Saudiyya ta yi barazanar fara kai wa Qatar hari
- Saudiyya tayi barazanar fara afkawa Qatar muddin ta sayi makakin S-400 daga Rasha
- Sarkin Saudiyya Salman ya ce mallakar S-400 din barazana ne ga tsaron kasar sa
- Sarki Salman kuma ya nemi shugaban kasar Faransa Macron ya saka baki a batun cinikin makamin
Gwamnatin kasar Saudiyya ta yi barazanar fara kaiwa kasar Qatar hari har idan bata dakatar da cinikin sayan makamin kakkabo jiragen yaki ko makami mai linzami mai kirar S-400 daga kasar Rasha ba.
Wata jaridar kasar Faransa mai suna Le Monde ta ruwaito cewa Sarkin Saudiyya Salman ya aikewa shugaban kasar Faransa Emmanuel Macron wasika inda ya nuna damuwarsa a kan tattaunawar da ke tsakanin Qatar da Rasha dangane da cinikin makamin na S-400.
KU KARANTA: Dubi yadda jihohin Arewa ke kan gaba wajen adadin mutanen da za'a dauka aikin 'Dan sanda
Sarki Salman na Saudiyya ya ce mallakar makamin kakkabo jiragen yaki da makamai masu linzami da Qatar ke kokarin yi barazana ce ga tsaron Saudiyya hakan yasa ya nemi Faransa ta shiga tsakani.
A ranar 5 ga watan Yunin 2017, Saudiyya tare da kasashen Bahrain da Hadaddiyar Daular Larabawa da Masar sun cinma matsaya na kafawa Qatar takunkumin diflomasiyya wanda ya kunshi rufe iyakokinsu na sama, ruwa da kasa ga Qatar saboda suna zarginta da daukan nauyin ta'addanci.
Amma daga baya, Saudiyya ta dage takunkumin da ta kafawa kasar Qatar tare da gindaya mata sharudda da suka hada da rufe sansanin sojin Turkiya da ke kasar na Qatar da kuma kulle kafar yada labarai ta Aljazeerah.
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa
Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng