Kame al-Ouda da hana shi yin Hajji ya girgiza mabiyansa da ke cikin Saudiyya da ma wajen kasar mai tsarki.
Sananne ne wajen bin hanyar sauyi cikin Musulunci, kuma rashin halartarsa ya rage tasirin muryar da ke kira da sauyi cikin tsarin addinin.
Mabiyansa sun fassara kama shi tare da tsare shi a matsayin yunkurin hana masu ra’ayoyi na kawo sauyi yin magana.
Kungiyoyin kare hakkin dan Adam na duniya irin su Amnesty International sun yi Allah-wadai da kama al-Ouda da kuma hana shi ibada, inda suka ce hakan saba wa ‘yancin addini.
Sauran manyan malamai 5 da aka hana Hajji
Rahotanni sun nuna cewa Saudiyya na da tsari na takaita shigar malaman addini da masu tsattsauran ra’ayi da ke sabawa manufofin gwamnatin kasar.
Yawancin wadannan takunkuman na fitowa ne daga sukar manufofin Saudiyya ko kuma kasancewar su ‘yan kungiyar Shi'a.
Rahoton Hajj Monitor na 2023 ya bayyana cewa wadannan malaman Musulunci guda biyar sun fuskanci takunkumi daga shiga Makka ko gudanar da aikin Hajji:
- Dr. Muhammad al-Saghir (Masar)
- Sheikh Wajdi Ghoneim (Masar)
- Sheikh Muhammad Abd al-Maqsoud (Masar)
- Dr. Ali al-Sallabi (Libiya)
- Sheikh Sadiq al-Gharyani (Libiya)
- Tariq Ramadan (UK)
- Mohammad al-Arefe (Saudi Arabia)
- Mohammed al-Hassan Ould al-Dedew (Mauritania)
- Mohammad Rateb al-Nabulsi (Syria)
- Ali al-Qaradaghi (Iraq/Qatar)
- Mohammad al-Ali Sabouni (Syria)
- Mohammad Mukhtar Shanqeeti (Mauritania/Qatar)
- Adnan Ibrahim (Austria)
- Hassan Farhan al-Maliki (Saudi Arabia)
Rahoton bai bayyana lokaci da cikakken dalilin hana kowannensu Hajji ba, amma yana danganta hakan da alakarsu da 'yan Shi'a da kuma sukar manufofin Saudiyya.
Tasirin lamarin kan ‘yancin addini da diflomasiyya

Source: Twitter
Hana Sheikh Ahmad Gumi da wasu malamai yin Hajji ya haifar da tambayoyi masu zurfi kan ‘yancin addini da siyasantar da ibada.
A matsayinta na mai kula da wuraren ibada mafi tsarki cikin Musulunci, Saudiyya na da karfin iko kan aikin Hajji da ya ke shigo da miliyoyin Musulmai kasar duk shekara.
Ko da yake Saudiyya na iya daukar wannan mataki da hujjar kare tsaro da tabbatar da doka yayin Hajji, amma akwai bukatar tantance ko hakan bai sabawa damar ba Musulmai yin ibada ba.
Yayin da Duniyar Musulmi ke fama da irin wadannan sabani, lamarin yana jaddada bukatar tattaunawa domin tabbatar da cewa aikin Hajji ya kasance hanya ta hadin kai ba sabani ba.
'Abin da Gumi ya ce kan Hajjin 2025'
Tun da fari, mun ruwaito cewa, Dr Ahmad Gumi ya yi magana kan aikin Hajjin shekarar 2025 saboda zargin hukumomin Saudiyya da kawo masa cikas.
Malamin ya yi zargin cewa bayyana ra’ayinsa kan siyasar duniya ne suka sa aka nuna rashin gamsuwa da zuwansa Hajji.
Sheikh Gumi ya gode wa gwamnatin Najeriya da ta tsaya masa, ya ce yanzu zai mayar da hankali kan lafiyarsa da harkokin noma.
Asali: Legit.ng




